DGM 04

9 1 0
                                    

BAYAN WATA UKU

Mun gama hutun makarata in da muka koma makarata yau kusa wata daya kenan, karatu muke tukuru yayin da nake karatun ne a garin Diffa. Kullum in nazo hutu in dai har zan koma makaranta to cikin kuke nake komawa haka wannan karan ma. Kuma kar ku manta har wannan lokacin ban daina wannan mummunar mafarkin ba, kullum cikin addu'o'i muke da iyayena. Shakuwa ta da masoyi na Mahaman Zayyan kuwa sai kara hauhawa yake in da duk ya bi ya dabaibaye cikin zuciya ta lungu da sako. Muna waya sosai da iyayena da kuma kawa ta Sadiya in da kullum muke cikin bada labarai kamar muna tare waje daya.

Haka ma iyayena kullum cikin kira suke, bayan sanin lafiya ta da yadda na tashi sai su daura da nasihu inda kullum maganar dai daya ce, ta na kula da kaina nayi karatun sosai duk da sun san ina koƙari sosai sannan abin da ya kaini garin kenan amma dole ne sai ana tunasar da ni. Kuma na kula sosai da addini na da tarbiyya ta sannan ban da ganin na sama da ni abin da yake jawo yawan lalacewar y'ara, ma'ana ban da cewa sai nayi abin da wani na yayi ko yake da shi. Na tsaya iya matsayin da Allah ya ajjeni ai dama kowane bawa ba daidai suke ba dan haka na kiyaye sosai wajen kula da kawaye. Sannan na kasan ce mai godiya da Allah a ko wane hali nake da kuma duk inda Allah ya ajjeni. Daga karshe kuma suyi mana addu'ar Allah yayi mana albarka ya shirya mu yayi wa rayuwar mu albarka me yawa. Na kan amsa da ameen ya Allah duk lokacin da suke mana addu'ar nan. Har sai da na tuna da nasiha da kullum Maa take yawan maimaita mini

"Ayah banda shashanci da bin kawayen banza bayan wadanda muka san ki da su. Ki rike mutuncin ki duk inda kike duk da bana tantanma ko shaayi akan ki ko tarbiyyar da muka baki amma duk da haka dan yau ne ka haifeshi baka haifi halin shi ba. Ki sa wa ranki da kanki ko bama ganin ki ki tuna Allah yana ganin ki duk inda kike dan Allah ki kula da Sallah.
Allah yabaki sa'a akan karatun ki da duk abinda kika sa gaba in alkhairi ne gareki da mu da sauran musulmai baki daya in kuma ba alkhairi Allah ya musanya miki da mafi alkhairin sa gareki. Amine!. "

Ire-iren addu'o'i da nasihar su gare ni kenan kullum. Duk ranar da sukai min irin wannan maganganun sai inji illahirin jiki na yayi sanyi. Sann nakan gode ma Allah ba adadi na azurtani da yayi da iyaye nagari yanda kullum bakin su cikin mana addu'a da fatan alkhairi suke.

Fitowar mu kenan daga class zamu break mun jera reras mu shida muna tafiya daddaya daddaya rataye da jaka a kafadun mu da kuma wani book haka rike a hannun mu sai taku muke muna rangaji kamar bishiyar maina Fatouma, Adama, Rabi'ah, Gambo sai Fatima Bintou da Ni cikon ta shidan su. Mu shidan nan kawayen juna ne kuma tunda muke bamu taba samun sabo da wani gulmace gulmace irin na sauran team din kawaye wanda kullum suna cikin rigima da kurayyar juna. Tafiya muke muna zolayar juna muna ta raha sai ga Fatouma da fadin

"Ma chérie kishin ki nake gaskiyar magana saboda kinyi dacen saurayi kamar Mahaman Zayyan. Wallahi ba karya ya hadu kiga yadda bawan Allah nan yake rawar kafa da ke abun har burgeni yake wallahi gashi albarkacin ki muma duk muna samun alkhairi. Ke kuma yar rainin hankali sai wahalar da shi kike kina ja mishi aji ke gani Zaïya mai aji kar dai garin jan ajin ya tsinke (tana banka min hararar wasa)."

Kafin taci gaba daga inda ta tsaya
"Bayan kina gani cikin mu ba mai tsayayyen saurayi irin naki gashi da komai ba laifi in da ni ke da wannan santalelin saurayin tuni na bashi dama an kayi tambaya da komai muna gama wannan shekarar sai dai gida na yara na barku da wahalar takarda da zuwa makaranta sai dai kuna dinga zuwamin gida kuna kwadayi."

Ta fara daga kafada tana irin tafiyar manyan mata wai ga ita mai miji a hannu kawaye su zo gidan ta kwadayi hhhh.
Duk sai da tasa muka tunsire da dariya muna kallon yadda take takawa daddaya tana rangwada wai ga ita matar manya. Muna cikin yin dariyar muka ji Rabi'ah na fadin

"Kai dan Allah ku bar takura wa kawata haka nan a kan Zayyan. Dan kun samu yana baku cin hanci shine kun bi kun takura mata dan Allah ku tsarara mata hakanan mana kuma mu fah bama yin Zayyan din nan naku ehe sai dan boko Karim ko kawata". Ta kashe min ido daya

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant