Chapter twelve

64 6 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 12*

          "Hajiyata kije in ji Hajiya babba" da idanu kawai ta bi Aminatu sannan ta miƙe ta nufi upstairs. Ajiyar zuciya Aminatu ta sauke tana maye gurbin ta a kujerar a fili ta ce, "Kina ruwa kham! A zaune Noor ta tarar da Mom tana latsa waya, a hankali ta zauna a kan couch idanunta na kawo ruwa. "Shikenan dan Tahir ya tafi sai aka ce miki mutuwa zai yi? Duk kin bi kin ɗaga hankalin ki kamar a kanki aka fara soyayya ko aure? Su sauran mazan da za'a tafi tare da su fa? An ce miki basu da iyali? Addu'a kawai za kiyi masa, kar na ƙara ganin hawayen ki! Noor bata iya cewa komai ba sai share hawayen da suke kuma zubowa ta ke. Bayan sallar magrib Noor ta nufi falon Daddy ɗinta, shigowa tayi a hankali, a zaune ta hango shi waya kare a kunnen shi, tsayawa tayi tana kallonsa..... Misalin ƙarfe biyu na dare Aminatu na tsaye cikin duhu a falon me girma gwamna tana kalle² tsaf dama ta karance wajen tsaf tun ba yau ba, hakan ya saka ta fara tafiya a hankali tana ƴan taɓe² dan kar ta bige da wani abun. Drawer da ke falon ta nufa ta ciro ƴar fitilarta ta haska tare da buɗewa a hankali, takardu ne a ciki, fito dasu tayi tsaf ta fara dubawa amma duka takardun na harkar siyasa ne. Mayarwa tayi ta rufe ta kuma buɗe dayen drawer, akwati me ɗauke da pin ta gani. Kashe fitilar tayi ta ɗauke akwatin ta nufo hanyar fita, haske ne ya gauraye falon gaba daya. Zuciyarta ce tayi wani irin bugawa da karfi. "Waye nan? Ta ji saukar muryar sa a kokan kunnenta. Bata ce komai ba ta fita da saurin gaske. Biyota yayi amma sam ko ne kama da ita be gani ba. Aminatu kuwa karkashin bene ta shige gumi na keto mata, tana ganin shi yazo ya shige sai data ga dawowar shi sannan ta fito. P cap ɗin kanta ta gyara ta nufi ɓangaren su. Ɗakinta ta shiga tana ɗaukar wayarta ta shiga kiran Hydar. Bugu daya ya ɗauka dan already jiranta yake. " Na dai ga akwati but akwai security kana wajen har yanzu? Shuru tayi tana sauraren shi kafin ta katse. A ɗankwali ta kulle akwatin sannan ta fito tana kalle². Tafiya tayi me tsayi kafin ta isa gate ɗin da zai fitar da kai daga ainahin cikin gidan. Sojoji ta gani  su uku suna shan shayi. Runtsa idanunta tayi ta koma baya, laɓewa tayi tare da making sound me karfi. Tana kallonsu suka fara kalle² kafin su miƙe biyu suka nufo inda take daye kuma yana bakin gate din. Ta space din baya ta nufi inda ɗayen sojan yake kafin ya an kara ta buga masa akwatin hannunta a wuyansa kasancewar ta baya ta biyo be ganta ba. Kan ya dawo hayyacinsa ta fice a guje, gudu take iya karfinta har ta fice daga gidan sauran securities kuwa sun shiga turaka ba daɗewa. Tana fitowa dae dae bakin ƙofa Hydar ya buɗe mata mota ta shiga ko rufewa bata ƙarasa yi ba ya ja motar a 360 suka bar wajen. Ajiyar zuciya ta fara saukewa tana cire Pcap ɗin kanta. Gumi take yi sosai, AC ta ƙaro tana sauke numfashi. "I'm a dead meat da sun kamani! Ban taɓa tunanin zan iya wannan gudun ba! "Sorry" ya faɗa hankalin shi a kan tuƙin da yake. Sai da sukayi nisa sosai kafin ya nema musu hotel. Bayan sun isa hotel