DGM 19

4 0 0
                                    

Bayan kirana da akayi a waya da yadda aka kwatantamin halin da yake ciki sosai na shiga damuwa amma tuna cewa komai daga Allah ne yasa nake jin sanyi kaɗan daga can kasan zuciya ta yayin da na amsa cikin damuwa da sannan muryata har rawa take
     "Hisham shima jiki ba dadi ga shi can yana cikin mawuyacin hali" cikin dabara mahaifin su yaƙe daɗɗaba min baya al'amar ban hakuri da lallashi.
Na juyo muna fuskantar juna yayin da hawaye suke sintirin sauka daga idanuna zuwa saman kumatuna kafin su gangara zuwa kasa
   "Abban Zaïya! ya zan yi? ga Zaïya nan ba lafiya? Sannan yanzu a kira ace min shima yana cikin mawuyacin hali, da wanne zan ji?"
Nayi saurari faɗin
  "Astagfirllah! Allah ka sassauta musu ka basu lafiya mai amfani, ka tashi kafadun su ya Rabbi" yayin da nake goge ruwan hawayena da gaban rigar sa. Inda ya amsa min da
    "Ameen ya Rabbi, tun farko abin da yakamata ki fada ke nan Oum Zaïya, ba wai kuka ba"

Yayin da jikin Zaïya yayi sanani kafin inda muka fidda rai da ita kafin Allah ya dauke mata duk wani radadi da take a jikin ta. Yayin da a lokacin Fanta take fadan rashin kai Zaïya gidan sarki dan a tsallake ta
   "Me zai hana ku kai ta gidan sarki munafukar nan ta tsallake ta?na ke ga kamar hakan zai fi akan zaman ku gida yarinya tana ta wahala" ta sake maimaita a karo na biyu

  "Gidan sarki fa Fanta ? Haba ta ya ma zamu yi haka, ai wannan bai kamata ba, In sha Zaïya zata samu sauki ne, ki kwantar da hankalin ki, nasan abin da yasa kika fadi haka" na amsa mata yayin da nake ganin rashin dacewar yin hakan, gefe guda kuma tunanin halin da Hisham yake ciki nake.

Cikin fushi Fanta ta amsa da "shikenan tun da kina ganin hakan shine daidai, ke mai zuciyar imani baki son ki tozarta Sadiya ko? yayin da 'yarki take cikin mawuyacin hali kike wasu magana"

   "In sha Allah ko bata tsallake min yarinya ba inda sauran rayuwar ta Allah zai bata lafiya, sannan ina da yakinin amana ma ba zai barta taba, Zaïya kuma Allah zai bata lafiya, na gode miki sosai da kulawar ki gare ta"
Na ci-gaba da cewa "Banda abin ki akwai Allah shine wanda zai iya komai a sanda ya ga damar hakan, kar ki manta kullum cikin addu'a muke wa ya'yan nan, dan Allah ki bar maganar nan haka duk ɗaya muke. Kaddara ce ta riga da ta afku sai dai fatan Allah ya kiyaye gaba ya tsare zuri'ar mu

   "Shikenan Allah ya bata lafiya" ta amsa cikin sanyin murya. Saboda gaskiyar maganar ranta bai so haka ba, ta so a ce an je gidan sarki.

Yayin da nake ganin hakan kamar bai dace ba, ace yau mune kuke karar Sadiya, Allah ya tashi kafadun yaran nan ya basu lafiya. Ban an kara ba na ji ta ci-gaba da cewa

   "Hum Allah dai ya kyauta, Oum Zaïya amma ai ba yau ba nake ta cewa kina hana Zaïya shiga gidan sannan ko ita Sadiya tazo gidanki ki na hana yaran ki fitowa wajen ta kika ƙi yarda da ni ga shi yanzu kinga da idon ki amma shine harda cewa mu rufa mata asiri bayan ita so tayi ta kashe miki yarinya ta tona miki asiri. Yarinyar da bata ji kunyar neman kashe miki y'a ba kike kare wa har baki son a kaita gaban sarki?.

  "Haba Fanta ba ƙin yarda na yi da maganarki ba, yarinyar nan Sadiya na dauke ta tamkar ƙanwa kuma y'a duba da yadda suke da Zaïya, sannan ko da tana da abun cutar wa ban taba tunanin zata iya cutar da mu ba bare har ta cutar da Zaïya wacce ta kasance Aminiya gare ta, me afkuwa dai ta afku Allah ya kara tsare gaba da sauran yaran. Yanzu in kin lura amana da zumunci da addu'a su suka taka rawa wajen saukaka lamarin ma baki daya"

"Aameen Allah ya tsare su baki ɗaya
Kuma fa haka ne kam, ji yadda komai ya zo cikin sauki"

Fanta bata so haka ba, gani take kamar  Maah na kaunar Sadiya har wannan lokacin duk da abin da ta yi mata. Saboda ta so ace anyi ƙarar Sadiya dan ta tsallake Ayah amma sam Maa ta ƙi bada goyon bayan kasancewar hakan. Sadiya ta zame musu 'yar gida ta yanda take ganin rashin dacewar kaita ko ina ne.

          ***           ***           ***
Sannun a hankali na fara buɗe idanuna bayan wani lokaci mai tsawo. Ban san ya akayi ko me akayi ba bayan na saurari abin da ya faru bakin mahaifiyata na ji jikina kamar ba nawa ba sannu a hankali ganina da jina suka dauke sai bayan wani lokaci na farfaɗo inda a lokacin kusan karfe goma zuwa sha ɗayan rana ne. Ina ƙoƙarin tashi na ji duk jikin ba kwari. Na kokarta na jingina da jikin bango yayin da naga gidan ya kara cika da mutane saɓanin baya, wanda nake kyautata zato wasunsu sun zo kawai dan suga ya na koma, na mutu ko ina raye da sauransu. Sai dai Allah cikin ikonsa jikina alhamdulillahi yanzu bana jin komai saɓanin dazu da nake jin wasu abubuwa a fuskata, nan mahaifiyata ta taimaka min na mike tsaye na shiga bandaki nayi wanka na daura arwallah na fito na tada sallah. Bayan na gama ne tantie Fanta ta matsamin na fada mata ya akayi har na je gidan Sadiya a mafarki, nan na labarta yanda mukayi da yanda akayi ta canza zuwa mage da kuma yanda akayi na bita har zuwa gidan ta yayinda ta cika da sananin mamaki da al'ajabi yadda Sadiya take sauya wa zuwa wata halitta sai ware ido take

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant