Chapter Two

109 6 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 2*

       Da sauri tabi bayan shi, kafin ta isa har ya shiga lifter, ƙoƙarin tsayar da lifter tayi amma bata samu nasara ba idanunta cikin nashi har lifter ta karasa rufe. "Shi ne?! Ta tambayi kanta. "No! Me zai kawo shi wajen dad? But the eyes are so thesame" ta kuma faɗa tana tunanin idanun Raihan. Iska ta furzar ta bakinta tana komawa ofis ɗin Dad. Zama tayi tana kallon dad ta ce, "Daddy waye wanda ya fita da baƙaƙen kaya yanzu? "Wa kenan? Cewar Dad yana kallonta. "Just now fa ya fita yana sanye da baƙaƙen kaya da Pcap" ta kuma faɗa tana nuna hanyar waje. "Oh! Wai Xexe! Yana kai min aike ne mostly lafiya dae? Kai ta girgiza tana ajiye files ɗin hannunta ta ce, "Please sign them, Ina shoe's ɗin? "Suna store bari na saka a fitar miki da su, ki saka a raba biyu ki kai rabin orphanage" "Ok in sha Allah, Allah ya bada nasara Dad" ta ƙarashe maganar tana murmushi. Da Amin ya amsa sannan ya bata katin dake buɗe kofar store. Tahir ta kira tare da workers ɗin dad aka kai takalman mota. Direct orphanage suka fara nufa, kayan abinci, na sawa da magani tayi donating sai da akai hotuna sannan suka tafi, inda suka je jiya ta koma sai data karasa aikinta tsaf sannan suka bar wajen... Kasancewar yau ɗin jikinta da sauki asibiti ta saka suka wuce .. tun da ta shigo cikin asibitin mutane suka fara ranki ya daɗe, ward ward ta dinga bi duk me ƙaramin karfi sai data taimaka nan ma sai da akai hotuna sannan suka baro.

    Bayan sun dawo gida wanka tayi tana kwanciya, mutumin dazu ne ya fado mata, ita kam sosai idanunsa sukai mata kama dana Raihan, amma ai ba yadda za'ayi RAIHAN din yazo har office din Dad me zai kawo shi ma? Ƙaramin tsaki tayi tana ɗaukar wayarta dake charji, kirane ya shigo bata ɗau lokaci ba ta ɗauka tana faɗin " *ASIYA* ya kike? Daga ɗayen bangaren Asiya ta amsa da "Lafiya lau fa *AMINA* zan shigo kina gida dai ko? Sai da Noor tayi murmushi sannan ta amsa da "Ina gida, hope dae ba fita za muyi ba? "Of course yes, kema kinsa fita ce, kwata² fa banyi gyaran gashi ba, ke asif ba bakya ɗokin bikin" "no ba haka bane kinsan idan zaɓe ya matso, shikenan kizo nima sai ayi min" da yawwa Asiya ta amsa sannan ta ɗora da faɗin "Za ki dae je dinner ɗin ko? Sai da Noor ta juya idanunta kafin ta ce, "Kinsan fa ni ba wai Kano na taɓa zuwa ba" "Na sani Please dae ki daure, sai ki zauna a hotel tare da su *JUWAIRAH* "shikenan zan fadawa Mom dan nasan Dad bai da matsala sai kinzo ɗin " daga haka sukai sallama. Ta shi Noor tayi ta shirya cikin Abaya, fitowa tayi tana ƙwallawa Saddeeqa kira. Da sauri ta fito daga kitchen tana faɗin "Gani" "Zan fita idan mom ta dawo kice na wuce saloon ni da Asiya, kafin na dawo kiyi min grilled fishand it should be spicy" "An gama" cewar Saddeeqa kanta a sunkuye. Noor bata ƙara cewa komai ba ta nufi ƙasa. Tana zaune a falon kasa Asiya ta shigo, itama yar gayu ce kamar dae Noor kuma daga gani kasan Naira ta zauna. "Amarya! Cewar Noor tana murmushi. "Ke kuma ango ko? Ina mom? "Bata nan fa" Noor ta bata amsa. "Ok, muje ko? Cewar Asiya. Ta shi Noor tayi tana faɗin "Mun daɗe bamu haɗu ba fa, kin ƙara kyau sosai lallai Isma'il yana shan gyara" Dariya Asiya tayi tana shiga mota. Mota biyu ce ta raka su zuwa saloon din, har baƙin ƙunshi Noor tayi iya hannu. Amarya kuma har da ja. Sai bayan magrib prayer suka baro saloon din, har gida suka mayar da Asiya sannan itama suka dawo gida. Bata tarar da kowa a falon ƙasa ba, stairs ta wuce, a zaune taga Dad a falon sama yana kallon News. "Kin dawo? Ya faɗa yana kai duban shi gareta. Zama tayi a gefen shi tana faɗin "Eh, ina mom? "Tana daki, ya campaign ɗin yau? "Komai lafiya Lau, ai in sha Allah kaine governor Daddy, yawwa daddy Dan Allah kayi wa Mom magana kaga wanda Asiya zata aura ɗan Kano ne, kuma bayan an ɗaura aure dangin mijin zasuyi dinner a kano kuma kasan I'm her best friend be kamata ace banje ba, Nasan kai baka da matsala da zuwana inaso kayi wa Mom magana Please" sai da yayi murmushi kafin ya ce, "Shikenan, yaushe ne? "Jibi ne fa za'a fara, on Friday kuma zamu tafi" "Ok, that's Good, kema ya kamata ki fito da naki mijin ko? Relaxing tayi a kujera tana kallon TV ta ce, "Dad nifa bazan ɗauki raini ba that's why I'm still single besides bana son yin aure yanzu " 23yrs fa Noor? Haka kike so kiyi ta zama? Tashi tayi tana faɗin"Na gaji zanje na kwanta " da good nite ya amsa sannan ta wuce. Wanka tayi sannan tayi sallah ta kwanta bata dade ba bacci ya ɗauketa.  Washe gari shirin office tayi, ta riga mahaifinta isa, bayan tayi settling ta fara duba abubuwan da suke dasu ahead of them da yadda zasu cimma komai kafin a fara zaɓe. Secretary ɗinta ce ta kirata, ɗauka tayi tana faɗin "What? "Wani ne yazo yana nemanki, yace ke kika bashi kati" "ok" Ta faɗa tana ajiye telephone ɗin. Knocking ɗin kofar akai sannan aka shigo. Kallonsa tayi from head to toe, very dirty daga inda take tana jiyo irin tsamin da yake yi a ƙallah zaiyi 25yrs. "Ina kwana? Ya faɗa har da durkusawa. "Lafiya tashi zauna a kujera" ta faɗa tana ƙoƙarin saita expression ɗin fuskarta. Da sauri ya zauna yana washe baki ya ce, "Allah ya biyaku, dama innata ce ta bani katin ta ce ke kika bata inzo zaki bani aiki" Murmushi ta ɗanyi dan sai yanzu ta gane shi. "Ina CV dinka? Ta faɗa tana kallon shi. "Na'am? Cewar shi yana zuba mata idanu. "CV, takardun neman aiki" ta mai maita masa. "Au, babu ai, iya ka cina secondary kuma ko waec da neco banyi ba" Shuru tayi na ƴan dakiku kafin ta ce, "Shikenan, kaga nan dae bama ɗaukar wanda be karatu me zurfi ba, alfarma ɗaya zan maka zan baka aiki, zaka dinga goge goge da shara, duk da dai akwai masu yi amma zan baka wannan opportunity ɗin saboda bazaki ji dadi ba idan nace ka tafi saboda ni innarka ce min tayi kayi karatu shiyasa na baka katina kazo inga ko da aikin da zan iya baka so na saka a nemo maka, amma tunda ta kasance haka, kullum da safe kafin 7 kazo ka share min offis sannan ka goge, kuma ya zamana kana lura sosai da aikinka banda karambani kaji ko? Zan dinga baka dubu sha biyar a wata" godiya ya shiga yi mata ba ƙaƙƙautawa. "Ta shi kaje zan saka a nuna maka yadda aikin yake gobe zaka fara" godiya yayi mata sannan ya fita, room freshener ta fesa kamar zata karar dashi kafin ta koma ta zauna tana sauke numfashi.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now