Chapter seven

58 5 0
                                    

✨ *AMINATU* ✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*FREE BOOK*

*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*

*Page 7*

          "Mom regarding my new maid! Baki ganta bane? "Na ganta mana, what's wrong with her? Kai Noor ta girgiza kafin ta ce, "She seems illiterate! Bagidajiya ce sosai fa! How can she cook! Clean my room! Arrange my clothes and other needs of mine? "Wadda ta kawota tayi assuring ɗina, kuma ai duk abincin da kike ci ita ke girkawa kina fita take gyara miki ɗaki, I'm impressed... just give her a chance" cewar Mom tana murmushi "shikenan, dama inaso muyi magana"  Noor ta faɗa idanunta a kan Mom.. "A kan Tahir" "me ya faru? Mom ta faɗa tana kafeta da idanu. Sunkuyar da kai tayi tana kallon zoben gwal ɗin dake hannunta ta ce, " Menene relationship ɗin mu? Sai da Mom taja numfashi sannan ta ce, "Yayanki ne what else? "Amma meyasa babu wanda ya taɓa faɗa min? "Menene amfanin faɗa miki me zai ƙare ki da shi! Mahaifinsa did horrible things to your dad naga ma ƙoƙarin His Excellency da ya riƙe masa ɗansa" "Amma ai ba Tahir ne yayi masa laifi ba, hope dae bakya jin haushin sa? Sai da Mom tayi murmushi kafin ta ce, " Meyasa zanji haushin shi? Da ina jin haushin shi bazan yarda ku dinga mu'amala ba har nayi trusting ɗin shi na dinga bari kina duk wani harkokin ki dashi" "Hakane, shikenan" Noor said calmly "Good, maganar tafiyarki wajen FARIDA fa? Kai ta girgiza da sauri kafin ta ce, "Sai nan gaba in sha Allah" "tohm shikenan Allah yayi miki albarka" da Amin ta amsa sannan ta bar ɗakin. A zaune ta kuma tarar da Aminatu a falon dakinta tana kallo. Tana ganinta ta miƙe ta ce, "Yanzu fa nake shirin tafiya sai kuma na manta na cigaba da kallo, ni kuwa hajiya na ce kullum a rana kike yini ne? Naga fatarki sai haske take wallahi tallahi shar dake" "Eh kema ki dinga zama a cikin ranar kullum" daga haka Noor ta wuce ta barta. Da kallo Aminatu ta bita har ta shige ɗaki.  Missed calls ɗin Tahir ta gani har uku. Zama tayi tare da cire wayar a charji tayi dailing number shi, kamar jira yake tana shiga ya ɗauka. "Ina kika saka wayar? "Naje wajen Mom, so what's up? Sai daya numfasa sannan ya ce, " A date are you in? Murmushi ta ɗanyi kafin ta ce, "So soon? I just accepted fa? Daga ɗayen ɓangaren ya ce, " Ai ba abun sauri bane we have known each other for the past 20yrs so me muke jira Noor? If possible ki sanar da Yallabai akan relationship ɗin mu there is nothing to Wait about" "seriously? Ta faɗa tana Dan murmushi me sauti. "Yeah ko kinfi ƙarfina? "Eh kasan ai taimakon ka zanyi ko? Dariya yayi me sauti kafin ya ce, " i will be superior soon, yanzu dai zaki je? "Eh" ta amsa masa. "Ok thanks ki shirya after isha'i" da toh ta amsa sannan sukai sallama. Ta daɗe rabon data tsinci kanta cikin farin ciki irin haka. Dama tana sonshi ne? Why all this happiness all of the sudden, toh daga faruwar abu just few moments ago? Kwanciya tayi tana lumshe idanunta.  Da sauri kuma ta tashi zaune a fili ta ce, "Me uncle yayi wa Daddy! Mom tace something horrible? Kafaɗa ta daga alamar ina ruwanta. Har zata koma ta kwanta ta kuma faɗin "Toh idan hakan ya shafi relationship ɗina da Tahir fa? Iska ta furzar kafin ta ce, " Nasan Dad zai so abinda nake so! That won't be a problem" murmushi tayi ta koma ta kwanta.

      Da daddadare tana cikin shiryawa Mom ta shigo ɗakin nata. "Ina kuma zuwa" "Zan fita cin abinci ne" "Ok Tahir yaje da ke" "Ok Mom" ta faɗa tana murmushi. "Gobe za muyi baƙi abokan mahaifinki, so kar kije ko ina kuma behave well ki shirya cikin kayan hausawa kinji ko? "Tohm" ta amsa tana spraying perfumes iri² a jikinta. "Kamar wadda zata je zance? Cewar Mom tana kallonta. Noor dai murmushi kawai tayi. Handbag ɗinta ta ɗauka tana kallon Mom ta ce , "Sai mun dawo" "Kinyi reserving restaurant dai ko? Kai ta ɗaga alamar eh. "Ok Allah ya tsare ki kula kinji? Da toh ta amsa sannan ta fita. A stairs suka haɗu da Aminatu dake waya. Bata bi ta kanta ba ta wuce, da sauri Aminatu ta kashe wayar tana bin bayanta ta ce " Allah ya tsare Hajajju" da Amin ta amsa sannan ta fita. Ajiyar zuciya Aminatu ta sauke bayan fitarta. Tana fitowa compound ɗin taga motar Tahir. Buɗewa tayi ta shiga front seat tana faɗin " Sorry I'm late" "kallonta ya tsaya yi" ɓata rai tayi ba tare da ta kalleshi ba ta ce, " Sai dare ya ƙara yi? "Kinyi kyau" sai a lokacin ta kalleshi shima ya sha kyau cikin kaftan, mostly da suit take yawan ganin shi ko kuma kayan sojoji shiyasa yanzun yayi mata wani bala'in kyau. "Kaima haka" "na gode ranki ya daɗe" murmushi kawai tayi, gate aka Buɗe musu bayan sun isa sannan suka fice. Hannayen sa ya saka cikin nata, dayen hannun kuma yana driving, ɗagowa tayi ta kalleshi sai kuma ta mai da idanunta kan hannun su. " Ban taɓa tunanin za kiyi accepting so soon ba, ko dai dama kin daɗe kina sona? "Sa'a kawai kaci" bai ce komai ba sai murmushi da yayi. Har suka isa restaurant ɗin bata kara ce wa komai ba. Kasancewar yayi reserving babu kowa a restaurant ɗin, shiga sukai suka zauna sannan   aka kawo musu menu. "Me zaki ci? Ya faɗa bayan ya gama duba menu ɗin" " i prefer onion mix cabbage soup" "shikenan? Ya faɗa yana zaro ido. "Yeah" "me kika ci kafin ki fito? "Nothing fa, kasan dare ne" "hakane" ya faɗa yana kiran waitress ɗin. Abinda zata kawo musu ya fada mata sannan ta bar wajen. "Kina son strawberry smoothie ai ko? Kai ta daga alamar eh. Ba'a daɗe ba akai serving ɗinsu. A hankali ta saka chokali ta fara ɗibar soup ɗin ta kai baki. Tahir dai kallonta kawai yake yi. "Zai huce idan baka sha ba" numfashi yaja yana saukewa a hankali ya ce " Yes ma'am" bata kula shi ba ta cigaba da shan soup ɗin ta, tas ta shanye sannan  ta ɗauki smoothie ɗinta ta fara sha. Bai wani sha dayawa ba dan ba so yake ba saboda ita ya sha soup ɗin. Smoothie ɗin ya ɗauka ya fara sha yana kallonta. "Sai na kware sannan zaka daina kallona ko? "I can't forbid my self ne, kinsan ko wani ɗan adam da baiwar da Allah yayi masa ko? Toh ke ya miki baiwar kyau" juya idanunta tayi tana kallonsa ba tare da tace komai ba. Hannunta ya riko yana faɗin "Promise me to stay by side no matter the circumstances" "in sha Allah" ta amsa masa. Gold ring me ɗauke da diamond a saman shi matsayin ado ya saka mata a yatsanta ya ce, "Idan kika cire zoban nan kamar kin dena sona ne" kai ta gyada alamar toh. Biyan kudin abincin yayi sannan suka fito hannayen su cikin na juna. Shi ya buɗe mata mota ta shiga sannan ya zagaya ya shiga wajen driver. Bayan sun isa gida har parking lot yaje yayi parking da ita a ciki yana kallonta cikin idanunta ya ce, thanks for your time Yar gidan gwamna" "Ok sirikin gwamna" kansa ya shafa yana dariya. Mota ta buɗe ta fito shima fitowa yayi yana faɗin "Good nite" hannu ta ɗaga masa sannan ta nufi entrance ɗin gidan. A baranda  suka haɗu da Daddy. "Sannu da zuwa daddy" ta faɗa tana kallon shi. "Ina kikaje? "Na fita cin abinci ne" ta bashi amsa tana kallon shi. "Ok ke da Tahir ne? Daddy ya kuma tambayar ta. "Eh" ta bashi amsa. "Ok zan samar miki personal driver kinji ko? Kina wahalar da Tahir dayawa" kai ta girgiza tana faɗin "Ni bana son kowa da Daddy kawai ka barmin Tahir ɗin ai bai ce ya gaji ba" murmushi Daddy yayi yana kallonta da kyau ya ce, "Shikenan, ya kuma batun aure, akwai dan gidan gwamnan jihar Kano da zasu zo gobe za kuyi magana kinji ko? Ɓata rai tayi tana kallon daddy ta ce, "I have someone that I love" "ai baki fada min ba, who's he? Gabanta na faduwa ta ce, "Tahir". Gira ɗaya Daddy ya ɗaga kafin ya ce, "Who's he? "Tahir dae na gidan nan" "Tahir kuma? Cewar dad cikin mamaki, kai ta ɗaga alamar eh. Kai ya jinjina sannan ya ce, "Ok, kije ciki ki huta" da toh ta amsa sannan ta wuce ta bar Daddy a wajen..

🌸AMINATU 🌸Where stories live. Discover now