ɗin number motarsa ya cire ya saka wani number sannan suka nufi cikin hotel ɗin. Ɗaki ya kama musu. Suna shiga ɗakin ta kunce gashinta da take ji ya mata nauyi ga zafi da take ji. Acn ɗakin Hydar ya kunna yana kallonta ya ce, "Bari na baki ruwa " bata ce komai ba ta zauna. Ruwa ya kira aka kawo musu. Sai data sha kafin ta kalleshi ta ce, "Whats up? Kaje kuwa? "No sai 3 sannan zasu zo, ki zauna a nan! Ni da team ɗina zamu je, already Abbas ya bani address ɗin Raihan is not going anymore! Ki kwanta ki huta idan na dawo sai a duba me a cikin akwatin" "Ok but you should be very careful" Kai ya gyaɗa mata sannan ya fita. Bluetooth ya saka a kunnen shi, bayan sunyi magana da team ɗinsa. A office ɗinsu suka haɗu ko wanne ya shirya dama Hydar ɗin ake jira. "Kuyi a hankali Hydar! Cewar Abbas yana kallon su. "In sha Allah! "Good, wire house ɗinsa make sure babu wanda ya ganku and do not attack! I will make sure cewa an kama ɗaya daga cikin su! Moreover Hydar akwai wani akwati dake ɗakin general if possible ka saka Aminatu taɗauko it will help saboda akwai jerin sunayen wadanda suke harƙallar miyagun kwayoyi da bindigu da ake shigo da su" "Ok" cewar Hydar yana kallon shi. A mota ɗaya suka bar office ɗin bayan sun gama tsara yadda zasu dira a wajen dan already Abbas yayi musu bayanin yadda gidan yake. Abbas ne ya fara sauka sannan su duk suka rarrabu. Inda zasu haɗu da mutumin Abbas ya je ya zauna ba'a ɗau lokaci ba mutumin yazo, bazai wuce sa'an Hydar ba ya sha baƙaƙen kaya kamar shedan. Zama yayi yana faɗin "Motocin suna daga chan baya kaya sun iso! Ka cewa General inga cikon kudina! Tahir fa? Ya General yayi dashi? Sai da Abbas ya cijee lips ɗinsa sannan ya ce, "Kai ma kasan kwanan zancen! Murmushi mutumin yayi yana faɗin "Good for him!  "Muje na fara ganin kayan! Cewar Abbas yana miƙewa. Mutanen mutumin ne suka rakosu har zuwa inda trailers ɗin suke an rufe su da algarara. Buɗewa ya saka akayi, buhunhuna ne cike da ciyayi sai ka taba zaka ji bindigu. "Ok kwayoyin fa? Cewar Abbas yana kallon shi.  "Yawwa an samu ƙari fa a kan kuɗin ƙwayar kuɗin shi ya kama 1.2b a kudin Nigeria ka fada masa, muje ka gani" bin bayansa Abbas yayi nan ma ya nuna masa ƙwayar da ke cikin suitcases sunfi dari jere a motar. "Muje kayi signing sai na wuce" kai Abbas ya gyaɗa. Juyowar da za suyi mutumin yaji saukar bullet a kafafun shi duk biyun. A wajen ya zube kan kace me mutanensa sun fara musayar wuta. Tuni Abbas yayi flat a kasa yana kallon mutumin ya ce, "What's all this? Cike da azaba ya ce, "I don't know eith... kasa ƙarasawa yayi saboda azabar zafin da yake ji a ƙafafun shi. Da ƙyar Abbas ya kai shi motar su Hydar... Hydar dake maƙale a maɓuya ya danna Bluetooth dinsa yana faɗin "Waye yayi attacking? This isn't our plan? Amsa suka bashi da ba kowa. Sosai abun ya bashi mamaki, dole ya fito ya na gyara gun ɗin hannunsa, tafiya yake da baya² yana waige².. ji yayi ya taka hannun mutum... da sauri ya matsa yana saita ta da bindiga.. hannunta toshe a bakinta sai uban gumi take haɗawa. Baya ganinta sosai sai kyallin zoben dake hannunta yake iya hangowa. Bindiga yaji an saita a ƙeyarsa... yana shirin juyowa yaji fitar bullet, da karfi ya runtsa idanunsa... "Hydar muje! Yaji an faɗa da karfi. Cike da mamaki ya juyo yana kallonta. Aminatu ce. Ganin ya kafeta da idanu ya saka ta ce, "Muje mana! Bai ce komai ba ya juyo yana kallon macen dake tsugunne har lokacin a wajen. Hasketa Aminatu tayi. Zaro idanunta tayi tana kallon Noor. "What?! Cewar Aminatu da ƙarfi. Zumbur ta miƙe, saita ta Aminatu tayi da bindiga tana kallon Hydar ta ce, "Leave! "Baki da hankali ne! Kasheta zakiyi? Ya faɗa yana kwace bindigar hannunta. "She's one of them! Me kake tunanin tana yi anan? Kai Noor ta girgiza tana kuka. Hannayenta Aminatu ta riko ta hadesu ta baya... "Da zafi ki sakeni dan Allah" ta faɗa cikin raunananniyar murya. "Please Aminatu I... "Wai kai Hydar me yake damunk... Aminatu bata karasa ba suka ji karar bullet... kallon juna Hydar da  Aminatu sukayi, a hankali Noor tayi ƙasa idanunta sun firfito waje tana kallon mutumin da Aminatu ta harba a cinya dan shi ne ya harbeta.. zaro ido mutumin yayi dan Aminatu yaso harba amma ya harbi ƴar me gidan me gidan su. A mugun tsorace ya nemi hanyar guduwa amma Hydar ya chafko shi da karfi... "Noor! Cewar Aminatu tana kallon Noor data fara rufe idanunta a hankali. Da ƙyar Aminatu ta iya daukar Noor a baya zuwa mota Hydar kuma ya tasa keyar mutumin.  "Where are you taking me! Abbas kana ina? Ogan su ya faɗa yana ƙoƙarin kwace kanshi daga hannun sauran team ɗin su Hydar. Kan bindiga Aminatu ta buga masa tana faɗin "Dallah rufe mana baki" kasancewar motar Sceina ce babba ta ɗaukesu su duka. A asibiti aka sauke Hydar, Aminatu da Noor, Emergency suka nufa da Noor da ko motsi bata iyawa. Doctor on call ne ya kallesu yana shirin fara jawabin bazai karbi Noor ba sai da Police Hydar ya nuna masa ID ɗinsa. A wajen A$E ɗin suka tsaya Aminatu ta kasa zaune ta kasa tsaye. "In the first place me ya kawoki? This happened all because of you! Meyasa ba zaki taba tsayawa a matsayinki ba! Nan ba hurumin ki bane Amina! Da mamaki take kallon shi har ya kammala maganar shi. "ok saboda an harbeta? Ni kasan irin hatsarin dana saka kaina saboda kai? Me kuke yi ne ma awajen a laɓe kamar barayi? Kunfi kowa sanin dole convey ɗin sa zasu dinga zagaye wajen and you guyx are expecting they won't caught you? How on earth do you guyz think of that? "Ok yanzu da kika zo kikai attacking yayi helping? You ain't there when we planned how to deal with the issue! Meyasa kawai zaki ɓullo from no where? Yanzu ita Noor ɗin da kikai silar harbinta da akayi fa? "Oh ni ce ma sila? Cewar Aminatu ranta ba dad'i! "Idan ma ni ce sila good for her! Ta ɗanɗana taji yadda mahaifinta yake saka a ɗau ran wasu! I pray she won't make it! Daga haka ta wurga masa mayafin Noor dake hannunta tana barin wajen. Ajiyar zuciya ya sauke.. Aminatu bata daɗe da barin wajen ba likitoci suka fito da Noor za'a shiga da ita theater. "Za muje kasa hannu" wata nurse ta faɗa tana kallonsa. Bai ce komai ba ya bi bayanta. Takardar taking consent ta ba shi, ya cike sannan ya saka hannu. Kan shi ya dafa yana jin kafafun shi sun masa nauyi. "Kar ka damu zata ji sauƙi kuyi ta addu'a" daga haka ta bar shi a wajen.  A chan OPR kuwa sai da suka ɗau awa kusan uku sannan aka fito da Noor zuwa ICU. Sai daya zauna a ofishin likitan kafin likitan ya fara jawabi kamar haka, " Is she the daughter of Alkasim? Meaning our governor? Kai ya girgiza alamar a'a. Kai likitan ya gyada kafin ya cigaba da cewa, " She's in severe pain and there is 50% chance of survival! Meaning we can loose her or she can regained consciousness, firstly ta shiga shock kafin faruwar abun! Lucky her kuma bullet ɗin be kai zuciyarta ba! Zamu barta a ICU mu gani zuwa wani ɗan lokaci, amma idan kuna ganin zaku fitar da ita waje toh! Mudai munyi iya ƙoƙarin mu, fakawarta kuma sai lokacin da Allah yayi ko yau ko gobe ko jibi nan da sati daya bamu dai sani ba" cike da damuwa Hydar ya ce, "Ok amma kana ganin bazata wuce sati dayen ba? Likitan na girgiza kai ya ce, "Bazan ce ga ranar da zata tashi ba dan zata iya tashi yau kuma zata iya kai wa har shekara daya ma ko fiye da hakan! Zaro ido yayi yana kallon likitan! "Ka kwantar da hankalinka, yanzu dai ya kamata a sanar da family ɗinta, za kai billing na komai ko sai yan uwan nata sunzo? "Nima ai dan uwanta ne! Bari naje na biya" cewar Hydar yana ƙoƙarin miƙewa. "Tsaya ka haɗa da wannan drugs ɗin" cewar likitan yana ciro prescription sheet, rubuce² yayi sannan ya mika masa ya karɓa tare da ficewa. Bayan ya siyo drugs ɗin ya biya kudin komai kafin ya nufi ICU ɗin. Mask ya saka tare da cire takalmin sa ya shiga tare da izinin nurses ɗin da ke icu din. Drugs ɗin ya basu yana nufar inda Noor take a kwance, wata uwar roba sake a bakinta kamar dai ta suctioning, hancinta sanye da oxygen tube, hannunta sanye da cannula the both hands ɗan yatsanta kuma sanye da pulse oximeter, ga 12load na ECG a kirjinta an rufe da blue ɗin zani na asibiti, lokacin daya ta canza ta kara wani haske.  "Allah ya baki lafiya" ya faɗa yana fitowa daga wajen.  Kiran Abbas ne ya shigo wayar shi. Ɗauka yayi tare da karawa a kunne. "Me ya faru ne? Komai ya tafi dai²" "No Abbas! Ban san me ya kawo Noor ba and she was shut yanzu ma she's unconscious muna asibiti" "what?! Wace Noor ɗin ma tukunna? Cewar Abbas daga dayen side ɗin da karfi. "Noor dae ta gidan da kake! Ban san yadda zanyi ba, Please mu haɗu by 9 yanzu zan wuce gida nayi wanka" da ok Abbas ya amsa sannan Hydar ya katse kiran yana furzar da iska. Hotel ɗin daya kama ya nufa dan ya bar laptop ɗinsa a chan. A gefen gado ya zauna yana riƙe kan shi da ya fara ciwo. Fitowa tayi daga bathroom tana daure medium towel a gashinta. Birki taja ganinshi a zaune, sai kuma ta fara komawa da baya². Ɗagowa yayi suka hada ido, a hankali ya sauke idanunshi daga kallon ta. Slowly ya mike ya fice, 20mins ya bata kafin ya dawo ɗakin. A zaune ya ganta tana shan malt. "I'm sorry for what happened" ya faɗa yana kallonta. Dan ɗagowa tayi ta kalleshi ba tare da ta ce komai ba. "I said I'm sorry" "Meyasa zaka ce sorry? After all ni ya kamata na baka hakuri nasa anyi hurting girlfriend dinka! Iska ya furzar yana kallonta ya ce, " She's a married woman so please let's keep that aside I just loose my temper yesterday kiyi hkr" "Ba komai Hydar" daga haka ta mike. "What's in the box? "Ban bude ba" ta bashi amsa ba tare da ta kalle shi. "Amina nasan ban kyauta ba Please kar kiyi fushi aiki muke, so kar mu dinga jin haushin juna"  "Ni bana jin haushinka! Daga haka ta buɗe nufi kofa ta fice. Akwatin ya ɗauka ya ɓalle shi, daloli ya gani a ciki kamar zasuyi magana, fito dasu yayi kaf kafin ya tsinci ƙaramin littafi, buɗewa yayi ya fara dubawa, sunaye ne iri² a jiki da wasu lissafi da bai gane musu ba. Rufewa yayi ya mayar da kudin ya rufe ya daure akwatin a ɗankwalin. Ƙarfe 9 Abbas yazo hotel ɗin. Hydar na zaune yana jiran shi ya shigo. Miƙewa yayi yana kallonsa ya ce, " Ina Tahir yaje? "Meyasa kake tambaya? "Nayi tunanin ka ce min General ya tura shi mission meyasa zaiyi haka bayan yasan shi din ango ne angon ma na ƴarsa? "Abu ne me wahala Tahir ya dawo! Yayi planning wani abu daban da bani da tabbaci a kai" kai Hydar ya gyaɗa kafin ya ce, "Yanzu dae maganar Noor nasan soon parents ɗinta zasu fara nemanta kuma bana so kowa yayi finding out inda take! Inaso nasan dalilin zuwanta wajen nan jiya" "Wani waje kenan? Abbas ya faɗa yana kallon Hydar. "Inda muka je! A chan muka ganta ni da Amina kuma a chan aka harbeta, mun kama mutum biyu duk suka wajen IG Ɗahir! "Good! Yanzu dae dole mu fitar da Noor daga asibiti I'm pretty sure bata da masaniya akan abinda mahaifinta keyi" kai Hydar ya girgiza yana kallon Abbas ya ce, "I'm not that sure saboda mun rabu da Noor baram² saboda na faɗa mata mahaifinta is a criminal I even sent her some few evidence amma ta rufe idanunta har tayi blocking ɗina so that bazan iya reaching ɗinta ba, lokacin dana ganta she looks scared and shocked! " yanzu dai bamu da ta cewa dole mu jira ta farka! Kuma indai za'a fitar da Noor daga asibiti kasan dai sai dai ta zamana karkashin kulawar likitoci, kuma that will cost a lot, sannan a ina ma zaka sakata? Ko kana da gida ne? "Bani da shi, i think is better na kaita Kano waje Mommy zan mata explaining ɗin komai" "ok me gidan ku fa? "Bansan yadda zai ɗauki maganar ba kasan halin shi" "Sun santa dama? Abbas ya kuma tambayar shi. "Eh, more especially my mother amma bata san ƴar wace ba! But my junior sister *Mami* knows! She's her big fan on social media" kai ya gyaɗa yana kallon Hydar ya ce, " Ka kaita kawai dan baka da wani option zamanta a Abuja ma bazai yu ba kai kanka kasan General nemanka yake, yanzu abinda zakai ka fara fadawa Mommynka kafin ka shirya komai You have to spend alot fa, dan sai ka siyi equipments na asibiti da za'a mata amfani dasu kamar yadda ake mata a asibiti kuma ka samu personal doctor da za'ayi trusting dinsa ya dinga dubata, if possible kawai kasa Amina ta dauko ATM card ɗinta ayi amfani da kudin dan gaskiya you can't afford it all" "but her pin? Hydar ya Faɗa yana kallon shi. "Mata ai basa saka abinda ya wuce date of birth ɗin su, muyu trying idan beyi ba sai muyu tunanin wata hanyar" kai Hydar ya gyaɗa alamar toh.....

Autarmama ce.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now