SADIYA
Cikin dariya
"Kawa kin san Allah! Ni ke ce ma kike kara min dariya kai dole ma in dara, ni fah ban ma sa wannan a kai na ba. Kin san wani abu ma? ai da fari bawan Allah shi ya so auren ta sai rawar kafa yake. Ba ki san wani abu ba ai ce masa tayi sai ta kare karatu zasu yi aure shine kwanaki suna waya da abokinsa yake fada masa auren sa sannan yace ya gayya ce shi dauran auren in da ya tura masa foton su shi da amaryar sa"."Kar dai ita ce amaryan tasa?"
"Kamar ko kin sani yana duba foton yaga ashe Jamilar sa ce wanda tace ya jira ta gama karatu. Ashe kawai yaudara ce."
Zaïya tana kai ruwa bakin ta take fadin
"To alhamdulillah mun huta, wannan case ya mutu kenan tunda zata auri wani. Hankalin mu ya kwanta."
"Ai na rabaki da namijin da ya fara neman aure tunda ya yi niyyar auren nan ko ba wannan sai yayi. Har fah kayan tambayar aure yaso su kai, Allah ne bai sa suna nan ajje da kaya to kinga zancen mun huta bata taso ba ma. Kinga kenan ba zancen kwanciyar hankali Allah dai ya kawo ta gari."
"Yo ita yarinyar har yanzu bata ce mishi gashi zata yi aure ba. Kuma haka ne fah indai sukai niyya sai sunyi "
"Ta ya zata fada mishi, tunda tana samu yana tura mata da kudi."
"Can ta matse musu, ai in kaki sharan masallaci za kayi na kasuwa."
Tuni muka gama karyawa Zaïya ta kau da kwanukan gefe. Ta mike saman katifar ta tana miko ma Ibrahim hannu irin ya zo gare ta. Shi ko ba bata lokaci ya isa gare ta yana wangale baki. Kafin naji tana
"Wai ni cewa nake Ali baya son macce mai karatun boko ko me aikin office ba."
"Haka ne ina shine ma babban dalilin da yasa taki auren sa tunda dai ita yar boko ce"
"Ta yiwu dan tana ma gaba gare mu a karatu sannan in kin gan ta dama cikakkiyar yar boko ce"
"Amma kamar na ji yace ya amince za tayi aikin banda komawa karatu dai"
"Tab ai ga irin ta nan wallahi tana da gaskiya da zata auri wanin shi. Yo ko ni ce wanda zan aura yace bazan yi aiki ba ko ba zan je karin karatu ba sabbb zan hakura da shi."
"Kawa ke ce kuwa? A kan karatu ko aiki sai ki hakura da aure"
"Ah ah kar ki fassara ni fah bance zan hakura da aure ba amma zan hakura da mijin tunda ba iya shi daya ne a duniyar ba.?"
Akan me ace iyayen mu su sha wahalar karatun mu sai mun zama ko kusan zaman abin morewa wani can daga sama idan ya fado yace bai san da zancen ba saboda ba wahalar sa a ciki.
Kuma fa abin bakin cikin suna ganin wadan da basa zuwa karatun bokon amma saboda son kai da san zuciya irin nasu sai ki ga sun nacewa masu karatu kuma sannan su nuna basa son karatun ai wannan zalunci ne karara. Wallahi_✓Shiyasa bahaushe yace ƙwarya ta bi ƙwarya._
_Son zuciya da zalunci ne zai sa ka auri wacce take karatu ko aiki ; bayan aure kuma ka hana ta karatu ko aikin....._
_✓Idan baka son karatu ko aikin..._
_....to yafi alkhairi ka auri wacce bata da alaka da karatu ko aiki._"Hakkun maganar ki dutse"
"Ban son zolaya fah"
"Ba zolaye bace kawa gaskiya ce. Kin ga dai ni dama ba wani nesa nayi a karatun bokon ba balle na tada hankali na amma ita ta san tayi nisa sosai a cikin ta ai kin yarda tai. Ba kin ce har license kare ta ba."
"Eh , ni dan Allah a bar maganar nan haka mu dauko wata me amfani."
"Haka ne kam, wai ya labarin Mahaman Zayyan ne?"
"Yana cikin koshin lafiya har kin za zuciya ta bugawa da sauri daga ambaton sa."
"Hhhh amma Zaïya baki da kunya, a gaba na kike irin wannan maganar."
VOUS LISEZ
DAGA MAKWABTAKA
Non-FictionInna lillahi wa Inna lillahiraj'un abin da yawancin mutanen dake gurin suke fada kenan duk inda ka ƙalla sai dai kaga bakin kowa na motsi bi ma'ana kowa da abin da yake fada kenan... Mutane kewaye da ita kowa idanunsa cike da hawaye hanci sai zuba r...