Chapter thirteen

42 5 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 13*

      Daddy ne zaune a kan cushion yana karkaɗa kafafu cikin jimanta lamarin ya fara faɗin,   "Wani ya shigo min gida har cikin dakina! "Waye zai shigo ranka ya daɗe? Kasan dai idan ba Noor ba babu me shiga dakinka a wannan lokacin" kai ya girgiza yana karkaɗa kafafun shi ya ce, " Ba Noor bace domin an ɗauke min akwatin da nake saka kuɗi! Ina yarinyar nan Amina? Me aikin Noor? "Bata da lafiya ai tun jiya sa safe, tun azahar ta bar sashin nan ɗazu ma likita yazo ya saka mata ruwa" Daddy bai cewa Mom komai ba ya tashi ya fice. Har karfe 1n rana Mom bata ga Noor ta fito ba, ɗakinta ta nufa amma tana buɗewa taga wayam. Toilet tayi knocking nan ma data ji shuru ta buɗe taga bata ciki. Fitowa tayi daga ɗakin ta fara dube². Layinta ta kira amma ba'a ɗauka ba, ɗakin Noor ta dawo taga wayar a kan bedside drawer. Sakkowa tayi ta shiga kiran me aikinta. Tambayarta tayi ko taga Noor amma ta ce a'a. Duk neman da zatayi mata tayi daga karshe ta ayyana cewa fita Noor ɗin tayi. Wasa² har karfe 10na dare babu Noor babu labarinta nan hankalinta ya tashi. Aminatu da shigowar ta ɓangaren kenan Mom ta tareta tana faɗin "Tun safe Noor ta fita shuru haryanzu bata dawo ba" "Kuma bata faɗa miki inda zata je ba? Cewar Aminatu tana kallon Mom. "Ni bata ce min komai ba! Bari na sanar da mahaifinta" daga haka Mom ta bar wajen. Taɓe baki Aminatu tayi sannan ta wuce sama. Da sauri ta shiga ɗakin Noor ta fara bincike, a cikin wata mini bag taga ATMs har huɗu duka ta kwaso tare da ɗaukar wayar Noor ɗin ta fito. Bayan ta koma bangarenta ta dauki duk abinda zata ɗauka ta zumbula hijabi ta fito. Har tafice babu wanda ya ce mata kala dan duk sun santa ko dan surutun ta. Tafiya tayi me nisa kafin taga motar Hydar. Bayan ta shiga ta ajiye masa ATMs din tare da wayar Noor ba tare da tace komai ba. Shima bai kulata ba yaja motar suka bar layin. Sai da suka ɗau hanya sannan ya ce, "Ina zan kaiki? Kinsan dai bazaki koma gidan nan ba! Kin gama aikinki" "ka saukeni a ko ina" cewar Aminatu tana kallon window. " Amma ai na baki hakuri ko? Kinsan bana son yawan magana meyasa kike saka ni? "Nan ya isa saukeni " ta faɗa tana kallon shi. " gefen titi ya gangara tare da yin parking ya kulle motar yana dubanta ya ce, "Zan kai Noor gidan mu, hope idan kin koma Kano zaki dinga zuwa? "Aikina ya kare daku idan aka sallameni wajen aiki that's all! Aikine ya haɗa mu kuma ya raba" ajiyar zuciya ya sauke yana buɗe motar. Fita tayi tana buga murfin motar a 360 ya bar wajen. Har yayi nisa ya dawo still tana tsaye a wajen ga jaka goye a bayanta. Murfin motar ya buɗe mata yana faɗin "Shigo" rufe masa murfin motar tayi tana yin gaba. Sakkowa yayi tare da bin bayanta. "Dan Allah kiyi hakuri is not safe na saukeki anan ke kaɗai! "Wallahi babu inda zan koma! Kaje kawai zan karasa chan restaurant din naci abinci don't worry! Daga haka ta wuce shi. Ajiyar zuciya ya sauke ya koma mota, a baya ya dinga bin ta har sai data shiga restaurant ɗin sannan ya ɗau hanyar gida. Bayan ya isa gida wayar Noor ya jona a charji, sai data kusa cika sannan ya cire, Apps din banki ya gani kan wayarta har biyar. UBA ya fara shiga.. password ya gani, sunanta ya gwada amma error ƙaramin tsaki yayi yana saka sunan Daddy aikuwa ya buɗe ajiyar zuciya ya sauke balance dinta ya duba 500k ne kawai a ciki. Fita yayi daga app ɗin ya shiga wallet na kuda bank. Nan ma da password numbers har shida ake bukata. First 6 of her phone number ya saka aikuwa yana sawa ya bude. Wani murmushi yayi dan yau ɗin yaga da sa'a yazo. Balance din dake ciki over 7m+ zaro ido yayi kadan kafin ya fara ƙoƙarin yin transfer ɗin kudin ta account ɗinsa... password na transfer yake ta gwadawa ya gwada yafi sau shida. Tsaki yayi yana kallon wayar, tunowa da abinda Abbas ya ce dazu.. aikuwa da sauri ya saka date of birth ɗinta sai gashi transfer ya tafi... haske yaga wayarsa tayi na 5m. Ajiyar zuciya ya sauke yana cire sims ɗinta daga wayar tare da kashe wayan nata. A daren yayi ordering duk abinda likita ya faɗa masa yana da bukatar siya 4.8m ya kashe komai da komai. Ajiyar zuciya ya sauke yana tsoron dialing number Mommy, for him is better ya nemi gida ya saka ta! Yasan ko Mom dinsa ta yarda Abba bazai bari ba more especially idan yasan gaskiyar lamari. Ajiye wayar shi yayi yana rufe idanun shi. Wa she gari bayan ya dawo daga asibiti wajen aiki ya nufa. Offis ɗin  Inspector General Ɗahir ya nufa, sai da aka bashi izinin shigowa sannan ya shigo. Zama yayi a kujerar bayan ya sara masa. " Muna da ƙwararan hujjoji akan Alkasim, yanzu abinda nake so da kai da team dinka akwai wai babban yaron shi Xexe suke ce masa a kamo shi! Sai mun tabbatar yayi confessing komai a gaban kotu! Ga hotan shi! IG Ɗahir ya ƙarashe maganar yana tura hotan Raihan gaban Hydar. Da idanu Hydar yabi hotan yayan shi kafin ya hadiye wani abu ya ce, "Ok sir" "Dole mu kawo karshen abinda yake yi a ƙasar nan! Yana kashe mutane amma kuma yana nuna cewa yafi kowa sansu! Ya lulluɓe mutane a baibai! Wannan yaron nashi inaso a kawo shi gabana! Yana zaune a cikin ƙauyukan dake cikin garin nan! Yawwa ina CL Amina? "Nasan tana gida yanzu haka! Jiya muka rabu da ita" "Ok, ya kamata a ce General lieutenant Salis ya kira ni she really tried, Amma zan kira inji yadda ta isa! Good job Aliyu! Murmushi kawai Hydar yayi sannan ya tashi, sallama suka yi ya fita yana duƙun ƙune hotan Raihan ya saka a aljihu. Bayan ya koma gida number Abdullah ya shiga kira, bugu uku ya ɗauka tun kafin Hydar yayi magana Abdallah ya ce, "Ina ta kiranka bata shiga, kasan Uncle Mustapha ya bani Khairat? I'm telling you! I love that girl! Ƙaramin tsaki Hydar yayi yana cewa, "Ita Khairat ɗin Baba ya baka? Khairat dai 16yrs old? "Toh menene? Ko so kake na zama tuzuru kamar ka? Next week ma zan wuce US ɗin ai, sunyi magana da Dad ɗina, in sha Allah kafin next year za'ayi auren" "Ok, kafin ka tafi dai ina so ka samar min gida me kyau zan siya" "Gida kuma? Me za kayi da gida? Ko auren ne? "Kawai kayi abinda na ce and this is between me and you bana so kowa ya sani idan nace kowa ina nufin kowa da kowa just me and you idan naji labarin nan ko a wajen Mommy ne ubanka zaka ci! " Auren sirri kake son yi? Dariya