Chapter twenty

47 4 2
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 20*

         "Zarah ya kike? "Lafiya Bilkisu me nake ji haka? Sam baki kyauta ba kam kawai sai ki kwace masa mata? Kinsan halin Aminar itama ba kirki ta cika ba, zan turo Hydar yaxo ya dauketa dan Allah ki dena biye wa sakarcinta. Daga haka ta katse wayar dan bata son umman ta ce wani abun. "Kira min Hydar" mikewa yayi ya fita compound ɗin gidan. A zaune yaga Hydar ɗin kusa da gateman suna hira. Karasawa yayi kafin ya ce wani abu Hydar ya rigashi da faɗin, "Lafiya? "Mommy na kira" bai amsa ba ya mike Raihan yabi bayan shi, a falo suka tarar da mommy. "kaje gidan Aunty Bilki ka dauko Amina! Da toh ya amsa kafin ya ballawa Raihan harara ya fice. Sai daya siyowa Aunty Bilki best deodorant dinta kafin ya isa gidan, sun sha hira har 10pm kafin ta saka Amina ta shirya ta biyoshi. Pharmacy ya kaita aka bata drugs duk da cewar ta sha a gidan Umma. Sai da suka ɗau hanyar gida kafin ya ce, "Ki dinga shan drugs ɗinki da zarar kin fara jin alamar menses ɗinki, kuma ki rage cin zaƙi" kai ta gyaɗa alamar toh. "Allah ya kara sauki " da amin ta amsa tana kwanciya jikin kujera. A compound suka tarar da Raihan, ko shiga gidan ba suyi ba ya kama hannun Amina ya saka cikin mota. Taɓe baki Hydar yayi ya wuce cikin gida. A falo ya tarar da mommy har zai wuce ya dawo ya zauna yana faɗin, " Daddy ya ce zanje US" "Ai na dauka bazaka min maganar ba tunda baka da hankali! "Kiyi hakuri" ya faɗa a hankali. " kai ka jiyo, idan kaje tare zaka dawo da Abba! Kar ka zauna kuma bar ganin na zuba maka ido kana abinda kaga dama ka fito da matar aure idan ba haka ba ni zan zaba maka tunda ka mata birjik a dangi! Ga kanwar Sadeeq nan masters take yi ma abunta a Paris ballantana kace yarinya ce kamar yadda kace da Amina! "Duk abinda kika ce yayi" daga haka ya wuce. Toilet ya shiga ya dau lokaci kafin ya fito yayi shirin bacci, lumshe idanun shi yayi little moment ɗin da yayi spending da Aminatu ya kasa goge su cikin kwakwalwar sa, be taba tunanin yadda yake jinta a zuciyarta ya kai haka ba, shekara guda da rasuwar ta amma ji yake kamar yau abin ya faru, mikewa zaune yayi yana furzar da iska, wayarsa ce ta fara ruri, ganin sunan Noor ya saka shi silencing wayar dan kar ma ta dameshi da kira. Knocking ɗin kofa yaji, mikewa yayi ya nufi ƙofar tare da kiran sunan mommy. Amsawa tayi, ajiyar zuciya ya sauke yana bude kofar, kallonsa tayi a nutse ta ce, " yau ma ka kasa baccin? Sauke idanun shi yayi ya bata waje ta shigo, rufe kofar yayi ya zauna a kusa da ita a sanyaye ta ce, " Kayi haƙuri Hydar" hannunta ya riƙe yana faɗin, "Ni zan baki haƙuri, I left you for almost a year! Kanshi ta shafa tare da sumbatar goshin shi ta ce, "Na yafe maka Hydar, inaso ka manta da komai ka fuskanci future dinka, Amina ta shigo rayuwarka kuma ta tafi hakan ba shi yake nufin naka rayuwar ya kare ba, addu'a kawai take bukata har yanzu ka kasa barin grief stage of your wife's death? Haba mana Hydar ka dauki kaddararka. Hasken da wayarsa tayi ne ya saka ta yin shuru, kallon wayar yayi kafin ya ɗauka yana disconnecting ɗin kiran. Nunfashi Mommy ta sauke tana shafa gefan fuskarshi ta ce, "Bana so kayi wahalar so irin wadda mahaifinka yayi dan Allah ka rage wannan tunanin kaji ko? Murmushi ya danyi yana kallon cikin idanun ta ya ce, " Ke kika so Daddy ya sha wahala ai! Anyway Abba deserves you! You made the right choice" rumgumeshi tayi tana shafa bayansa ta ce, "Wato kunsha labari wajen Ummi ko? Sakinta yayi yana faɗin, "Yes, har Umma! Ban taba tunanin Raihan ba ke kika haifeshi ba sai data warware mana komai but I pretended I know nothing har sai da Abba da Raihan suka fara faɗa Abba ya faɗa min" nunfashi ta sauke tana faɗin, "Rayuwa tana zuwar maka ne a yadda bakai tunani ba Hydar dan haka ka karbeta a duk yadda tazo maka ka kuma godewa Allah sai ya saka ta zame maka Alkhairi, moreover Please try and find suitable partner for yourself, nasan baka rasa masu sanka ba, duk da cewa bazan so hadinka da Noor ba amma idan kaga kana so zanyi welcoming dinta da open hand in sha Allah" "Maganar ƴar wajen Aunty Fatima fa? Ya faɗa yana kallon Mommy. "Kasan dai babba ce she won't take nonsense from you kuma I prefer someone that loves you alot" "Ai baki ji ta bakinta ba" "Ok zan tambayeta in sha Allah, kayi addu'a ka kwanta" kai ya gyaɗa yana kallonta. Miƙewa tayi ta fice, Hydar kuwa sai kusan 2 na dare yayi bacci.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now