PDV Sadiya
Tun da garin Allah ya waye har zuwa wannan lokaci zuciyar ta yaki samun sukuni da kwanciyar hankali gani take kamar ba gaske bane, ina ma a ce mafarki ne da wallahi idan ta tashi daga wannan barcin baza ta sake komawa ba.
Amma duba da jin yadda unguwa ya cika da hayaniya game da hatsaniyar mutane yasa zuciyar ta buga wa da karfi har sai da ta sa hannayen ta biyu ta dafe daidai zuciyar yayin da take jin ina ma hakan bata faru ba ina ma ace karya ne duk wannan abun bai faru ba. Ko da ma ya farun ina ma ace ba da ita ba ne, ta share ruwan hawayen da suke ta sintirin sauka daga allon fuskar ta, yayin da ta tuna cewa da gaske fa wannan abubuwan sun faru la'akari da yanda muryar Zaïya yake tashi cikin ɗoɗon kunnen ta kamar yanzu take maganar
Nan ƙwaƙwalwarta ya fara hau-sine wa
Ji take kamar yanzu ne Ayah ke fada mata kalaman, yayin da fuskar Zaïya ya shiga gilmawa a cikin fuskar ta da ƙwaƙwalwarta tana ganin kamar yanzu ne take faɗamata kalaman ba a daren jiya ba, wanda tun a daren jiyan suka daskare cikin ƙwaƙwalwar ta suka yi tasiri sosai cikin zuciyar ta
'Bakin alkalami ya riga da ya bushe' wata zuciyar ta fada mata
Yayin da ɗaya zuciyar take kara karfafa mata da ƙwarin gwiwa 'Bai bushe ba, ta wani ɓangaren kuma ya riga da ya bushe kamar mu'amalar ki da mutane, amma su Ayah ko yau kika je musu da tuban ki za su karbe ki, su din mutanen kwarai ne. Kar ki manta lokacin da 'yan unguwa suke zargin ki su su na tare da ke'.
Nan ɗayar zuciyar mai ingiza wa ta fara kwabar ta a kan sam kada ta nuna raunin ta 'neman yafiya na me? bayan ita aka so tozarta a duniya'. Ta shiga fara jijjiga kan ta alamar tabbatuwa
Cikin sauki ta amince da gurbatacciyar shawarar zuciyar ta akan lalle ita bata yarda da abin da ya faru daren jiya ba tana goyon bayan mijin ta, wanda tuni ya fita zuwa kai karar su Zaïya gidan sarki.Sai dai me? kwalla ne suka fara rige-rigen wanke kyakkyawar allon fuskar ta, ba komai ne yasa sauka wannan hawayen ba illa amon muryar maah da yake amsa kuwuwa a cikin kunnuwar ta, ta sa duka hannayen ta biyu ta done su. Tana girgiza kai tun tana tsaye sai da ta danganta da zama kan daya daga cikin kujerun dake falon ta
"Sadiya na damka miki amanar Zaïya"
"Zaïyah amanar ki ce a nan duniya, na baki ita amana" ji kake muryar yana kara maimaitawa kan sa kamar yanzu ne take fada mata"Me yasa? Me yasa?" Shine abin da take fadi cikin daga murya yayin da hawaye ya jike mata gaban rigar ta sharkab.
Tana nan zaune yayin da ta yi nisa sosai cikin duniyar tunani, ta je muryar Ibrahim din ta yana fadin "Mama anti chéri" nan da nan ta kau da kanta gefe tana share sauran kwallan ta, zuciyar ta ya karaya 'lalle yaro yaro ne, yanzu bai san abin da yake faruwa ba har yake tambayar Zaïya dan bai ganta ta zo yau ba?' ta tambayi kan ta.
Sai dai kafin ta amsa masa ta ji "Mama ga can maman Abdrahaman kwance a kasa tana kuka" Inji ɗan ta babba.
Sai lokacin ma ta tuna da Hunaida wanda tun a daren jiya ta fadi kuma ba wanda ya bi ta kan ta dan mijin su cewa ya yi duk karya ne ba abin da ya same ta. Kawai sai tayi kamar bata ji su ba daidai kuma lokacin Ali ya shigo dakin ta da maganar...
PDV Hunaida.
Tun a jiya da daren da wannan abun ya faru da 'yar uwa na shiga cikin tashin hankali da tsangwama daga mijina. Ni lokacin da abun ya faruwa ina bacci saboda cikin baccin ne ma na ji hayaniya ta yi yawa yayin da nake tunanin na maƙara sallahn asubahi dan ina zaton ko gari ne ya waye, amma abun mamaki cikin magagin bacci na lalubo wayata ina duba lokaci sai na ga ashe karfe kusan hudun dare har yanzu da saura lokacin sallah. Da yake girkin Sadiya ce sannan inda turakar mijin mu yake da cikin gida akwai dan tazara hakan yasa sai ban kawo komai a raina ba kan wannan haniyar da nake ji, amma sai dai jin abun kamar kusa da Ni yasa na muskuta na tashi zaune na baza kunnuwa ko makotane barayi suka shigo musu. Sai dai abin da idanuna suka gane min ne yasa na yi hanzarin mikewa tsaye ban shirya ba, cikin zare idanuna sosai saboda ganin Sadiya ta shigo part din mu a guje daga ita sai fatar jikin ta ma'ana haihuwar uwar ta inda ta shiga dakina wanda shine farkon shigowa part din sannan ita nata dakin a kulle yake yayin da ban gama tsinkewa da mamakin ganin ta haihuwar uwar ta ba na ga shigowar 'yar uwa cikin wani irin hali wanda ba zan iya misalta muku shi ba sannan ban taba sanin ta da hakan, sannan me ya kawo ta cikin wannan daren? kuma kamar Sadiya ta biyo? duba da yadda take, kamar mai neman wani abu tana ta dube dube a ko ina amma bata shiga dakina ba wanda yake a bude, ko ina sai da duba yayin da ta jijjiga kofar dakin Sadiya inda ta ji a rufe har kitchen sai da ta leka. Ina cikin wannan kasurgumin mamaki sai ganin mutane nai na ta shigowa cikin gidan abin da ya kara bani mamaki ma harda iyayen 'yar uwa sannan ga 'yan unguwa maza da mata. Sai na fara ma 'yar uwa magana daga inda nake amma sai na lura kamar bata ji na hakan yasa na je kusa da ita ina ƙoƙarin ɗafata ganin halin da take ciki yayin da hawaye tuni sun wanke min fuska na tautsayin ta, yayin da na ji wata kalmar da ta ɗaki ɗoɗon kunnena zuwa cikin ƙwaƙwalwata wanda na yi mamaki jin sa daga bakin mai ita kalmar da ta amsa kuwuwa cikin ƙwaƙwalwata fiye da sau biyar
VOUS LISEZ
DAGA MAKWABTAKA
Non-FictionInna lillahi wa Inna lillahiraj'un abin da yawancin mutanen dake gurin suke fada kenan duk inda ka ƙalla sai dai kaga bakin kowa na motsi bi ma'ana kowa da abin da yake fada kenan... Mutane kewaye da ita kowa idanunsa cike da hawaye hanci sai zuba r...