Bayan na dawowa da yan satit-tika uncle dina (wan mahaifiyata) yazo min da labarin wani abokin shi yace ana neman ma'aikata a bankin su mai zaman kanta inda ya nuna min yana son na kai takardu na sun yi magana da abokinsa. Da fari ban so yin hakan ba saboda na kwallafa rai ina da burin sai na samu bac amma daga baya da uncle ya tsaya ya nuna da kwadaitamin mahimmancin yin haƙan sai na amince zan aje walaAllah ko zan dace tunda yanda aka rubuta a kwatance yadda ake son ma'aikaciya/ma'aikaci ya kasance ni har nafi hakan. Da taimakon sa da ta 'yan uwa da abokan arziki da kwarin gwiwarsu na hada takardun da ake bukata na bawa shi uncle din nace ya kai min. Ya nuna min sam ba zai kai ba na kai da kaina yafi hakan ko nayi da kaina na kai har kamfanin inda ake ajewa na bayar na dawo sai dai fatan dacewa.
Bayan watanni da aje takardar neman aiki shiru kake ji malam yaci shirwa saboda ban ji daga masu neman ba ma'ana ban ji an neme ni ko kira na ta waya ba hakan yasa na fidda ran samun wannan aikin daga kaina da zuciya ta na shiga harkar gabana yayin da har lokacin ban daina mummunar mafarki ba sannan mun dasa da MZ daga inda muka tsaya yayin da nake sama sama da shi har lokaci dan ina kyautata zaton halinsu na maza yake son nuna min sannan ban son a maimaita hakan yasa nima na tattare shi na aje shi gefe ba wai dan ban son shi ba ah ah saboda nemawa kai da zuciya salama duk da kullum sai ya kira musha hira har dare kuma har lokacin son shi bai taba girgiza daga inda yake ba sai ma daɗa karuwa da yake.
Bangaren karatu Maa taso sannan ta kwadaita min na karanci likita na fita batun BAC na ki saboda naki jinin karatun likita hakan yasa wannan shekarar ban komai nake nan zaune gida ba karatu ba komai ina kashe zani. Ganin haka yasa Maa tace na koma islamiyya ya fi zaman.Kwatsam wata ranar asabar da safe wajen tara da wani abu ya gotta ina zaune saman kujera ni ɗaya a farfajiyar gida yayin da Maa take cikin daki gidan ba kowa dan duk yaran sun tafi makaranta Sadiya ta shigo cikin farin ciki fuskar ta cike da murna sai murmushi hade da dariya take min yayin da muke hada ido da ita ta wuce Ni ta dauko kujerar roba itama ta aje dab inda nake kafin ta rungume Ni, ina biye da ita ta ido da hanci bude ina kallon yadda take cike da murna da annashuwa sosai nake cikin mamaki da zakuwar jin me muka samu na murna haka ban an kara ba na ji ta dafa ni tana fadin abin da ya kara shayar da ni ruwan mamakinta saboda a nawa tunanin bai kayi tayi murna haka ba
"Kawa albishir! Jiya nayi mafarki kina aiki a banki". Cikin zumudi da murna
"Allah yasa! Kai amman yau kinsha da ni duk wannan murna da farin ciki na mafarki ne dama. Allah na ɗauka wani abun ne daban amma kin san mafarki ba gaske bane" Cikin mamakin jin abin da yasa Sadiya take murna haka ina murmushi yake.
"Dama ne ma? Dama ne? To me yafi wannan da kike son ji aikin banki fa nace miki? Mafarki ne amma Allah da gaske zaki samu ne In sha Allah". Ta karasa tana marai-raicewa.
"Haba kawalliya i hakuri kawai dan na fidda wannan batu ta aiki a raina ne ban zata shi kikayi mafarki a kai bane. Haka ne wani lokaci mafarki yakan zama gaske. Allah ya yarda kawata" Cikin muryar lallashin da kwantar da kai a ƙafadar ta.
"Yauwa ko ke fah ameen ya Rabbi In sha Allahu ma zaki samu ne, amma yanzu da kin fara aiki zakiyi wuyar gani ki barni da kewarki". Cikin muryar tausayi yayin da take shafa kwantaccen sumar kan Ayah dake saman ƙafadar ta har lokacin. Gwanin sha'awa idan ka gansu.
"Hhh sai kace wanda akace zan bar garin. Meyasa zanyi wuyar gani bayan aikin anan garin zanyi shi " Yayin da nake ƙoƙarin tashi daga ƙafadar Sadiya muna fuskantar juna.
"Eh! Ina nufin in kin fita bakwai sai shida fa ake dawowa mu da ganin ki ai sai yamma ke nan har na fara jin kamshin kewarki tun yanzu kawa". Tayi kalar marai-raicewa ta lankwabar da kai tana kallona.
"Allah da abun dariya kike aikin da ban ma samu ba kike irin wannan maganganun kawa sai kace wacce aka ce miki ranar monday zan fara tafiya aikin". Na karasa da murmushi mai hada da dariya ina mamakin Sadiya tunda na aje takardar nan take ta min addu'a kai kace ita ce mai neman aikin ta damu sosai.
"Ai na fadamiki zaki samu ne ki bar ma tantanma ko shakku"
"Ki ji ki da wata magana ai sanin gaibu sai Allah dan wannan ai gaibu ne tunda masu neman na da yawa"
"Ai nima In sha Allahu nace Shikenan naji! Dama abin da yasa nayi sammako ke nan tunda na yi mafarkin nan cikin dare ina Allah Allah gari ya waye nazo na fada miki. Bari naje na gaishe da Maa sai in koma gida kafin y'aran su tashi su san bana gidan, ko Babansu bai san da na fito ba sabar ina zumudin na fadamiki wannan mafarkin, shine ko murna bak'iya irin sosai ba" Tana yatsina fuska irin bata ji dadi yadda ban bawa mafarkin ta mahimmanci ba.
