JARABAWAR KARSHEN SHEKARA
Makarantar cike take da dalibai lungu da tsako duka inda ka wurga ido dalibai ne burjik saura zaune saman kujerun dake filin makarantar sauransu tsastsaye suna hirar duniya sauransu kuma suna magana ne akan takardar kashe wanda wasu suke jin ya yi musu tsauri wasu kuma suke jin ya yi musu dadi kowa dai da abinda yake fada duk wadannan masu maganar cikin su waɗanda suka gama sun ka fito ne yayin da saura har yanzu suna class ba su gama ba. Cikin waɗanda suka gama suka fito akwai kawayen nan shida inda biyu ba su gama sun fito ba.
Wani team na gani inda suke jajen yayi tsauri sosai yayin da team din yan shida suke magana a kan ci gaban rayuwar su. Sai kuma jimamin zaman jiran sakamako "Allah yasa muji alkhair" shi ne abinda yake tashi daga bakunan daliban dake cikin wannan makarantar. Can na hango su hudu zaune (Ayah, Fatouma, Adama da kuma Gambo) saman kujerun dake cikin filin makarantar suna jiran fitowar sauran kawayen su da basu gama sun fito daga class ba, suna hirar su ta yan mata inda Fatouma cikin zumudi da farin ciki take maganar"Mun gama da BAC yanzu sai zancen aure."
"Ance miki babu wani karatun bayan bac ne?"
"Ko akwai mun yi a dakin auren mu"
"Allah ya tabbatar mana abinda yafi alkhairi"
"Ameen! Amma fah ina ga Ayah ke ce ta farkon mu wajen shiga daga ciki"
"Allah matsani. Sannan idan kuma bamu ci bac din ba fa?"
"Shi ma ba zai hana ayi auren ba."
"Wai ku baku da abin fada ne muka ji ku shiru. Sai zuba muke da Ayah"
"A'a kice dai sai zuba kike, Ni kawai amsa nake baki. Ke ma dai banda abin ki kawa har yanzu fah bamu rike diplôme din mu a hannu ba."
"Wallahi hakan ba zai hana ni walwala ta ba, in ma ban samu ba akwai gaba ai"
"Ke fah dama karatun nan ba wani mahimmanci kika bashi ba shi yasa ba ruwan ki."
"Ku da kuka bashi mahimmanci Allah ya bada sa'a."
"Ameen ya Allah!"
Bayan fitowar sauran muka kama hanyar zuwa gida inda Souleymane ya zo ya maida mu.
Mu kai waya da iyayena inda sukai mana fatan nasara me yawa.Sai gamu bayan kwana biyar makaranta ta sake cika da dalibai masu duba sakamako wadan su na murna sun ci yayin da waɗansu na kukan ba su ga suna su ba. Muna gaban takarda da aka kafa sunayen wa dan da suka ci jarabawa muna ta duba wa amma shiru ba sunayen mu. In da cikin mu shidan ba wanda ya ci jarabawar nan take muma muka rungumi juna muna kukan bakin ciki saboda bamu ji dadin hakan ba a ƙalla a cikin mu shida ace ko da daya ce ta samu. Amma tunda lamarin na Allah ne da kuma rabo yasa muka rungumi kaddarar sannan muka hakura da kukan muka sake runguman juna inda mukai fatan Allah yasa sa da rabon mu nan gaba. Sai dai kuma wata shekara zamu sake zama in muna cikin masa rai. Mun yi jigum muna lalashin zuciyoyin mu muka ji
"Ni fah maganar gaskiya in kina jin tawa gwara ki bawa bawan Allahn dama ayi zancen auren ku musha biki mu rage zafin rashin samun bac da mukayi."
"Ai muna da shekara daya na sake zaman bac."
"Na fa lura Ayah sam baki son ana miki zancen aure. Bawan allahn kuna tare da shi yau kusan shekara daya da wani abu, kuna soyayya me safta yana son ki kina son sa amma ki kasa bashi dama."
"Ba zaki gane bane Fatouma, ba wai kin bashi dama nayi ba, wallahi nima wani sa'in bana sanin abinda nake fadi idan yayi min zancen aure. Sannan ga wani uban haushi da nake ji idan yayi min maganar."
"Hum dan dai kinsa karatun boko a zuciyar ki ne fa madam. Allah ya bamu abin da yafi alkhairi"
"Ameen kin gama magana. Yau dai kinyi magana mai ma'ana."
VOUS LISEZ
DAGA MAKWABTAKA
Non-FictionInna lillahi wa Inna lillahiraj'un abin da yawancin mutanen dake gurin suke fada kenan duk inda ka ƙalla sai dai kaga bakin kowa na motsi bi ma'ana kowa da abin da yake fada kenan... Mutane kewaye da ita kowa idanunsa cike da hawaye hanci sai zuba r...