Chapter fifteen

69 6 1
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 15*

        Pictures ɗin dake gaban shi yake kallo ɗayen bayan ɗaya kafin ya ɗago ya kalli Goje ya ce, "Ka tabbatar this is him? "Kalli da kyau mana ranka ya daɗe! Cewar Goje yana kuma yin dai² da hotunan. " Kana so ka ce min shi da Hydar uwa daya uba daya suke? Sannan wannan ƙaninsa ne wannan kuma ƙanwar sa? "Tabbas ranka ya daɗe! Raihan spy ne a cikin mu! Har chan Kano na bishi kuma na fi sati ina bibiyar shi, kafin ya bar nan Abuja har barazana ya min akan sai ya tawatsa ni saboda incident ɗin daya faru we raped his girlfriend ashe ba Gf din Hydar ba ce Raihan ne yake sonta! Yayi rantsuwa akan sai yaga bayan mu, tun daga lokacin na fara zargin sa kuma already nasan yana yawan zuwa Kano nayi deciding na bishi dan naga me yake yi a chan dan a yadda muka sani bashi da kowa, shi ne na gano wannan information ɗin" Ran Dad a ɓace ya ke jinjina kai! Wato Raihan raina masa hankali kawai yake yi! Ya gama yarda dashi ya san sirrinsa ashe spy ne? "Idan kana so za mu iya kamo shi" "kai ma kasan Xexe ba kanwar lasa bane! Abinda za kuyi shine inaso ko ta halin ƙaka ku nemo inda Amina take ku kawo min ita! Har da wannan! Ya karashe maganar yana nuna Mami dake jikin hotan. "An gama ranka ya daɗe! Cewar Goje. "Ta haka ne kawai Raihan zai zo da ƙafafun shi! Zai san yayi betraying ɗina! Daga haka ya miƙe ya bar Goje a wajen.

*Kano*

      Hydar da Raihan ne tsaye veranda suna magana, a nutse Hydar yake kallon Raihan da ke magana, bayan ya kammala Hydar ya kalle shi ya ce,"Toh ni me zanyi maka? Kai ka saka kanka a ciki! Maganar Aminatu kuwa ka cireta a ranka" " kaima kasan i can't! Itace macen dana fara so bazan iya yarda na cireta haka kawai ba, sannan ni ba ina maka magana akan ka kula dani ba i can take care of my self! Ina yi maka magana ne akan su Mami, I saw someone taking pictures of us lokacin da muka je shopping, I'm not sure amma Ina zargin mutanen Gov. Ne" shuru Hydar yayi na ɗan lokaci kafin ya kalleshi ya ce, " Meyasa kake tunanin shi ne? "Saboda mun sami matsala da Goje na lura kuma kamar ya daɗe yana zargina, ina tunanin shi ne yake saka min ido kuma in dai shine by now yasan ina da ahali, the worst part ɗin ma shine Gov. ya gane cewa ni da kai ƴan uwa na, zai ɗauka betraying ɗinsa nake kuma na san waye shi zai yi ƙoƙarin ganin na kawo kaina gareshi maybe he's going to take my dear one! I bet Amina ko someone else dae! "Kaga abin nake guje maka ko? Yanzu shi har yana da gut ɗin da zai sake ɗauke Amina? For good 1months bata da lafiya all because of him! Kaga Raihan kawai ka kai kanka wajen police komai zaizo da sauki" kai Raihan ya girgiza yana kallon Hydar ya ce, "I can't do that Hydar ban taɓa tunanin zan yi regretting abubuwa nan kusa ba saboda na ɗauka banda wani future anan gaba! I love Aminatu and I want to spend the rest of my life with her! Wani ɗan iskan kallo yayi masa sai kuma ya ce, " Amina kuma tafi karfin ka! Daga haka ya bar wajen. Fita yayi daga gidan gaba ɗaya yana so ya samu nutsuwar da zai san yadda zai ɓullowa lamarin saboda his family's safety! Gidan sa ya nufa, a compound ɗin gidan yaga likitar dake kula da Noor da alama ta gama tafiya za tayi.  Ƙarasawa yayi in da take yana faɗin "Abdallah yana ciki ne? "Eh ai anan nazo na same shi" "Ok, ya jikin nata? "Ko wani lokaci zata iya farkawa ku dai cigaba da addu'a, na bawa Abdallah list ɗin abubuwan da za'a siyo Please a siyo kafin nazo gobe sannan tunda ɗinkin nata ya warke is better a siyo mata riguna marasa nauyi kuma masu fadi dogaye idan na goge mata jiki a dinga saka mata, yawwa kaga har zan mata, result na test ɗin da akai mata" buɗe jakarta tayi ta ciro tana kallonsa ta ce, " Congratulations" daga haka ta bar wajen. "Congratulations? Ya mai maita kalmar yana kallon abinda ta bashi. Da sauri ya buɗe takardu ne har biyu, daya hoto ne da akai ya nuna komai na ciki is ok dangane da aikin da akayi mata, ɗayen kuma PT ne kuma ya nuna positive she's 2months pregnant. Ninkewa yayi ya saka a aljihu, kafin ya karasa wayarsa ta fara ringing. IG ne hakan ya saka ya ɗauka da sauri tare da karawa a kunne. " Aliyu ya kake? "Fine sir! Ya amsa masa. Daga ɗaya bangaren IG ya ce, " Anga Abbas amma yana ƙarƙashin kulawar likito ci his condition is severe,  take care of your self in sha Allah next month zamu shigar da ƙara" "Ok Allah ya bashi lafiya" "Amin, naji Amina za tayi resigning is it true? "Yes sir! Hydar ya amsa masa. "Ok aure zatayi ne dai ko? "Yes sir! Hydar ya kuma bashi amsa. "Ok Bye! Daga haka ya kashe wayar. Cikin gidan ya nufa, a zaune yaga Abdallah yana kallo yana cin abinci. "Sannu da kokari" cewar Hydar yana kallon shi. "Ƙoƙarin kam ina yi, tunda ka hanani tafiya US! Murmushi ya ɗanyi kafin ya ce, "Ina list ɗin da aka baka? A aljihun gaban rigar shi ya ciro yana miƙa masa tare da faɗin "Wallahi duk ranar da Abba ya gane ka ajiye wata a cikin gidan nan kashinka ya bushe ƙayau" "Waye zai faɗa musu? Bayan babu wanda yasan ma na siyi gida? Kai dai kawai ka ce min bakinka yana ƙaiƙayi kana so ka fada a gida shikenan" dariya Abdallah yayi ya cigaba da cin abincin shi. Ɗakin da Noor take ya nufa, daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta, daga bisani ya fita tare da rufe kofar. "Likitan fa ta ce a dinga karanta mata stories" da mamaki Hydar ya ce, "Wani irin labari matar marabarta da matacce numfashi wanda shima da taimakon oxygen? "Ta ce wai zata ji! A dinga yi mata, kuma kar ka ce na dinga yi dan bazan iya ba, Daddy ma ya fara min faɗa bana yawan zama a kasuwa"  "Naji" Hydar ya faɗa yana nufar ɗakinsa na gidan. Bai daɗe a kwance ba bacci ya dauke shi dan daka kwana biyu ba wani baccin kirki yake samu ba....

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now