"Haba kawa wa ya ce ban yi murna da jin mafarkin ki ki ba ai mai sonka ne ma zayi mafarki da kai har ya ga abin alhakairin ka nayi murna sosai da jin hakan sannan Allah ya tabbatar mana da hakan in alkhairi ne kawa ki bar wannan kumbure kumburen nan Maa tana ciki kije ku gaisa din". Na runguma ta ina murmushi dan ta saki ranta Nan da nan itama ta rungume ni muka kyalkyale da dariya.
Shiru shiru har lokacin ban ji kira ba sannan ban ji an ɗauki ma'aikata ba sai na tuntubi wani wanda muka hadu da shi wajen neman aiki shima yaje aje takarda nan muka saba muka amshi numbern juna ko in waninmu ya samu labari ya tuntubi dan uwansa. Wayanshi na ta ringing bai daga ba har ya katse dan kanshi Ni ma sai ban kara kira ba bayan kaman minti biyar sai gashi ya maido kira, na ɗaga muka gaisa cikin nishadi yana ta zolaya ta
"Babban yarinya naga kiran ki bana kusa ne, ya ake ciki". Da yasan ya yi laifi (sanin cewa bana son yana kirana da hakan) har ina jiyo murmushi da yake ta ɓangaren sa a waya.
"Hhh rabani da babban yarinyar nan nima tambaya nake dan naji shiru ne, mutanen nan har yanzu basu kiramu ba, ko har an dauki na ɗaukawan ne ban da labari?"
"Kina ina ne? Baki da labari kenan ai tuni an ɗauka har ya fara aiki yau kusan fin wata daya"
"Kai haba! Wallahi ban da labari ina nan zaune jiran gawan shanu, ashe har an tafi wata da daukawa to wa suka dauka ne a cikinmu?". Da mamaki tayi tambayar.
"Ai ba anan suka ɗauka ba a can Diffa suka kawo wani"
"Na fahimta Allah ya bamu wani mafi alkhairi"
"Aameen ya Allah Manyan kasa". Ya kuma zolaya ta yana ta min dariya har cikin wayan nake jin dariyar sa.
"Kan ka ake ji ni rabani da Manyan kasa nan kar Manyan su ji su min titse". Sai turo baki take kamar yana ganin ta.
"Hhhh wa isa ya miki wani abu ya batun karatu wace matsaya kike"
"Babu wata matsaya likita Maa take son na karanta Ni kuma nafi son na koma yin BAC"
"Dan Allah rabu da zancen BAC din nan ki kama wani abun in yaso ko baki son likitan sai ki ƙaranci wani fanni in yaso sai kiyi candidate libre na bac"
"Ni fah in ba BAC ba bana bukatar wani karatu"
"Ah ah lalle soyayyar ki ga bac mai girma ce Allah ya bayyana mana alkhairi shi"
"Ameen". Cikin sanyin murya saboda kowa hake yake cemin gashi ban san me yasa nake son shi haka ba saboda nayi nayi na fidda BAC din nan a rai amma kamar ana kara ruramin yin sa ne. Haka dai muka tattauna yabani 'yan shawarwari duba da cewa ya girmemin sosai ya kwadaitamin da na amince nayi karatun likitar tun da Maa na son hakan. Ban san me yasa ba amma sam bani jin yin wata karatu bayan bac; zuciya ta duk sai naji ta cunkushe waje daya na kan ji irin haka ne duk lokacin da ake min magana ta cigaban karatu ko ake min zancen aure. Na rasa gane abin da yake sa Ni jin hakan. Bayan munyi sallama da shi na fada wa Maa yanda mukayi da shi tuni an ɗauki ma'aikaci saidai mu tari wani kuma.
★★ Bayan wata biyar bana taba mantawa wata ranar juma'a ina kwance ina danne danne a wayata sai ga kira wata bakuwar number kamar kar na daga har ya kusan katse wa kafin na daga nayi shiru ban an kara ba naji sallamar mallakin number cikin wata murya mai cike da natsuwa da kuma kamala inda ya baiyana min kansa da kuma abin da yasa ya kira yana nema na ranar juma'a in zo kamfani za'ayi min job interview kafin a ɗauke ni. Nan da nan na amsa masa da zan shigo ranar juma'ar In sha Allah. Yana kashe waya na fito da gudu sai dakin Maa ina ta murna dan cike nake da farin ciki samun wannan kiran, Nan da nan cikin farin ciki da murna na faɗa wa Maa yadda mukayi da shi ita ma tayi farin ciki sosai sannan tayi min addu'a samun nasara da alkhairi. Muna idawa da Maa nayi gidan su Sadiya cikin gudu gudu sauri sauri bayan sallama ban saurari amsar su ba naje da gudu na fada jikinta na rungume ta itama ta rungume Ni, ban ce da ita komai ba yayin da ita ma bata tambayeni komai tsawon wani lokaci kafin na katse shirin da fadin
VOUS LISEZ
DAGA MAKWABTAKA
Non-FictionInna lillahi wa Inna lillahiraj'un abin da yawancin mutanen dake gurin suke fada kenan duk inda ka ƙalla sai dai kaga bakin kowa na motsi bi ma'ana kowa da abin da yake fada kenan... Mutane kewaye da ita kowa idanunsa cike da hawaye hanci sai zuba r...