DGM 01

147 3 0
                                    

PREMIÈRE PARTIE:

N°01

ZAÏYA

Babban gida ne share kal-kal sai kyalli yake ba datti ko kadan ga shuke shuke daga ko wace kusurwa ta gidan ga kuma wani katon iccen lemu kore shar da shi a tsakiyar gidan wanda ya kara wa gidan kyau sosai. Gidan ne na masu rufin asiri sosai dan ya hadu daga mashiga babban kofa ce wanda zai sada ka da dakin samarin gidan wato su Hisham hakama idan ka dan shigo ta daman ka zaka samu banɗaki gaba kaɗan kuma dakin maigidan ne wato Abba idan ka kara gaba kuma babban falo ce dauke da ciki daya da toilette na matar gidan daga hagu kuma zaka samu dakin yan matan gidan wato dakin su Zaïya. Gaban shi kadan kuma kitchen ce share kal cike da kayan abinci daga bayan dakin su Hisham kuma garke ce ta raguna manya biyu a share ita ma sai abin cin su dake gaban su.

Ku san karfe 8h45 na safe kokowa take dan neman kowace kanta dalilin an danne mata wuyan ta an kuma shake ta sosai ta yadda baza ta iya ko da kwakkwaran motsi ne dan kwatar kanta ba. A bin al'ajabin ma har kawo yau bata taba sanin ko da wa take kokowan ba saboda kullum ta kan yi irin wannan kokowa ne a duk sanda ta kwanta barci amma har kawo yau bata taba iya ganin fuskar abin fadan nata ba. Sannan bata iya ganin komai nashi sai iya hannun da ake ta son danne wuyan ta, ita kuma sai ƙoƙarin neman kowace kanta take da iya ƙarfin da Allah ya bata.
Amma kash abin kamar da wuya dan ita ji take ma kamar ba da mutum take wannan wahala ba dan duk tabi ta jige da zufa ga uban nishin da take da kuma burma ihun da take duk a banza tunda ba me jin ta bare ta sa ran wani zai kawo mata dauki ko agajin gaggawa. Gashi kara jin ta take kamar duk jikinta ba rai dan kama daga babban yatsun kafarta zuwa kan ta duk ba wani amfanin da suke mata kai hatta da ɗan karamin yatsan ta na hannu ya gagare ta ta daga shi. Amma duk wannan halin da take ciki bai sa ta daina ambaton Allah ba daga cikin zuciyar ta saboda ko daidai da bakin ta wannan bata iya bude shi sannan ita kuma bata daina karantar duk ayar da ta zo zuciyar ta ba cikin hakan Allah ya hore mata da yawan karantar AYATUL QURSIYYU ba gaggauta wa. Sannu a hankali ta fara jin karfi na shigarta in da Allah ya bata sa'an buge idanun wannan abin da ya ad'dabi rayuwar ta. Duk da hakan ba'a daina shaƙar mata wuyan ba sannan ita ma ba ta daina karantar addu'o i da take a zuciyar ta ba duk da mafi rinjaye shine *AYYATUL QURSIYYU din kuma ta san da ta buge shi sannan tana kyautata zato a ido ne ta buge shi duk da har wannan lokacin bata iya cewa ta ga fuskar abun fadan na ta.

Sannu a hankali Allah cikin ikon sa ya bata damar bude idanun ta wanda sun canza launi daga fari zuwa ja sosai inda take jin wani yaji yaji da ga cikin su. Duk wannan kokawar da ta sha da ihun da tayi ta yi ba wanda yaji bare a kawo mata dauki gashi ita kuma tana bude idanu ta hango yan uwanta gasu kusa da ita sannan ta na jin maganganun su da na sauran mutanen gidan, amma a ce nata ba wanda ya ji duba da kusancin dake sakanin su na ko da tari kayi za'a ji ta, duk da haka ba wanda yaji uban ihun da tayi baiwar Allah.
Sai da ta dauki lokaci mai tsayi kafin ta samu ta farka daga wannan mummunar mafarki wanda ba daman ta kwanta bacci dan da ta runtse sai ta yi ire-iren mafarkai nan ko dare ko safe kai ko da rana ne idan dai ta kwanta to fah ba baccin kirki sai tashin hankali a mafarki. Allah sarki baiwar Allah har ya kai ga bata son kwanciya bacci saboda kullum tana cikin wannan fargabar kada ta kwanta azo a kashe ta kamar yadda me danne yake fada, sannan ko da bai fada ba duk me hankali zai gane yanda yake shage mata wuya ai son kashe ta yake...

Cikin kuka da faduwar gaba na yaushe ne wannan abun zai zo mata karshe dan yanzu kusan shekara kenan da fara wannan mummunar mafarki ko mafarkin wahala sannan kullum abu ɗaya ake shi ne na kashe mata jiki da kuma shake mata wuya da iya karfi ta fara magana wa kanta da kuma addu'o'i

"Yaushe wannan abun zai bar ni nayi bacci kamar kowa? Wai ma me yake nema da ni ne? Shin aljan ne ko kuwa wani abun daban ne wanda har yanzu Allah bai bani ilimin sanin sa?.
Allah ka kawo karshen wannan abun, ya Rabbi ka fini sanin abin da yake damuna da kuma abin da yake son cutar da ni, ya Ubangijina kai min maganin abin da na sani da wanda ma bani da masaniyar sa ka yaye min wannan wahalar da nake ciki, ka gaffarta min ya Allah ka yafe min kurakurai na ka bani lafiya mai amfani."

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant