DGM 07

9 1 0
                                    

BAYAN SATI DAYA

                 Mahaman Zayyan (MZ)

       Kirr kirr kirr waya ce ke ta kuka yana neman dauki. Shi kuma yana rike da wayar a hannun sa yana ganin kiran amma yaki dagawa saboda dama indai ta kira baya taba dagawa sai dai ya maida kira. Kuma ita ma da kanta ta san da haka hakan yasa yaƙi dagawa yana jira wayar ta tsinke ya maida mata kira. Yanzu in ya kashe nata kiran ya kira ta shima kuma rigima ce zata sake yi masa shiyasa yaƙi ya katse kiran ta har sai da ya katse dan kanshi sannan ya maida mata kira.

   "Mon amour albishirin ka." Cikin zumudi  da tsananin farin ciki take maganar

   "Goro fara kal yar babyta, me muka samu ne haka."

   "Chéri abin da muka jima muna dakon zuwan sa shine yau Allah ya bani damar furta maka shi".

   "Masha Allah chérie ta! Wannan menene shi? Na kagu na ji shi"

  "Umm... dama zancen auren mu ne na amince ka turo." Sai kace yana ganinta har wani rufe ido take da duka tafukan hannayen ta tana murmushi mai kama da dariya.

   "Da gaske kike ma chérie?"

   "Eh wallahi da gaske nake, har cikin zuciya ta."

     'Sai da bayan da tayi BAC wajen so uku bata samu ba shine yanzu take son na tura gidan su? Nan ai lokacin da tace zata sake yin BAC na uku na roketa Allah Annabi akan dan Allah ta hakura da BAC din nan ta zo muyi auren mu ai k'iyawa ta yi, ta nuna lalle fa BAC  shine gaba. Sai yanzu da ta rasa shine take mun zancen aure. Duk da har yanzu dai ina sonta sannan a shirye nake da na aure ta sannan naji dadin albishir din da ta yi min, amma...'. Abinda yake fada a zuciyarsa kenan. Sannan kuma bai san me yasa ba ya maida mata da

"Amma chérie kuma kamar sai da kika ga baki samu abin da ya fini ba shine yasa yanzu kika amince da son na turo din ko?."

   "Haba chéri yau ni kake cewa haka? Dan kawai na furta mata haka? Ban sammaci wannan kalmar daga gare ba sannan ina zaton ko da wani ne ya fadi haka a gaban ka sai inda karfin ka ya kare, kuma ko da duk duniya zasu fadi irin haka a kaina ina da yakinin banda kai, amma gashi yau da bakinka ka fada min..."

Tana kwance saman katifa ne manne da wayar a kunne amma da jin abin da chérinta ya fada sai da ta mike zaune dan furicin masoyinta wanda tunda take da shi bai taba fada mata makamanciyar abin da ya fada mata yanzu ba. Me yake damun Zayyan ne? Yau Zayyan ne da fada mata haƙa? Idanun ta duk sun kawo ruwa amma basu sauka ba. Tana can cikin mamakin furicinsa ta kara jin

   "Eh ai gaskiya na fada bae, ba karya nayi miki ba. Nan nan lokacin da nake binki tun bayan bac din ki na farko a kan ki amince min na turo gidan ku amma kika yi ta wasa da hankali na. Hakan yasa iyayen na suka bani auren yar uwata, Ni da ke duk hankalin mu yayi mummunar tashi inda a lokacin kika ƙ'i saurara ta sannan soboda son da nake miki yasa inda na yi miki alkhairin ki kwantar da hankali zanyi duk yadda zanyi na ganin na ruguza wannan maganar. Inda baki ma san ya akayi, ya na yi fama da iyayena ba ke dai kawai kiran ki nayi na fada miki an sauke zancen aurena da Hauwa wacce iyayena suka zaba min. Kuma duk nayi ne saboda ke, sannan a lokacin ma sai da na fada miki cewa mahaifina ga abin da ya gind'aya min.. ko in kin manta ne na tuna miki?"

Ban so na fada mata duk wannan maganganun ba saboda nasan zai bata mata rai sannan bana son duk wani abin da zai bata ranta amma dole ne yau nayi hakan dan tasan da kuskurenta.

   "Bana bukatar tunin ka chéri, na gode maka, sannan na gode da soyayyar da ka nuna min, amman kasan cewa nafi karfin wulakanci ko da a gurin wani ne balle kai. Yanzu ma ba rasa masoya nayi ba sannan ba wai dan ban samu BAC yasa nace na aminta da kai ka turo ba, lokacin hakan ne yayi sannan naji amsa ta... kit ta yanke wayar"

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant