Chapter twenty one

37 4 2
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 21*

          "Allah ya shige mana gaba ya bashi mace ta gari" da Amin suka amsa har shi Hydar ɗin. Ƙarfe 7 da yan mintina jirginsu ya tashi zuwa US. They spent a lot of quality times with their family living there more especially Hydar with his biological father, satinsu biyu suka dauko hanya har su Aunty Maryam da Mustapha tare da yara, Raihan ma yayi interview kuma yaci an ce masa ko wani time za'a iya nemansa ya zamana cikin shiri.  Tun safe Aunty Saudah da Amina suke gidan Raihan, tare suka gyara ko ina har girki Aunty Saudah tayi masa sannan ta saka Amina ta shirya tayi kyau abinta. Gidan su Mommy ta wuce bayan ta bar Amina a gida. Bata daɗe da isa ba suka iso gidan,  "Ashe har da ku za'a taho? Cewar Mommy tana kallon Aunty Maryam. "Eh wallahi mu dan kwana biyu mu koma an mun daɗe bamu leko ba, su Farooq dae an chan Russia" Aunty Maryam ta ƙarashe maganar tana dariya. "Bari ya dau ƴar mutane ya kaita inda ba uwa bare uba, ga yaro karami" zama Aunty Maryam tayi tana faɗin, "wallahi fa, Allah dae ya basu zaman lafiya, ni kam Aunty Zarah haka nan za'a zubawa Hydar idanu? Hydar dake zaune a falon ya miƙe yana wucewa daki. "Mustapha muje daki" cewar Abba yana kallon Daddy. "Oh sannunku da zuwa, Yaya" cewar mommy tana kallonsu. "A'a ku gama gulmar jama'ar" cewar Abba yana nufar daki. Daddy kuwa murmushi yayi ya ce, "Sai yanzu kika ganmu kenan? "Kuyi haƙuri dan Allah" bai ce komai ba ya wuce. Kallon su Ahmad Mommy tayi tana faɗin, "Kuke kuyi wanka ku huta ko, ke Fatima kije dakina tare da Khadijah" da toh suka amsa sannan suka miƙe tare da barin falon. "Ni kam Aunty Zarah ko irin ta Raihan ne ayi wa Hydar mana, zaman nan fa bai da amfani haka ya kai 35yrs ko fi ma fa idan ban manta ba! Bazai yu kam a zuba masa na mujiya ba ai ba shi yayi kansa ba" "Ku bashi time Dan Allah" cewar Raihan yana kallon su. "Kai tashi ka tafi gida" cewar Aunty Saudah data fito daga kitchen yanzu. Miƙewa yayi yana faɗin, "Idan naje gidan me zanyi? "Ai matarka na chan, zaka wuce ko kuwa? Aunty Maryam ta faɗa tana ɓalla masa harara. Jakarsa ya rataya sannan yayi musu sallama ya fita. "Ta shi muje kiyi wanka ki huta ga abinci nan, Saude dan Allah ki kawo musu abinci daki" "Toh Yaya" ta amsa tana murmushi.  

      Raihan kuwa bayan ya isa gida a falo ya tarar da Amina tana kallon TV, tana jin footsteps ta dan juyo ta kalleshi. Karasa shigowa yayi tare da kulle kofar idanunsa a kanta ya ce, "Lafiya? Juyawa tayi ta cigaba da kallonta ba tare da tace uffan ba. " Babu sannu da zuwa? Volume ta kara a TVn alamar ya dameta. Ƙarasowa yayi ya kwace remote din ya kashe TVn. "Kallo fa nake" "Bakiyi missing dina ba? Ya fada yana bin jikinta da kallo. "Oh baka samo baturiyar ba? "C'mon! Kina da matsala, duk lokacin da nayi kokarin na zama so nicely sai kin bata min rai! Idanunshi ta kalla for a few seconds kafin ta dauke da sauri. "Sannu da zuwa" ta faɗa tana nufar stairs. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya bi bayanta. Tana jin footsteps dinsa ta diba a guje dan ta dauka kamata zaiyi. Ƙaramin tsaki yayi ya wuce ɗakinsa. Amina kuwa fadan Ummanta ne ya dinga mata yawo akai, chan ta turo baki ta sake fitowa daga dakinta ta sakko kasa ta haɗa masa abinci. Fitowar Raihan daga toilet ba jimawa ta murda handle din kofar. Wayam taga falon nasa, bedroom ta nufa bayan ta ajiye tray ɗin abincin a falo. "Ka fito ga abin... bata ƙarasa ba sakamakon ganinsa da tayi naked trying to tie up his bathrobe. Juyawa tayi da sauri tana zaro idanu. "ina zakije? Ya fada da sauri. Aikuwa a guje tayi hanyar barin bedroom ɗin. Biyota yayi amma ina har ta fice a 360. Dakinta ta shiga ta kulle zuciyarta na bugawa da karfin gaske! Bazata taɓa manta abinda ya faru tsakanin su ba, yanzu kuwa tasan zata iya mutuwa idan ya sake yi. Bata wani dade da zama ba taji knocking, shuru tayi tana matsawa chan karshen gado. Shurun data ji an dena bugawa ya saka ta taso a hankali ta leka ta jikin kofa taga ba kowa, buɗewa tayi a hankali tana lekowa, ihu ta saki kafin ta rufe kofar ya rike gam. Kasa jan kofar tayi hakan ya saka ta saki tana turo baki ta ce, "Ni kar ka datse min hannu" "What are you afraid of? Ya faɗa yana shigowa dakin nata. "Ba komai kaci abinci ka kwanta ka huta" "eh ai abincin nazo ci" ya faɗa yana rike mata hannu. "Ai na kai maka falonka" "shiii! Yana dora yatsansa akan lebanta. Buda baki tayi ta cijeshi. "Auchh! Ya faɗa yana yarfe hannu still be saketa ba daga rikon da yayi ma ta. " Yaya dan Allah ka cikani" "Idan naƙi fa? Kai ta girgiza tana shagwabe fuska. "Hannuna zafi" ta faɗa hawaye na biyo kuncinta. Sassauta rikon yayi yana faɗin, "Sorry" hawaye ne kawai yake tsiyaya a idanunta kirjinta na bugawa, ita sam bata so taga Raihan yayi laushi haka sau da dama yakan zuwar mata da abinda take jin haryanzu baza kuma aminta da shi ba. "Dan Allah ka sakeni" ta faɗa tana jan majina. "Not today please! Sosai idanunsa ke rikitata. Kuka ta saki sosai tana kokarin kwatar kanta daga gare shi. "Ya isa mana! Zauna" ya faɗa yana zaunar da ita a kan gado. " Kiyi shuru ki kwantar da hankalinki, kina jina? Kai ta daga alamar eh. "Good, inaso ki sani I'm a human being kuma mutum me lafiya, kusan 6months da auren mu we just had an affair once! Only once Amina! Ai na miki kokarin, ni namijin aure ne so Please ki zamar dani cikakken namijin aure! Though nasan na aikata laifuka a baya but ban taba aikata zina ba, kece mace ta farko dana fara sani, kuma naji dad'i nima daya kasance ni ne namijin daya fara saninki, nasan s**x is not the only thing in marriage amma cikin kaso 100 za'a iya bashi 40%, duk haukan da kike nasan by time kika kara mallakar hankalin ki zaki daina" "Ai kace baka sona! Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi. "Nasan na fadi hakan, you're not my first love amma ina fatan ki zama last, we aren't related by blood amma ina jinki har cikin zuciyata, zuwana US ya saka na kara fahimtar hakan, your childishness and everything about you Amina" Shuru tayi zuciyarta na bugawa. Janyota yayi jikinshi yana shafa bayanta. "Dan Allah kayi hakuri ka kyaleni" "i can't" Kuka ta saka me karfi sosai. Runtsa idanunshi yayi yana sakinta. "Sorry" daga haka ya mike ya fita ya barta. Har yamma Amina na daki sai bayan sallar isha'i ta fito. Bata ga kowa a falon ba, kitchen ta nufa ta dumama abinci taci ta ajiye ragowar, fitowa tayi tana sauke ajiyar zuciya. Kofar falon aka bude, Raihan ne ya shigo hannunsa rike da Leda yar karama. "Fita kayi? "Eh" ya amsa yana zama a kan kujera. Zama tayi a gefan sa tana faɗin, "Yaya ya maganar makarantar tawa? "Waye yace miki zaki cigaba da karatu? Shuru tayi tana kallon shi. "Ki cire ma maganar fara University a ranki" ya kuma faɗa yana mikewa ya wuce sama. Bayansa ta bi tana faɗin, "Ai dai kasan kowa yana cigaba da karatu a dangin mu! "Toh yar dangi! Daga haka ya shige ɗakinsa. Bude kofar dakin tayi tana cewa, "Wallahi sai na faɗawa mommy abinda kace" juyowa yayi yana haɗe rai ya ce, "Allah yasa naji kin kai zancen nan gida! "Wai kai Yaya an ce maka haka akeyi? Wannan ai tauye hakkine! "Nima ai kina tauye min nawa hakkin" daga haka ya kunna TV ko kallonta be kara yi ba. "Haba dan Allah Yaya" "Kinga karki dameni" zama tayi tana kallonsa ta ce, " Sai ku hana matanku karatu amma idan kun kai matanku asibiti kuce kunfi so likita mace ta duba ta! Ita ba'a sonta a gidansu aka barta ta cigaba da karatun? Sannan idan zaku karo wa matanku kishiya ku je ku dauko me ilimi ita kun hanata tun tana da damar yi" wani smirk yayi kafin ya jiyo ya kalleta few seconds later ya ce, "Kalleta! Kallon screen din wayarsa tayi. A very cute and beautiful lady ta gani ta sha kyau cikin riga da wando looking so elegant and matured kana ganinta kasan kuɗi sun zauna ga komai nan chas² Breast dinta are so full haka ma waist dinta. "Ina ruwana da ita toh da kake nuna min" "so nake ki ganta ai saboda ita zan aura, sunan ta Aminatu amma Noor ake kiranta, nasan ita bazata taba hanani abinda kike hanani ba! Ita da take ma da abun duniya" daga haka ya tashi ya barta a wajen. Hawaye taji masu zafi sun biyo kuncinta. Har karfe 10 tana zaune a wajen taci kuma ta godewa Allah. Raihan kuwa ya ɗauka ta fita, ya fito daukat ruwa ya ganta ta kife kai a kujera. "Amina! Ya kira sunanta. Ɗagowa tayi tana goge idanunta. "Kuka kuma? Me akai miki? Kamar jira take ta kuma fashewa da kuka har da shassheka. Inda take ya ƙaraso yana zaunawa ya ce, " Meyafaru? Dan sincerely ya manta abinda yayi mata. "Wallahi sai na fadawa Umma abinda kace, bayan nice ma na taimake ka na aureka sai ka dinga min gori, ai ba ni na bawa kaina irin wannan halittar ba, haka Allah yake son ganina shiyasa yayi ni haka, ita din da zaka je ka auro sai kayi ta aurota" Murmushi ya ɗanyi kaɗan yana faɗin, "Kiyi haƙuri toh, dena kuka" kwace hannunta tayi da sauri tana mikewa tsaye. Shima mikewar yayi yana rikota da kyau whispering in her ears. Nunfashi taja a hankali tana kallon Beard ɗinsa. "So please stay calm" ya faɗa yana kallon cikin idanunta. Sauke idanun ta tayi daga cikin nashi. A hankali yayi hugging dinta ko kirjinsa bata kawo ba saboda yadda ya fita tsaho. " Ke dince you're too small and tiny" "Bacci xanje nayi" ta fada tana barin jikinsa. Daukarta yayi kamar baby yana faɗin, " Yau da ni zakiyi bacci" bata ce komai ba har ya sauketa a kan gadon shi. Falo ya koma ya dauko ruwa tare da kashe filitar falon. Tun kafin yayi shirin bacci Amina ta fara bacci duk ta takure waje daya. Sai kusan 2am Raihan ya gama saloli sannan ya hau kan gadon yana lumshe idanun shi, kusan kullum sleepless night yake samu, yana yawan yin horrible dreams more especially akan abinda ya aikata a baya. Amina ya janyo jikinsa bai dau lokacin ba bacci ya dauke shi.
