Chapter sixteen

55 7 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 16*

Sosai motar su IG take gudu har suka iso inda tracker ɗin yake nuna location ɗin da Raihan ya ke..
       "This is where his location shows! Cikin ƙarfin hali Hydar ya kalli IG Ɗahir ya ce, "Mu je ciki" sauka su ka yi daga motar suna bin tracker ɗin har suka isa building ɗin da su Raihan suke, anan tracker ɗin ya cigaba da nuna musu hanya, suna shiga cikin wajen suka ga Aminatu a kwance ga bomb ɗaure a jikinta hannayenta sanye da kacha da kwaɗo. Da sauri IG Ɗahir da Hydar suka tsugunna, pulse ɗin ta IG ya taɓa ya ji yana harbawa, kallon ɗaya daga cikin convey ɗin da suka taho dasu yayi yana faɗin "Mu cigaba da dubawa, bari na kaita mota! Kai Hydar ya gyaɗa yana miƙewa yabi bayan sauran mutanen... shi ya fara nufar stairs ɗin riƙe da bindiga har ya isa ƙarshen sa be ga mutanen General ba.. kar'ar duka yaji hakan ya saka ya laɓe yana gyara abin maganar dake kunnensa ya ce, "Suna sama, You guyx should get ready to attack" leƙawa yayi yaga sun ɗaure Raihan suna dukansa a ciki ga Mami kwance a kasa. Runtsa idanunsa yayi ganin yadda sukai wa Raihan ko maƙiyinsa sai ya tausaya masa. Fetur Goje ya fara watsa masa a jiki da alama dae ƙona shi suke sonyi da ranshi. Shiga wajen Hydar yayi yana saita Goje da bindiga beyi wata² ba ya sakar masa a  hannu ko tsayawa beyi ba ya kuma sakar masa a ƙafarsa, yaran goje ne suka nufo shi da wuka dan ba bindiga a hannunsu, tun kafin su karaso inda yake ya sakarwa ɗaya harsashi, dayen kuwa tawagar da su IG suka taho da su ne suka harbe shi. Lighter ɗin dake hannun Goje ya kunna yana cillawa Raihan, a 360 Hydar ya bigeta da kafa tayi gefe nan danan wajen ya fara kamawa dan feturin duk ya zuba a wajen, kwan ce Raihan suka fara yi, a kafaɗa Hydar ya dauke shi ya bar wajen sai warin fetur suke yi, Goje da yaransa kuwa ankwa aka saka musu suka ta so ƙeyarsu, ɗaya kuma ya ɗauko Mami. Asibiti suka nufa direct, gaba ɗaya IG was speechless mutane suyi ta aikata muggan ayyuka kamar ba su tunanin mutuwa zasu haɗu da Allah. Su Goje kuwa offis aka kai su. Zama Hydar yayi yana sauke ajiyar zuciya. Mami aka fara fitowa da ita, da sauri Hydar ya miƙe yana kallon likitar ya ce, "Ya ya? "I'm sorry but she's no more! Muje kuyi cike² sai a bayar da gawar ta" kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun Hydar ya fara nanata wa, kafafunshi sun kasa ɗaukar shi, ciwan da kanshi yake ya ƙaru, komawa yayi ya zauna yana runtsa idanun shi. "Muje na cike" cewar IG yana kallon likitar. Wucewa akai da gawar Mami, IG ya bi likitar yayi duk abinda ya dace sannan ya dawo... zama yayi a kusa da Hydar ya ce, "Ka wuce gawar gida ni zan a fito da su Hydar" kai kawai ya iya ɗagawa kafin ya miƙe, a ambulance aka tafi da gawar Mami tare da Hydar zuwa gidan su Ummi. Ummi na jin shigowar ambulance ta fito da sauri tana kallon motar. Buɗe wa akai Hydar ya fito sannan aka fito da gawar Mami. Gaban Ummi ne yayi mummunan faɗuwa, ƙarasawa tayi da sauri tana faɗin "Me wannan? Cikin ƙarfin hali ya ce, "Allah yayi wa Mami rasuwa" "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Cewar Ummi tana buɗe fuskar Mami. Rufewa tayi tana jin hawaye na taruwa a idanunta. Har cikin falo aka shigar da gawar Mami kafin su tafi. "Kai duniya! Hakan nan me sunanta ta tafi ta bar duniyar nan kamar yadda aka kawota a ambulance haka itama gashi! Yarinya me hankali da son jama'a! Hasbinnallahu wa ni'imalwakil, Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Me ya faru ne Hydar? Naga duk ciwuka a jikinta ko hatsari tayi? Zama yayi yana jin zuciyarsa tayi masa nauyi da ƙyar ya iya faɗin " Saceta akai aka kuma kasheta" kasa magana Ummi tayi sai zama da tayi. "Bari naje nayi booking Flight Ummi" daga haka ya miƙe ya fice. Bai dawo gidan ba sai 1na dare, gobe da karfe 7 jirginsu zai tashi. Ummi ce ta kwana da gawar Mami washe gari da safe har da IG Ɗahir suka wuce Kano tare da Ummi da gawar Mami. Mommy na zaune a falo ita da Abba da jiya ya dawo daga kasar waje suka ji shigowar taxi cikin gidan. Farooq ne ya fara fita sannan Abba, ganin yanayin Hydar ya saka Farooq saurin ƙarasawa, Ummi ce ta fito tana gyara hijabinta, gawar Mami Hydar ya fito da ita IG na taimaka masa dan tayi nauyi sosai. Da idanu suka bisu, sai da suka shiga cikin falon sannan Mommy ta mike ta ƙarasa inda Hydar yake gabanta na faduwa ta ce, "Me ya samet... bata karasa ba dan yanayin da Mami take ciki zaka tabbatar da cewa da rasu... zaunar da ita Abba yayi, a kan carpet Hydar ya kwantar da ita yana kallon Ummi y ce a shiryata ta daɗe da rasuwa ana sakkowa daga sallar juma'a za'a mata sallah in sha Allah" daga haka ya fice. Kasa kuka Mommy tayi duk da tana son yin kukan. Duk abin bukata Hydar ya kawo sannan Ummi tayi mata abinda ya dace, Abba ne ya shigo da makara aka dorata sannan suka fita dan yin sallar juma'a. Kusa da gawar ta Mommy ta zauna tana buɗe fuskarta gani take kamar za'a tasheta ace mafarki take yi! Mami dai ƴarta mace ƙwaya ɗaya? Sosai zuciyarta tayi nauyi cikin ƙarfin hali ta ce, "Allah ya jikanƙi Mami, Allah ya saka miki" da Amin Ummi ta amsa... Kafin a kai Mami su Aunty Saudah, Grandma ɗin Raihan da su Abdallah, yan uwa dai duk sunzo gida ya cika banda koke² babu abinda kake ji..a haka suka dawo daga masallaci da kyar aka fito da gawar Mami Saboda riƙeta da suka dinga yi, a masallacin da akai sallar juma'a akai mata sallah dan an sanar su tsaya za'a sallaci gawa. Bayan sun dawo daga kai ta gidanta na gaskiya a ɗaki Hydar ya kulle kan shi, sai alokacin yaji hawaye masu zafi na zubowa a kuncinsa, duk cikin family ɗinsu babu yarinyar da suke dai² tawa kamar Mami she's so decent! Ji yake da zai ga Dad yanzu babu abinda zai hana shi harbeshi! Bayan sallar magariba ya fito, har lokacin da mutane fam dinsu suna zaune a falo. " me sunan innarmu tashi ku ɗauko masa abinci dan Allah" cewar Aunty Saudah tana kallon macen dake zaune a kujera ta yi shuru. "No I'm ok" "Ina fa wani ok Aliyu? Tun rana fa baka ci komai ba! Kayi haƙuri kowa na haka ne, ita kanta Aunty Zarah ai taci abinci kai ma daurewa za kayi" fuskar shi ya shafa yana haɗiye wani abu da ƙyar kafin ya ce, "Zanje na ɗan dawo" "ina zaka je? Cewar Mommy tana kallonsa da idanunta da suka kumbura. " yanzu zan dawo" ya kuma faɗa yana kallonta. Tasowa tayi ta isa gaban shi da mari ta ɗauke shi! Da kallo suka bita duk mutanen da ke falo. " haba Aunty Zarah me haka? Cewar Aunty Saudah tana tasowa. "Ku tashi mu wuce daki! Mom ɗin Raihan ta faɗa tana kallon mutanen falon wanda duk yaran yan uwa ne! Ta shi sukayi suka bita zuwa ɗaki. "Dan Allah ka wuce" Aunty Saudah ta faɗa tana kallon Hydar da ya ƙame yana mamakin marin da mommy tayi masa dan shekaru 35 dai bazai ce ga ranar da mamanshi ta mare shi ba sai yau. "Ka faɗa min ka fara hauka ne? Me yarinyar chan take yi a gidan ka? Tun yaushe kake ajiyeta a gidanka? Wa ka taɓa faɗawa ka siyi gida har ka ɗauki ƴar waccan azzalumin ka saka a ciki? Kana gani dai abinda kayi abinda ya janyo ko? Kasan cewa mugun mutun ne ka ɗauke masa ƴa ka boye ana ta nema ga sakkayar da yayi ya kashe maka ƴar uwa! Ka yi gaggawar zuwa ka fitar da yarinyar nan kafin zuciya ta debe ni nayi mummunan saɓa maka wallahi! Shashasha sakarai kawai! Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta ya ce, "Bazan iya fitar da ita ko ina ba saboda bata san inda take ba she's unconscious" "Ban damu ba! Idan ma mutuwa za tayi ta mut... riƙeta Aunty Saudah tayi ganin kamar zata fadi. "Je ka Hydar" ta faɗa tana kallon shi. Ficewa yayi, a zaune yaga Abba da mutanen sa da yake karɓar gaisuwa, da wani ɗan iskan kallo Abban ya bishi. Abdallah ne ya tashi yabi bayan shi yana faɗin "Ai IG ya faɗi komai ni kuma na faɗawa su Abba gaskiya" "ka kyauta" abinda Hydar ya ce kenan ya fice daga gidan. Napep ya tsara ya kai shi gidan shi. Anan ya kwana washe gari sai 9 sannan ya iso gidan dan sai daya jira likitar dake duba Noor tazo tayi aikinta. A falo suka haɗu da Abba dake ƙoƙarin fitowa. Hanya ya bashi sai daya fita sannan ya biyo shi yana faɗin "Kayi haƙuri! "A'a ka nuna wa mutane basu isa dasu ba ai, mahaifinka yana hanya idan yazo kayi masa bayani" "Abba wallahi duk baku fahimci abunba! Shi IG ɗin be muku bayani ba? Wallahi I'm not at fault aikina kawai nake yi, kuma regarding his daughter be san ma tana wajena ba, i have something to investigate on her dan Allah Abba ka fahimceni kasan bazan taɓa yin abinda zai cutar da wani ba ballantana kuma kanwata, kawai duk baku fahimci abun bane, Abdallah ya rikita komai ya juya komai a bai²" "Ina jinka! Cewar Abba yana kallon shi. " I can't say anything ku jira a sallami Raihan daga asibiti ko kuma idan anyi sadakar uku muje Abuja! "Me hadin Raihan da issue dinnan Hydar? Abba ya faɗa yana kallon shi. "Zaka sani idan munje Abuja" shuru Abba yayi slowly yake recalling abinda IG ya fada musu jiya kafin ya fita. Wucewa Hydar zaiyi Abba ya riƙoshi kamar mai tsoron magana Abba ya ce, "Kana so ka nuna min Raihan ɗin da Inspector General Ɗahir ya ambata min jiya is my Raihan? My own son? Shuru Hydar yayi dan bai san me zai ce ba. "Ka bani amsa! Cewar Abba da karfi. "Dan Allah Abba ka kwantar da hankalin ka! Please" kamar Abba zaiyi kuka haka yake ji, riƙeshi Hydar yayi ganin kamar zai fadi, cikin ɗakinsa ya kai shi ɗan haryanzu guests ɗin basu tafi ba. "Dan Allah Abba ka kwantar da hankalin ka! Abba bai ce komai ba dan gani yake idan yayi magana zuciyarsa bugawa zatayi. Me yayi da Allah ya jarabceshi da yaro irin Raihan? Yanzu ɗan da ya haifa shi ne ɗan daba? Me kashe mutane? "Dan Allah don't think that much Abba komai zai zo da sauƙi in sha Allah" Hydar ya kuma faɗa kamar yasan tunanin da Abba ya ke. "Tun yaushe kasan hakan? Abba y tambaye shi. "An ɗan kwana biyu" ya bashi amsa ba tare da ya kalle shi ba. "Meyasa baka faɗa min ba? Meyasa?! "Kayi haƙuri Abba, na ɗauka zan iya gyara komai kuma bani da wannan karfin gwiwar da zan iya zuwa na tunkareka da wannan maganar" zuciyar Abba na tafasa ya ce, " Shi ya sani! Kashe shi za'ayi tunda hukuma ta kama shi! Ai ba shi kaɗai na haifa ba! Ajiyar zuciya Hydar ya sauke yana kallon Abba ya ce, "Ka dena faɗin haka dan Allah! Abba bai ce komai ba ya miƙe ya fice daga ɗakin... 

    *5 months later*

      Hydar na zaune gefen Noor yayi kyau sosai cikin farin yadin dake jikin shi, ita kuma a kwance ta ƙara haske abunta, a hankali yake karanta mata English novel ɗin dake hannunsa, wayarsa ce ta fara ruri.. ajiye littafin yayi yana ɗaukar kiran tare da ficewa daga ɗakin... "Hello sir! Daga ɗayen side ɗin IG ya ce, " On Monday za'a fara sauraron kar'ar, kana da tabbacin Raihan zaiyi confessing? "Not even Raihan har Goje in sha Allah, ga sauran shaidun mu kamar maman Sadeeq, Saddeeqa, da kuma kakar wannan yaron Idris more over Abbas! "Haka ne, duk wasu bayanan suna wajena a flash drive we pray for success dan ba ƙaramin abu muke yi ba, if we loose, our future is at stalk! "In sha Allah no loosing! Daga haka sukayi sallama. Sai daya koma ya duba Noor sannan ya bar gidan... A falo ya tarar da su Mommy suna kallo, zama yayi yana faɗin " Sai yaushe zaki koma Khairat? "Ai tazo kenan ana yin biki kuma na miƙa ta" cewar mommy tana dariya. " ikon Allah, dagaske dai auren nan za'ayi? Ya kuma faɗa yana kallon su. "Sai kayi ta zama ai ba aure nima aure xanyi ina so ma a haɗa dana Abbdallah in sha Allah! Cewar Farooq yana kallon shi. "Ah toh ku dinga yi masa faɗa,  ni har na gaji da magana, ga ɗan gidan Fatima ma 24yrs bikin saura sati biyu amma shi kam ko budurwa banji ya ce yana da ita ba" miƙewa Hydar yayi yana kallon su ya ce, "Ai aure lokaci ne" "Wallahi kawai a haɗa shi da Aminan Aunty Saudah! Juyowa yayi yana wa Farooq kallon baka da hankali kafin ya ce, "Wacece Amina? Wannan jaririyar dana kusa haifa? Ko ba ita ce last born ɗin Aunty Saudah ba? Wannan ta kai 12yrs ma kuwa? Dariya Khairat ta fashe da ita tana faɗin " Toh wallahi na girmeta da shekara daya, ni sha bakwai ita sha shida kuma tana da saurayinta yaro ba tsoho ba" dariya Mommy tayi tana kallon Hydar ganin yadda ya ƙanƙance idanu dan yana ɗaya daga cikin abinda ya tsana a ce masa tsoho. "Gaskiya ta faɗa ai" cewar Farooq yana dariya. "Ai nima bance ina so ba ina da tawa Aminar! "Noor?! Yaji Farooq ya faɗa. "Wannan fa matar aure ce n faɗa maka! Daga haka ya fice. "Allah ya kyauta, ya baku mata na gari" da Amin suka amsa gaba ɗaya. Supermarket ya nufa abubuwan buƙatar Noor da nashi ya siyo sannan ya ɗau hanyar zuwa gidan shi... yana shiga falon ya yarda ledar hannun shi, a kasa yaga Noor tana kuka. "Noor! Ya kirata yana kallon fuskarta. "Bana iya tafiya! Ta faɗa tana kuma fashewa da kuka, ɗagata yayi ya kwantar a kujera kafin ya ce, " Sannu meke miki ciwo? "Ba komai inaso nayi tafiya" ta kuma faɗa tana hawaye. Number likitar ya fara kira, bayan ta ɗauka yayi mata bayani, ta sanar dashi gata nan zuwa. Noor kuwa kuka take non stop. "Ya isa mana! Ya faɗa yana kallonta. "Dan Allah me ya samu kafafuna? "Babu komai" shuru tayi tana sheshekar kuka. Suna zaune matar tazo, kallon Noor tayi ta ce, " Ma sha Allah, ya jikin naki? A hankali ta amsa da sauƙi. "Haka ake so! Kiyi haƙuri dama ana iya fuskantar irin haka Amma a hankali ga komai ya dawo dai dai, akwai drugs ɗin da zan rubuta idan kina sha zaki watssake" bata ce komai ba. Maganin ta rubuta ta bawa Hydar, godiya yayi mata. Miƙewa tayi tana ɗorawa da faɗin "zaka dinga taimaka mata tana takawa ko daga gate ne zuwa cikin falo kullum a kalla sau ɗaya a rana" kai ya gyaɗa alamar toh. Fita tayi, dubansa ya mayar kan Noor yana faɗin "Bari na dafa miki abinci kici" "me ya faru jiya? Murmushi ya ɗanyi kaɗan tunowa da abinda ya faru a watanni data ke kira jiya. "Ba jiya bane, an kai 6-7months You even lost your child! Buɗe idanunta tayi da sauri tana faɗin "What child?! " Unborn child ɗinki kinyi ɓari lokacin da baki da lafiya, kin shiga coma ne for good 6months, Kuma kina nan, your parents though kin gudu ne saboda abinda ya faru har yanzu suna jiran dawowar ki, duk da kasancewar mahaifiyarki bata daina posting akan ɓatan ki ba" hawaye ne suka biyo kuncinta, na farko taji dad'i da aka ce cikin jikinta ya zube, na biyu kuma tana kuka ne saboda tuna Tahir... "Har yanzu babu wani labari akan shi? "Babu! Ya bata amsa yana kallonta. Da ƙyar ta haɗiye yawun bakinta kafin ta mayar da idanunta ta lumshe. "Ina son sani me ya kai ki wajen nan a daren ranar? Shuru tayi bata ce komai ba. "Ina jinki! Ya kuma faɗa yana zuba mata idanu....

Autarmama ce.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now