Chapter five

83 3 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 5*

       Tun da Noor ta farka kanta ke matsanancin ciwo, Mom dake gefanta tayi sauri faɗin "Ya kike ji yanzu? Ta shi zaune tayi tana kallon ɗakin ta da take ciki, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin "I'm ok, just a little bit headache but I will be ok in sha Allah, ina Saddeeqa? "Me kike so? Mom ta faɗa tana kallon ta. "Shayi zata kawo min" da toh Mom ta amsa sannan ta fita. Ita dawo da shayin a table ta ajiye tana kallon Noor ta ce, "Ki sha, ga maganin ciwan kai nan sai ki sha kiyi wanka kya fi jin daɗi" "thanks Mom"  murmushi kawai Mom tayi sannan ta fita. Bayan tayi wanka ta shirya number Hydar ta shiga kira for the first time tun bayan break up ɗinsu. Sai data kusa tsinkewa ya ɗauka ba tare da yace komai ba kamar yadda tayi tsanmani. "Please let's have dinner together tunda kana Abuja kazo gidan mu yau if possible" "Me kike so? Ya faɗa a hankali. Sai data sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa da "Please dae kazo is urgent and moreover vital" bata jira cewar shi ba ta kashe wayar. Bayan sallar magariba Daddy ya dawo, yaji sauki duk da cewa ciwan be warke ba. Noor na zaune a ɗakin shi tana haɗa masa shayi wayarta ta fara ruri, ganin hydar ya saka ta ajiye spoon ɗin hannunta ta ce, "Ina zuwa Daddy" murmushi Daddy yayi dan yaga sunan dake screen ɗin nata hoping a ce siriki ya samu. Fita tayi tana ɗaukar kiran. "Ina jiranki" daga haka ya katse wayar. Ɗakinta ta nufa da sauri ta ɗauko kimono ta ɗora kan riga da wando dake jikinta. Fitowa tayi tana kiran Saddeeqa. "Gani" Saddeeqa ta amsa tana isowa in da take. "Ki shirya komai a falon ƙasa" da toh ta amsa sannan Noor sakko. Bata ga motar shi a compound ba hakan ya saka ta ɗauki hanyar fita daga gidan. Ƙofa aka buɗe mata ta fita, a cikin mota ta hangoshi. Ƙarasawa tayi tana knocking ɗin glass din duk da cewa ya ganta. Sauke glass ɗin yayi yana kallonta ya ce, "What's it? "Muje ciki why are you acting strange? "Shigo mota I'm all ears! Daga haka yayi wining up. Bata da choice hakan nan ta zagaya ta shiga motar shi idanunta a kan shi ta ce, "Meyasa kake investigating akan case ɗin Juwairah? Kuma menene alaƙarka da Sadeeq? I mean marigayi Sadeeq? "He's my friend kuma ni na faɗa miki a kan case din Juwairah nake investigating? What's my business with her? Idan dan wannan kika kirani na baki amsa so zan tafi " ya karashe maganar yana kallonta. "Ban yarda da kai ba Hydar! Cewar Noor.  "Oops na manta congratulations! Cike da rashin fahimta ta ce, "Na me? "Nasan Dad ɗinki ne zaiyi nasara so shine na miki" Bata ce dashi komai ba tayi relaxing a kujera tana kallon screen din wayarta. "I'm going" ya faɗa yana tada mota. "Na ɗauka ce maka nayi za muyi dinner ko? Murmushi ya ɗanyi kaɗan kafin ya bata amsa da faɗin "Na saka Ummi tayi min girki kuma idan naci abinci anan bazan iya cin na Grandma ɗina ba" "okay wait for me zan maka packaging ka kai wa siblings dinka, idan ma abokinka na nan ka bashi ka ce in ji ni, bazaka saka na shiga kitchen a banza ba" ta ƙarashe maganar tana buɗe murfin motar. "He's my brother! Ya faɗa kamar ba shi yayi maganar ba. Juyowa tayi tana kallon sa ta ce, "Thesame mother and father? Kai ya daga mata alamar eh. "Amma baka taɓa faɗa min kana da yaya Raihan ba, Abbdallah, Farooq, walid kawai na sa ni" "Nima ai ban taɓa sanin kina da ƙawa Juwairah ba" "That's different Hydar, Amma shikenan ka jirani" da ok ya amsa sannan ta fita daga motar. Ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta dawo da basket me kyau ta zuba abinda tayi packaging, mota ta buɗe ta ajiye a ƙasan seat tana kallon shi ta ce, "ka kaiwa Raihan and send my regards" Kai ya gyaɗa alamar toh. Rufe masa mota tayi ta koma cikin gida. Ajiyar zuciya ta sauke yana girgiza kanshi rayuwar Amina tana bashi tausayi. Bayan ya isa gida basket ɗin ya ɗauko jin da nauyi ya saka shi buɗewa, plastic rubber hudu ne ko wanne cike da abinci ga drinks har da ruwa da fura masu sanyi. Kai ya girgiza ya rufe basket ɗin sannan ya shiga falo. Ummi, Daddy da kuma Raihan na falo suna kallon sakamakon zaɓe. Sallama yayi Ummi ce ta amsa tana faɗin "Kai dai baka gajiya da zirga² ya ciwan kan? Sai daya zauna sannan ya amsa da "Ya daina" "Itama Zarah sai dana faɗa mata a mai dakai gun likita shima uban naka taurin kai gareshi" murmushi yayi yana faɗin "Is not serious fa Ummi" "Ahtoh kasan bata so taji ko ɗan yatsa na maka ciwo" cewar Daddy yana gyara gilashin idanunshi. "Wannan fa? Ummi ta kuma faɗa tana kallon basket ɗin da ya shigo dashi. Ruwa Raihan ya ɗauka yana sha ba tare da ya kalli Hydar ba dan fushi yake da shi. "Budurwar Raihan ce ta aiko masa dashi" ruwan daya zuba a bakinsa ya furzar da ƙarfi idanunshi a kan hydar. "Me haka? Cewar daddy yana kallon shi. " Anyi zancen budurwa asirinsa ya tonu mana" cewar Ummi tana kallon sa. "Shiyasa yaki yarda a haɗa shi da ƴar gidan Fatima maimakon ya ce yana da wadda yake so toh waye zai hanaka? Ummi ta ƙarashe maganar tana kallon shi. "Ban da wata budurwa fa! Cewar Raihan idanunshi a kan Hydar. "Ahtoh nidae gashi nan ta bani na baka" daga haka ya bar musu falon. Bude basket din Raihan yayi yaga abinci ne har da fura me sanyi kuwa. "Ta kyauta kuwa, ka ɗebi wanda zaka ci ragowar a saka a fridge nasan Bazaka cinye ba" furar ya ɗauka yana faɗin "Na ƙoshi fa zan dai sha furar" daga haka ya mike yabi bayan Hydar. Sai daya jira ya fito daga toilet, yana tsane ruwan kanshi Raihan ya wafce towel ɗin ya ce, "Me kake nufi da abinda kayi yanzun? Murmushi kawai Hydar yayi ya nufi closet. "Magana fa nake maka ka mayar dani ɗan iska" "Idan ka gama fushin sai muyi magana" "Hydar kana bata min rai wallahi, meyasa zaka ce daga wajen GF ɗina abincin nan yazo? Abinda ma bansan dashi ba? "Yanzu ai ka sani" "ok Saboda na faɗa maka gaskiya kake ta wannan behaviours ɗin? Shikenan kai ka sani ka cigaba da saka kanka cikin harkar siyasa! "Inyi involving ko kar nayi involving ya zama dole saboda abinda aka sani kenan i have no other choice! "Then resign! Cewar Raihan kamar zai daki Hydar. "Saboda me? That's my profession and I like it! Please Raihan stop complicating things okay? "Baka san waye General ba HYDAR! I'm warning you! Daga haka ya fice daga dakin. Da kallon rashin fahimta hydar ya bishi. Ajiyar zuciya ya sauke ya shirya.

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now