DGM17

15 1 0
                                    

"Haka ne! ban san abin da kika gani a mafarkin ba amma zan iya fada miki iya abin da idanunmu ya gani tun daren jiya zuwa wayewar gari wala Allah ko zaki fahimci wani abu duba da cewa kina cikin rudani sosai." Inji Maa yayin da take kallona ido cikin ido.
Ni kuma sai aikin jijiga kai nake yayin da na kagu ta faɗamin abin da nake kyautata zato zai warware min wannan rudani da nake ciki. Saboda ƙwaƙwalwa da zuciyata har yanzu ihun mafarki suke min. Kamar tasan abin da nake jiran ji, sai tashin amon muryar ta na ji.

PDV Maah
     "Jiya da daddare ina daki saman darduma wajajen karfe uku da 'yan mintuna na dare ina lazimi. Na ji wani irin tashin amo mai karfin gaske da firgita wa wato ihu wanda yasa ni zabura na mike na leka inda na ji wannan sautin yayin da na gan ki kina wasu irin abubuwa kamar mai aljannu a kwancen kafin kikayi wata irin mikewa daga sama shimfidarki kika fara takawa sannu a hankali sai kace me bin wani abu. Sai nake tunanin ko magagin bacci yasa ki haka tun da naga kin tunkari wajen bandaki sai ban damu ba na koma na zauna na ci gaba da lazimina."

Tana fadin kamar ina bin wani abu, nan da nan massarrafar tunani na ta haska min lokacin da ta rikide ta koma ƙatuwar mage nake bin ta.

Kafin na ji ta daura da
   "Dan dai na san ba ki da aljannu da a ranar sai nace sune suke kanki saboda kina abu ne kamar masu ita saboda yanayin tafiyar ki a tsaye duk da haka ban kawo komai a kaina ba. Ni ci ba da abin da nake.
"Kafin na ji maganar mahaifin ki wanda ya gama arwallah kenan sai ya ga kin wuce shi zuwa kofar gida. Yayin da ko takalma babu a kafarki sannan babu kallabi, gashin kanki duk sun barbaje wanda Ni a farko ban lura da hakan ba. Hakan yasa mahaifin ki cikin mamaki ya fara kiran ki"

  "Zaïya! Zaïyah! Zaïyah!"

Amma abin mamaki sai baki amsa masa ba, kikai gaba sai tafiya kike yayin da kike kallon waje daya kuma kina ci gaba da tafiya. Ganin haka yasa mahaifin ki yayi azzamar kama ki ta tsintsiyar hannun yana kiran sunan ki a karo na biyu
     "Zaïya! Zaïya! Zaïya!"

Tun kina neman fisgewa daga rigon da ya yi miki abin da ya kara ba shi mamaki kenan har karfinki ya kare, hakan yasa kika fadi a gurin kina kallon saman ginin, yayin da mahaifin ki shima ya kai duban sa inda kike kallon tun dazu sai dai shi bai ga komai ba face wata mage wanda nan da nan tsabar tsoro ta gudu ta bar wajen. Hakan yasa mahaifin ki kokarin tashin dan uwan ki Ahmad wanda sam bashi da magagin bacci. Tunanin ko ban gama tawa nafillar ba

   "Ahmad rike min 'yar uwar nan taka kada ka bari ta fita dan na ga tana ƙoƙarin fita ban san abin da take gani ba, na samu na yi ko da raka'a biyu ne kafin musan abin da yake samun ta"

Ina jin haka na yi saurin mikewa na fita a guje jin abin da mahaifin ki ya fada inda na tarar da ke kwance kasa yayin da Ahmed yake tofa miki addu'a sosai hankalina ya tashi ganin halin da kike ciki

   "Abban Zaïya me yake samun ta ne? meke faruwa ne wai, dama ba banɗaki take son zuwa ne?

   "Ban sani ba nima na ganta ne tana koƙarin fita kuma ga shi taki magana bari nayi nafilla sai mu san na yi" inda ya tada ya fara nafillar sa.

Yayin da na amsa masa da "to"

Yanda na ga kina ƙoƙarin fisgewa dan ficewa daga hannun Ahmad yasa hankalina tashi, me yasa me ki? Halin da kike ciki yasa hawaye zuba daga idanuna. Take wani tunani yazo min na wani maganin gargajiya wanda yake maganin miyagu da na iska wanda nake siya baku son shan sa. Na yi sauri na shiga daki na bucika inda nake aje wannan maganin wanda ake shan sa cikin korya na dauko kullin tare da korya nazo na kunce na zuba cikin koryar na zuba ruwa a ciki na dauko ludai na motsa sosai nace da Ahmad din ya rike mun ke na ɗura miki.
Mun kokowa da ke kina fizge fizge da kyar muka samu muka dura maki wannan maganin. Nan take jikin ki ya saki kika zube a kasa hakan yasa muka sake ki yayin da naji kina wasu maganganu wanda na kasa gane kan su da ya tadamin hankali kina wasu abubuwa da yatsun ki kamar kina nuna wani abu wanda mu sam bamu fahimci komai ba, yayin da ganin halin da kike ciki yasa na fara ambaton Inn lillahi wa Inna ilaihiraji'un! Nan muka fara tofeki da addu'a Ni da Ahmed yayin da muke tunanin zance ya kare ashe da sauran rina a kaba.

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant