LAMIDO
"Kana nufin ka duba da kyau yanzu ba sunan ta a jikin takardar."
"Eh Baba ba tantama babu shi, saboda na duba da kyau ai tuni aka shafe shi kamar ba'a taba rubuta shi ba"
Cikin dariyar nasara da jin dadi yace
"Yauwa Masha Allah aiki yana kyau Yacoub, ina fatan tana cikin damuwa sosai?"
"Damuwa ma sosai dan ta kwallafa wa wannan bac din rai sosai akan saurayin dake neman auren ta ma."
"Hhh shima shegen zamuyi maganin shi ne. Dole ne ta dauwama cikin damuwa kunci da kuncin zuciya. Zan san yanda sanyi na raba su duk da soyayyar su daga Allah ne sai mun sha wuya kafin mu samu nasara."
"Baba ai ni ba ma wacce take ban haushi irin Sadiya sam taki bamu hadin kai. Yarinyar kuma gata da tsari sosai a jikin ta dan iyayen ta ba su bar ta haka ba, sannan ita ma tana yawan azkhar, mtsw" Inji Salma
"Bar ni da Sadiya Salma ni nasan yanda zan yi da ita. Kin san yarinyar duk ta gama mamaye zuciyarta ne shi yasa amma sannu a hankali zata dawo ne"
"Hakane kasan tun da ta koma can ta rage yin aiki sosai sannan bata cika zuwa taron dare ba kullum cikin bada uzuri take."
"Zata dawo hanya ne da kan ta. Kin san ita da sauran yan uwan ta biyu duk suna son bijirewa wannan abu ne, bare kuma da ta auri wannan mutanen nan masu dagaggen wondo. Tunda ya fara kaita islamiyyar su ta fara bijire mana da wadan su abubuwa."
"Kawai iya shege ce irin ta ta Baba, ai in kananu ne ita ce gaba."
Mama Hauwa dake zaune dan gefe da su saman dan tabarman kaba tana gutsira goron dake hannun ta tana kallon su amma bata tanka mu su ba. In da sabo ta saba da wadannan mutanen uba da y'ay'ansa zababbu biyu cikin y'ay'ansa shida suna tattaunawa akan lamarin da yau fin shekara uku suna yi wa mutum daya amma har yanzu basu samu yanda suke so ba daga yarinyar. Wani lokaci sai tayi ta jin tausayin yarinyar da iyayen ta dan sam su basu ma san ya yarinyar su take ba amma wani can ya hango yana ta neman yanda zai yi kastsara ta dan kawai su dauwama cikin kunci da damuwa. Ta sauke gwauron numfashi te fesar. Tana ta jin su suna tsara yadda zasu kara cutar da yarinyar da kuma kananun yara wanda ba su gama samun baki ba.
Wanda ba'su ma san da sunayi ba sai dai mutum ya ji a ji kin sa ko ya gani a aikace a jikin y'aran shi. Su kuma suna kara jin dadi idan sun yi nasara akan mutum su ka ga mutane na ta wahala. Duk da duk wanda suka kwallafawa rai indai ba suyi nasara akan shi ba to fa sun kama bibiyar sa kenan har illah Masha Allah.★★★
SHEKARA TA SAKE GEWAYE WA
(Shekara ta uku kenan ina BAC)"Inna lillahi wa Inna ilaihiraji'un...! Ayah dan Allah tashi, dan Allah ki tashi me zance wa iyayen ki in dai har mutuwa kikayi."
"Mama kamar fah suma tayi" Daya daga cikin yan matan ta ankarar da mahaifiyar su.
"Debo ruwa mu gani yi sauri mana. Wallahi tsabar rudewa na manta ma da wani ruwa."
Hankalin ahalin gidan babba da yaro duk a tashe yake ga su duk tsastsaye suke sun kasa zama saman kanta ba mai sukunin zama a cikin su, daga masu kuka na yi masu zagaye dakin nayi tsabar tashin hankali inda ita kuma mahaifiyar su take zaune dabas a kasa tallafe da kan Ayah saman cinyar ta wanda alama ya nuna ba motsin rai a jikin ta. Gashi lokacin shan ruwa yayi ko ina sai kiran sallah ake (ana cikin watan Ramadan ne inda yau azumi ta Ashirin kenan) amma su ba mai sukunin da ya kurbi ko da ruwa karamin cup ne dan bude baki suna ta Ayah.
Bayan ta kawo ruwa mai sanyi ta mika wa mahaifiyar su. Da sauri ta karbi ruwan ta kwara gaba dayan shi ga fuskar Ayah wacce take kwance saman cinyar. Ita da kanta sai da ta jike.
Nan da nan ko ta fara jan wani uban dogon numfashi kafin ta fara ƙoƙarin tashi daga kwancen da take saman cinyar ƙanwar mahaifiyar ta tana wani irin abu tana lumshe ita tana budewa irin har yanzu bata dawo normal cikin hayyacin ta sosai ba. Nan take mutanen wajen suka fara hamdallah suna riga-rigan karasawa inda Ayah take rike da kai tana jujuyawa.
VOUS LISEZ
DAGA MAKWABTAKA
Non-FictionInna lillahi wa Inna lillahiraj'un abin da yawancin mutanen dake gurin suke fada kenan duk inda ka ƙalla sai dai kaga bakin kowa na motsi bi ma'ana kowa da abin da yake fada kenan... Mutane kewaye da ita kowa idanunsa cike da hawaye hanci sai zuba r...