GDM 25

5 1 0
                                    

<< GIDAN SU ZAÏYAH >>

Bayan shigar ta gida bata zarce a ko ina ba sai cikin kuryar ɗakinta,
inda ta yi masauki saman katafaren gado ta saka duka hannayen biyu ta yi tagumi tana al'ajabin abubuwan da suke faruwa kwanakin nan cikin rayuwar y'ay'ansu, duk da ba abin al'ajabi bane saboda yin Allah ne. Amma abun yana damun ta sannan ita uwa ce ba zata so ta ga ya'yanta cikin ciwo da damuwa ba ko koma baya cikin y'ara sa'annanin su ba, fatan ta kullum Allah ya basu kwanciyar hankali da ta zuciya da kuma lafiya mai amfani.
Sannan tana ganin fa'idan addu'a sosai saboda Allah yana karba sannan tana gode masa a ko wane lokaci sai dai shi kaddara bata taɓa canzawa sai dai ta zo maka da sauki dalilin karfin addu'a da kake. Hakan yasa Allah yake saukaka musu al'amuran su.
Tabbas Zaïya tana cikin ciwo duk da ita tana ƙoƙarin boye wa dan kawai ta kwantar wa da iyayen ta hankali amma tun bayan faruwar wannan lamari ta lura da yanayin y'arta ya canza gaba ɗaya saboda tafiya take tana ramewa ga wasu uban kasusuwa da suka bayyana a wuyanta wanda da ba haka take ba sannan ta yi wani fayau ta ita ta kara haske saɓanin da, saboda Zaïya yarinya ce mai wayo da son mutane ga ta faran-faran bata da fari sannan ita ba baka ɓace, tun faruwar lamarin take basu maganin miyagu wanda ta amso wajen Sarkin mayu ga shi bata fasa musu addu'a ba kullum tana tofa musu a ruwa suna sha, mahaifinsu ma kullum cikin nema wa ya'yansa magani wanda musulimci ya amince da addu'o'i yake.

Yanzu abinda ya fi damuwa Maa shi ne rashin Hisham a kusa da ita, ya yake ciki? Ya ci bai ci ba ba wanda zai damu da shi tunda goggonsu Bintou ba damuwa ta yi ba. Bata san hawaye suna sauka daga cikin idanunta ba sai da ta ji ya dafa kafadarta yana share mata su

"Ki daure! Ki daure Allah yana son mai hakuri! Allah yana sane da mu sannan zai ya ye musu, kar ki bari zuciya da shedan su yi galaba kan ki wajen sakamiki abin da ba shi ba cikin kwakwalwar ki"

Ta yi murmushi mai ciwo tana ƙoƙarin shanye hawaye da suke kokarin fitowa
"Abban Zaïyah kai ma shaida ne ban taɓa saba wa mahaliccina kan son ya'ya ko dukiya ba. Ina wannan hawaye ne ba don komai ba sai dan tausayi irin na zuciyar mahaifiya" duk ƙoƙarin ta na ganin ta daina zubar da hawaye hakan ya gagara. Sai da ta zubar da su tass ta ji zuciyar ta ya yi sanyi.

"Alhamdulillahi da Allah ya baki wannan rahamar" yana zaune bakin gadon rungume da ita, ta kalle shi cikin mamaki

"E, tun da ke kinsamu kin yi kukan, zuciyar ki ta yi sauki daga nauyin da ya yi. Amma Ni tawa zuciyar har yanzu tana min nauyi saboda kukan zuci nake wanda hakan banda ƙara wa kai cuta ba abin da zai haifar min. Kafin na shigo wajen ki da na ga Zaïya zaune sai da zuciya ta ya karaya, kwata-kwata ta canza ciwo yana cinta sannu sannu, ban san abinda yake min dadi ba sannan ga Hisham da bamu san halin da yake ciki ba..."

"Inna lillahi wa Inna ilaihiraji'un" ta katse shi da faɗin haka

"Inna lillahi wa Inna ilaihiraji'un³" shima yana maimaita suna kallon junansu

Da gudu ta shigo dakin dan ko sallama bata ayi ba saɓar tana cikin tashin hankali tana son magana amma ta kasa, ta fara maida numfashi tana haki, Abba da Maa a tare suka mike suka isa inda take tsaye tana haki sai kace wanda ta yi gudun tsere tunda lamarin nan ya faru take jin rauni a zuciyarta, daga ta yi dan tafiya ko sauri sai ta ji dugun bugun zuciyarta ya karau ba kamar da ba...

"Lafiya Zaïya kike wannan haki daga waje zuwa cikin daki" Inji Abba yana shafan gabon bayan ta dan ta samu zuciyar ta ya daidaita

"Ah ah wai lafiya kike, me ya ja miki wannan hakin ne? Kinga wani abun tashin hankali ne? Ki nutsu ki yi mana bayani mana kina kara jefa mu cikin tashin hankali ne fa Ayah" Maa ta tambaya cikin al'ajabi.

Tana duge tana maida numfashi rike da ciki har lokacin magana ya gagare ta, ta nuna musu kofar fita daki da hannu tana ƙoƙarin magana amma magana ta ƙi zuwa

Vous avez atteint le dernier des chapitres publiés.

⏰ Dernière mise à jour : May 16 ⏰

Ajoutez cette histoire à votre Bibliothèque pour être informé des nouveaux chapitres !

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant