chapter eighteen

47 3 6
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 18*

         Wa she gari da safe da misalin karfe 10 Hydar ya bar gidan su ya nufi na shi gidan. A ƙofar ɗakinta ya tsaya ya fara knocking a hankali. "I'm coming" yaji ta faɗa daga ciki. Tsayawa yayi yana jiranta. Buɗe kofar tayi tana kallon shi with smile on her cute face ta ce, " Ina kwana? "I'm good ya jikin? Ya faɗa yana ɗauke idanun shi daga gareta. "Naji sauki" ta amsa a hankali. "Za ki koma wajen Mommy dina so prepare yourself" da ok ta amsa tana komawa ciki tare da taimakon crotches ɗinta. Ba ta dau lokaci ba ta fito tana kallonsa ta ce, "Mu je" from head to toe ya kalleta kafin ya miƙe ya nufi cikin ɗakin da ta fito, kayanta ya kwaso kaf a jaka sannan ya fito, miƙewa tayi suka fito ya buɗe mata mota ta shiga sannan shima ya shiga. Sai daya rufe gate ɗin gidan sannan ya koma mota suka bar layin. Sai da suka ɗau hanya kafin ta kalleshi ta ce, "What about Raihan? "He's fine" ya amsa a takaice. " Ok, amma dai da yardar Mom dinka zaka kaini gidanku ko? Kai kawai ya gyaɗa alamar eh. Bata ƙara cewa komai ba har suka isa gidan su Hydar. Bayan yayi parking ya sauka ya buɗe mata, shi ya taimaka mata ta fito ya bata crotches ɗin. Godiya ta masa sannan yayi mata jagora zuwa cikin gidan. Mommy ce kadai a falo tana kallo. Shi yayi sallama kafin Noor. Amsawa tayi tana binsu da idanu. A hankali Noor ta sauke nata idanun sosai Mommy ta mata kwarjini. "Shigo mana" cewar Mommy tana kallon ta. Crotches ɗinta ne ya faɗi da sauri Hydar ya riketa ganin zata faɗin. Taɓe baki Mommy tayi tana dauke idanunta. "Thanks" ta fada muryarta na rawa. Zaunar da ita yayi yana faɗin "Noor here is my Mother" bata yarda ta kalli Mommy ba ta ce, " Ina yini? "Lafiya" Mom ta amsa a takaice. Numfashi Hydar ya ja yana kallon Mom ya ce, "Ina Farooq? 'Ya fita" ta ba shi amsa. "Ok" ya amsa ba tare da ya iya cewa komai ba. Miƙewa Mommy tayi ta koma ɗaki. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Noor ya ce, " Mu je na kaiki daki" da toh ta amsa. Taimaka mata yayi ta miƙe ya kaita har dakin late Mami. Kallon ɗakin ta fara yi a hankali tana sauke ajiyar zuciya. " Ga toilet if you need anything let me know" Kai ta gyaɗa a hankali. Fita yayi ya nufi dakin Mommy, a falonta ya ganta tana shafa kan Walid dake bacci idanunta akan wayarta tana latsawa. Zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun dake falon yana haɗe tafikan hannunsa waje guda kafin ya ce, "Dan Allah mommy kiyi hakuri" "Ai ni babu abinda zance" "amma ai fushi kike" ya faɗa yana marairaice fuska. "Eh ina fushi tunda kaki jin magana, ai jikin nata is not worst Allah kaji na rantse gobe nake so ka mai da ita gida! Ajiyar zuciya ya sauke yana amsawa da "in sha Allah" sai a lokacin ta ɗan saki ranta tana dorawa da faɗin"Wa cece kuma Amina? Ba tare da ya kalleta ba ya ce, " Tare mukai aiki da ita akan case ɗin general" "ok a wani unguwa take? "Rijiyar zaki" ya bata amsa a nutse. " Ok amma baka taɓa min zancenta ba" Mommy ta kuma fada. "Abunne yazo all of the sudden that's why" idanunta a kanshi ta ce, "Ka tabbatar dai kana sonta ko? Kai ya gyaɗa alamar eh. "Good, ya maganar shi Raihan ɗin ya ake ciki? "Dole fa sai yaje gidan yari! There is nothing I can do gwanda ma ki kwantar da hankalinki, yaje ya karo hankali dan bai da shi" jikin Mommy a sanyaye ta ce, "ai Umar ya ce bazai bari yaje prison ba! Iska Hydar ya furzar