        Wa she gari da safe Hydar na dakinsa yana sipping din tean da Khadijah ta kawo masa wayarsa ta fara ringing. Sau daya ya kalleta kafin ya dauke kai ya cigaba da shan Black tea dinsa. "Bai taba tunanin neman macen aure yana da wahala ba sai yanzu, tunda har Abba ya fara magana yasan abun baxai zo masa da sauki ba, she kawai zai basu dama koma wacece a aura masa! Macen da yake so baya jin zai iya aurenta! Karar da wayarsa ta cigaba da yi ne ya saka shi dauka tare da karawa a kunne. "Hydar it's me Noor! Gobe zan shigo Nigeria and in sha Allah ina sa ran za'ayi releasing din Tahir" "Then? Ya faɗa yana sauraronta. " Kasan ni kaɗai ne family ɗinsa, we're starting afresh together in sha Allah, zamu koma Paris tare" "then? Ya kuma faɗa. "Nothing! Ta bashi amsa harda murmushinta. "Ain't you guys getting married? Bai san lokacin da maganar tayi escaping ba. "If he's ready I can give him a second chance I have no other choice and Ina ganin Tahir sai yafi ko wani namiji gani na da daraja so I think is the best decision I will ever make" "Ok, so meyasa kikai kirana? Daga dayen bangaren ta ce, " Just to inform you and if possible kazo Abuja mu haɗu, nasan be zama lallai mu kara ganin juna ba" "Ok" daga haka ya kashe wayar. Iska ya furzar yana hadiye wani abu da ƙyar. Shayinsa ya cigaba da sha amma hankalin sa baya tare dashi. Ji yayi an riƙe hannunsa, by then yaji yadda harshensa ke radadin zafi. Kallon Raihan yayi from head to toe. "Baka jin zafin shayin? Ji yadda yake hayaki fa" cup ɗin hannunsa ya ajiye yana mikewa ya shige toilet. Bai ɗau lokaci ba ya fito yana tsane ruwan fuskar shi. "Ɗazu Noor ta kirani za'ayi releasing din Tahir gobe zaka je Abujan ko? Kai ya gyaɗa yana zama a gefan gado. "Faɗa min meyafaru? "Nothing' Hydar ya amsa yana jona wayarsa a charji. " Yaushe ka fara boye min abubuwa? Kasan this isn't our deal? Ina son sani just tell me! Cewar Raihan yana kallonsa. Ganin yayi shuru ya sake faɗin, "I'm here for you and we promised each other no more hiding secret, na faɗa maka secret dina da matata irin zaman da muke You advice me and I'm trying to catch up things with her why won't you trust me that way and voice out your problem? I'm the only friend you have also your brother Ina jinka Hydar" ajiyar zuciya ya sauke yana kallo Raihan ya ce, "Idan nace maka nima bansan me yake damuna ba zaka yarda? Kai Raihan ya girgiza alamar a'a. "That's the problem, nima bansan me yake damuna ba! I just can't get her off my head! " da kace baka sani na? Yanzu fada min wacece? Raihan ya faɗa yana masa wani kallo. "Amina! Hydar ya faɗa without any hesitation. "Wai yaushe zaka fuskanci future dinka ne Hydar? Amina is gone! Just accept i... "Not her! Yayi saurin katse shi. Cikin rashin fahimta Raihan ya ce, "Toh wa kake nufi? "Noor! Ya kuma bashi amsa. "Noor! Raihan ya maimaita sunan cike da mamaki. "Na ɗauka kace min baka sonta? So tell me what happened? "Nothing Raihan, I love that girl from the exact day I set my eyes on her picture, kasanni bana following mata masu posting din kansu a media but I ended up following her liking her videos and her campaign back then, I just love everything about her, I have being hiding it for a while