ce ta kuɓucewa Hydar. Calmly ya ce, "Na faɗa maka ka kirani idan an samu Please as soon as possible! "Ok, a ina kake son gidan? Cewar Abbdallah daga ɗayen side ɗin. " faraway from our house! Your house, gidansu baffa, Aunty Khadijah! Da kuma Mom din Raihan" "What is wrong with you? Why are you distancing your self from your family? Cewar Abbdallah daga ɗayen side ɗin. "Kaga, za muyi magana idan nazo" "ok kamar na nawa kake so? Sai da Hydar ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Ka dai samo min flat me kyau sosai gini me kyau dan ba wani gidan zan sake siya ba idan zanyi aure so Please Ina son gida me kyau sosai sai kuyi magana da me gidan ni kuma  ka fada min price ɗin make sure kayi ciniki! "Ok in sha Allah" "Good, sai anjima" daga haka ya kashe wayar. Ummi ce ta shigo tana kallonsa ta ce, "Ga abinci! Ashe mahaifinka aurar da Khairat zai yi? "Haka Abbdallah yake ce min! "Ni dai sam banji dadi ba tayi ƙankanta ko 17yrs bata kai ba"  "ya za'ayi shi Abdallan ne ya takura na sani kuma kin san baba bazai ƙi ba" Nunfashi Ummi ta sauke tana ajiye tray ɗin hannunta ta ce, " Duk da haka da sai a bari sai ta shiga jami'a kamar 200l, zan masa magana gaskiya, kwana biyu Raihan bezo ba! Lafiya dai ko? "Kin san halinsa bansan inda yake ba! Kai ta girgiza kafin ta ce, "Toh Allah y kyauta" da Amin ya amsa yana zama. Fita tayi ta barshi. Kaɗan yaci abinci sannan ya nufi toilet... Bayan sallar isha'i yana zaune yana duba littafin da ya gani a box din General. Wayarsa ce fara ruri, ganin IG ƊAHIR ya sashi ɗauka tare da karawa a kunne. " Sorry na dameka, na ce kunyi waya da Amina? "No sir! Hydar ya ba shi amsa. "Ok! Na kira shugaban su ya ce bata zo and they have being calling her line no respond! "Ok sir let me try calling her" daga haka ya katse wayar. Da sauri ya fara neman layinta. Har ta gama ringing bata ɗauka ba, ya mata kira ya kai goma amma bata amsa ba. Sosai hankalin shi ya tashi dan gani yake ko da ace tayi avoiding kiran shi ai baza tayi avoiding kiran shugaban ta ba. Layin Abbas ya shiga kira. Sai data kusa tsinkewa ya ɗauka. "Abbas Aminatu is Missing are you sure everything is ok there? "Hydar! Kallon wayar Hydar yayi da sauri dan tabbatar da wanda ya kira da kuma muryar da yaji! "Are you there?! "RAIHAN! Ya faɗa da ƙarfi. "Hydar na ɗaga wayar nan ne dan na fada maka cewa kar kazo! Please and please Hydar! Ran Hydar ya fara ɓaci ya ce, " Ina Abbas? "Close to his dead Hydar! So please kar kace zaka zo! Spare your life" "Amina fa? Iska Raihan ya furzar yana faɗin "She's here too! But I will make sure she's save coz I love her! Runtsa idanunshi yayi yana jin zuciyarshi na tafasa. "General yana son haɗuwa da kai idan kana son ayi sparing life ɗin Amina da Abbas! Daga haka ya katse wayar. Rasa abunyi Hydar yayi for a moment. Yana shirin kiran IG Ɗahir yaga wayarsa tayi haske. Sako ne ya shigo ta number Abbas. "No matter what Hydar don't show up here! General zai saka na kiraka na faɗa maka address so please Hydar don't come" kallon wayar ya cigaba da yi bayan ya kammala karanta sakon. Kafin 5mins sai ga kira, da sauri ya ɗaga tare da danna recording. Address din inda zai samu motar da zata kawo shi inda suke tare da time din Raihan ya faɗa masa. Katse kiran yayi yana kallon agogon ɗakin, gobe by this time suke son ganinsa! Recording din ya turawa IG Ɗahir sai da yayi masa voice note kusan 2mins, ya daɗe yana kallon message ɗin kafin ya kunna data, he's just thinking of Raihan! Indai IG da convey dinsa suka je wajen yasan akwai possiblity a iya kama Raihan! Amma he can't be that selfish. Data ya kunna saƙon ya tafi. Layin Raihan ya shiga kira! Bugu uku ya ɗauka yana faɗin "Yanzu zan zo gida" daga haka ya katse. Har karfe 1 na dare Hydar na jiran Raihan. Sai 2:30am ya shigo gida. A zaune ya tarar da Hydar kana ganinsa kasan yana cikin damuwa. "Raihan! Ya kira shi yana jin zuciyarshi na ɗaci. " Aminatu is not safe! She's isn't under my control anymore Abbas yaba ni inji da shi! Hydar Please save her! Wani kallo Hydar yayi masa ya kasa cewa komai! "I can do nothing about her, tana hannun su Goje! Definitely zasu iya raping ɗinta even though I warn them! Zama Hydar yayi yana nanata kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun. "Ya kake ji a zuciyarka yanzu? Kasan mutane nawa kuka saka a irin wannan halin? Juwairah, Saddeeqa, Sadeeq da ma wanda ban sani ba!  "That isn't my job ka gane mana nifa kawai ina nemo masa information akan mutum kuma ya saka su Goje aiki yasa ka na tabbatar masa da aikin nasu" "Kuma kana kai mutane! "But is rare! Cewar Raihan. "Wallahi Raihan ka cucemu! "Kyan ka be amfane ka da komai ba! Ilimin ka be amfane ka da komai ba! Wallahi I regret having you as my brother! The person I can give my life for! My only friend! Raihan ka cucemu! Cewar Hydar yana kallonsa idanunsa sunyu ja. "I'm sorry that's my destiny, ni dai yanzu just save her please bana so yasan relationship ɗina da kai! Moreover be taɓa sanin ina da wani gata ba ya ɗauka banda ma iyaye" da kallo Hydar ya bi shi. Numfashi ya sauke yana kallon Hydar ya ce, " I'm sorry! "In dai kasan you're sorry dagaske gobe ka miƙa kanka ga police kuma kayi alkhawarin confessing a kotu! Kai Raihan ya girgiza yana faɗin " I can't do that! Indai nayi hakan i will ruined my life more and more, saboda ko da an kai General prison mutanensa na nan and they won't leave me! Kuma bana so nayi abinda za'a gane family ɗina! "Kasan kai ma jail zaka tafi ai just do it! Raihan bai ce komai ba ya fice. Daren ranar Hydar beyi wani baccin kirki ba, sun gama tsara yadda zasu yi da su IG ƊAHIR dan har da shi za'a je. Wa she gari karfe 7 ya bar gidan. Wajen Noor ya nufa, har yanzu tana ICU kullum jiya iyau, kawai dai ansan tana raye ne. Bai ɗau lokaci ba ya baro asibitin. Offis ya nufa anan ya ɓata lokaci sosai  dan bayan la'asar ya dawo gida. Har time ɗin Raihan na gidan. Sai da yaci abincin da Ummi ta kawo masa sannan yayi wanka, bayan ya fito yana ɓalle maballayen rigar shi Raihan ya shigo. "I'm leaving" "kana nufin bazaka miƙa kanka ba? "I won't! Amma idan an kamani that's fine! Daga haka ya bar ɗakin. Ƙarfe 8 na dare Hydar ya isa inda suka ce, aikuwa yana isa yaga motar su, bude masa akayi ya shiga suka bar wajen a guje. Tafiya ce me tsayo sukayi duk cikin motar babu me cewa uffan har suka isa. Sakkowa yayi yana bin wajen da kallo. "Muje! Yaji daya daga cikin mutanen da suka ɗauko shi ya faɗa. Bin bayan su yayi suka shiga wajen da yafi kama da kango amma babba ne sosai. A durƙushe ya ga Aminatu kana ganinta kasan taci duka ga gashin kanta duk a jike ya zubo mata a fuksa haka ma kayan jikinta are so tight dan riga da wando ne kuma sun jiƙe. "ACP HYDAR! Yaji muryar General. Ɗagowa yayi ya kalli direction ɗin da yake. "Ku caje shi sai ku barshi ya shigo" daga haka ya koma in da suka fito. Cajeshi suka fara yi kamar ɓarawo, kasancewar bai zo da komai ba basu samu komai ba. Shiga yayi yana bin ɗakin da kallo! " Nasan kasan ƴata ta ɓata! Kai ya girgiza alamar a'a. Murmushi kaɗan general yayi yana dorawa da faɗin " 4-5days kenan! I need your help! Duk ranar daka nemo min ƴata xanyi freeing Amina! Naji Raihan ya ce she's your girlfriend right? Shuru yayi yana kallon shi. "Kar ka damu! Nasan ba zaka bani matsala ba, yanzu ga wannan! Bana son wani matsala kaji ko? Ya ƙarashe maganar yana ajiye masa suitcase. "Buɗe mana" janyo suitcase ɗin Hydar yayi yana buɗewa... dollars ne na America sun cika suitcase ɗin. Rufewa Hydar yayi yana faɗin " Ok! "Very good na sani ai bazaka bani matsala ba! Maybe zaka iya yi wa yarinyar nan magana! Kai Goje shigo da ita! Ya faɗa da karfi. Ba'a ɗau lokaci ba suka shigo da Amina wadda da ƙyar take iya buɗe idanunta. A wajen ta durƙushe tana fashewa da kuka. "Don't act smart ACP HYDAR! If not kasan abinda ake cewa water thank that fills up slowly? Toh a ciki zan saka Amina! Zan baka 1-2hrs ka nemota idan ka kasa zaka tarar ruwa ya cinyeta a cikin tankin! So be sincere za kayi aiki da mu? " me kuke so? Ya faɗa yana kallon Amina. " haɗin kanka! Ka haɗa hannu da mu! Nasan kana da evidences sosai a kaina, I want them to be vanished! Baka da matsala dani in dai zaka bi ni, talk to her for a little bit itama ta bada haɗin kai! Daga haka ya miƙe ya fice. Bluetooth ɗin dake maƙale ƙasan harshen shi ya fito da shi yana sakawa a kunne idanunshi akan Aminatu ya ce, "I'm sorry" "please Hydar take me out of this place! Hydar please! Top dinshi ya cire yana miƙewa, inda take ya nufo ya dora mata top ɗin sa ya ce, " Get up! "I can't Hydar! Tsugunna yayi yana dafe Bluetooth dinsa ya ce, "Ok sir" daga haka ya cire shi. "Ta shi muje" kuka take sosai tana kallon Hydar. Shigowa Goje yayi yana kallon su ya ce, "Oga zai wuce ni kuma zan ɗauketa mu tafi! Ka daiji abinda aka ce ko? Sauke idanun shi yayi daga kan Goje yana kai dubansa ga Aminatu. Hannu Goje ya kai zai rikota, da karfi Hydar ya ture hannun yana masa wani kallo. Wata dariya Goje ya sheƙe da ita yana kallon Hydar ya ce, "Ni zaka faɗawa kishi? Toh bari kaji wallahi tallahi jiya da ita na kwana! haka ma yarana! Ya ƙarashe maganar yana fashewa da dariya. "Kai! Wasa ma kake! Tambayeta kaji! Kuma yau ma da ita zan kwana bilahil... be karasa ba sakamakon naushin da Hydar ya sauke masa a kumatu, hokorinsa ɗaya sai daya fita......

Autarmama ce

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now