yana kallon ta ya ce, "Babu abinda uncle Umar zai iya dole Raihan sai yaje prison is better ku kyaleshi ya girbi abinda ya shuka" "ai shikenan, rannan da mukai waya da shi ya shaida min wai yana son wata ni kam abun ya ban mamaki" murmushi ne yayi escaping lips ɗinsa kafin ya ce, "Ba shi da hankali duk abinda ya aikata yana da gut ɗin da zai ce yana son girlfriend dinta? Cikin rashin fahimta Mommy ta ce, "Girlfriend dinka? "Uhm, Amina yake so kuma yasan ina sonta" shuru Mommy tayi na ƴan seconds kafin ta ce, "Ikon Allah! Yanzu kai Hydar akan budurwa har kake so kuyi faɗa da dan uwanka? Ba tun yanzu ba Ummi ta sha faɗa min kuna faɗa ashe akan mace ne? Ko baka san Raihan ba be kamata ace zaka bari mace ta shiga tsakaninku ba, he's your brother! "Na san da duk wannan Mom, amma ni Amina take so not him! " Shikenan Allah ya zaba mafi alkhairi" da Amin ya amsa yana miƙewa ya fice. Hydar bai dawo gidan ba sai goma saura, a falo yaga Abba, Mommy, Farooq da kuma Noor. Ƙarasawa yayi yana zama a kan kujera. "Sannun ku da hutawa Abba" cewar Hydar yana kallon iyayen na shi. " Yawwa Aliyu, ashe gobe zaku tafi? "Eh" ya amsa a hankali. Kai Abba ya gyaɗa kafin ya ce, "Allah ya kai mu" da Ameen suka amsa gaba ɗaya. Ta shi Noor tayi ta nufi dakin da aka bata. " Gobe in sha Allah by 11am zamu je ka sanar musu kaji ko? Sunkuyar da kai Hydar yayi ya amsa da "toh Abba"  "Tuzuru za'a angwance" cewar Farooq yana dariya. Ƙaramin tsaki Hydar yayi yana kallon shi ba tare da ya ce komai ba ya nufi dakin shi. Sai da yayi wanka yayi shirin kwanciya ya kwanta a kan gado tare da kara gudun ac ya dauko wayar shi yana dialing number Aminatu, bugu huɗu ta ɗauka ba tare da tace komai ba, " Kina jina? "Uhm" ta amsa a hankali. " gobe by 11am su Abba zasu zo ki faɗawa mahaifinki"  ajiyar zuciya ya sauke me ƙarfi kafin ta ce, " Hydarrrr... "Ina jinki" ya faɗa jin tayi shuru" "Ok Allah ya kaimu" daga haka ta katse wayar. A chan bangarenta kuwa kawai ta aminta da Hydar ne ko zata samu saukin abinda take fuskanta a wajen ƴan unguwa da mahaifinta. Umma ce ta shigo ɗakin tana kallon ta tace, "Ba kiyi bacci b? Miƙewa zaune tayi tana kallonta ta ce, "Eh Umma" zama Umma tayi a gefenta tana taba jikinta ta ce, "Allah ya isar miki Amina an cuceki an cucemu ƴan uwanki yadda suka lalata miki rayuwa haka Allah zai lalata tasu rayuwar, in sha Allah karshen su bazai yi kyau ba! Allah ya saka miki" Umma ta ƙarashe maganar tana goge hawayen da suka zubo mata. Itama Aminatun nata hawayen ta goge tana kallon Umma ta ce, " Umma Hydar ya ce gobe iyayen shi zasu zo karfe 11am ki faɗawa Abba"  Umma na kallonta ta ce, "Toh shi yasan abinda ya faru? Kuma yasan kina da wannan cutar ko ince cututtukan? A hankali ta gyaɗa kanta tana ɗorawa da faɗin, "ya san komai Umma, yace yaji ya gani kuma is better nima na aureshi akan abubuwan da nake fuskanta a gidan nan da unguwar nan! "Ina tsoron halin maza Aminatu, kinsan dai ba hauka yake da zai hada gado dake ba! Ya kike tunanin rayuwar aure zata yuwu keda shi? Moreover mahaifinku bai san da wannan cutar ba! Ni gaba ɗaya tsoran lamarin nan nake Aminatu" " Addu'a kawai za muyi Umma, ina son Hydar haka Allah ya tsara min rayuwata kuma in sha Allah zanyi kokarin ganin na cinye jarabawar" ajiyar zuciya Umma ta sauke tana faɗin"Allah ya shige mana gaba, ki kwanta sai da safe" daga haka ya miƙe ta fice.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now