kafin na sanar da ita time din mun hadu a Abuja, Raihan i love her till date! "Kai tsaya! Toh ita Aminar daka aura fa har ka daina yi wa mutane magana saboda rasuwarta kana blaming din mutane? Cewar Raihan cikin confusion. "Ina matuƙar tausayinta ne musamman idan na duba da irin rayuwar data tsinci kanta wani lokacin ma nake ganin kamar fault di nane saboda da ban ajiyeta ba a wannan daren da duk hakan bata faru ba, na shiga tashin hankali lokacin data rasu saboda ina tunanin dalilin maganganun dasu Mommy sukai adakin ya saka ta saka daurewa tayi committing suicide kasan dama already she's depressed, but I never loved her! Iska Raihan ya furzar tabbas tunda Hydar ya zama so open haka abun ba karamin cin shi yake a zuciya ba. "But Hydar meyasa ka dinga avoiding dinta? Nasan itama tana sonka" "Yes I can tell that also, amma i think Tahir deserves her more" "Meyasa zaka ce haka? Cewar Raihan yana dafa shi. " Saboda a yanzun tana ganin Tahir yafi sonta kuma sai yafi ganin darajarta saboda issue din daya faru tsakanin su, kawai ka tayani da addu'a"  Raihan ji yake kamar yayi masa kuka. Tunda yake da Hydar be taɓa zama so Open ba kamar yau, da wuya dai kaji abinda yake cikin Hydar gaba ɗaya. "In sha Allah, Allah zai maka zabin alkhairi" da Amin ya amsa yana jingina jikin gado. Har yamma Raihan yana gidan, abinci ma sai kawo musu ake daki, zuwa lokacin Hydar ya dawo normal dinsa kai bazaka ce yana da wata damuwa ba. Bayan sun dawo daga sallar isha'i Raihan ya wuce gida. Dakin sai yayi masa fadi no one to speak with gashi mahaifinsa sun wuce Abuja dazu. Tashi yayi ya nufi dakin mommy. A zaune yagan su Abba yana tayata yankan farce. " Soyayya ta motsa kenan" ya faɗa yana yar dariya. "Da dai ba ruwanka wallahi amma yanzu kai na ka koyi magana" Abba ya faɗa yana yar dariya. "Uhm" cewar Hydar yana zama. "Toh shikenan an gama, bari naje wajen Umar, Hydar ko zaka je? "No Abba, Allah ya tsare" da Amin Abba ya amsa yana ficewa. Sai da Mommy ta zubar da farcen da Abba ya yanke mata sannan ta zauna kusa da Hydar ta ce, "Wani abun ya faru ne? Kai ya girgiza yana gyarawa ya kwantar da kanshi a kan cinyarta. A hankali ta sauki nunfashi tana faɗin, "Nasan be zama lallai ka fada min ba, amma dole kana da damuwa tunda har ka kasa zama kai kadai ka taho nan wajena, inaso kasan duk abinda ya faru da bawa toh daga Allah yake kuma ka dage da addu'a in sha Allah watarana sai labari, kai baka ga yadda dan uwanka ya nutsu ba kamar ba shi ba? Toh haka rayuwa take tana juyawa a lokacin da bakai zato ba, indai akan maganar auren da akai maka ne ka tsaya ka nutsu ka zabo wadda kake so kaji ko? Tashi zauna yayi yana kallonta ya ce, " Bani da wani zabi ki zaba min duk wadda kika ga ta miki inside or outside the family" Kai ta girgiza kafin ta ce, "A'a Hydar, abinda ya saka kaga anyi wa Raihan haka saboda abubuwan da suka faru, muddin yaje nema a waje toh za'ayi ta cecekuce ana dawo da baya, kai dai kayi ta addu'a matarka na nan zuwa in sha Allah" Shuru yayi zuciyarsa ma tsananta bugawa. Shi bai san ma ta yaya zai iya fadawa Mommy Noor yake so kuma yana ji yana gani zata tafi ta barshi.....

Autarmama ce

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now