SADIYAAH
Zaune saman daya daga cikin kujerun dake daki mai zaman mutum biyu tana shayar da ɗ'an ta Khalifa. Ita kuma ta shigo da sallama a bakin ta tana wa Ibrahim murmushi mai burge wa. Bayan na amsa ta samu guri a daya daga cikin kujerun dake falon ta zauna a saman mai zaman mutum daya tana mika ma Ibou hannu irin yazo gare ta shi ko sai makale kafada yake irin ba zai taho ba.
"Yaron nan akwai shi ƙiwuya in ba Zaïya ba sai ya nunawa kowa halin shi na k'in mutum."
Hunaida tai maganar tana kara janyo yaron jikin ta duk da yana botsarewa
"Ke da kike kula mishi kenan, yaron nan in ya girma akwai kallo"
"Hhh ai kema kin fi ji da shi a cikin y'aran duka, ga shi da shiga rai Tubarkhallah ai Ayah ta iya zaban masoyi". Ta kara sa fada cikin zolaya tana kallon yaron yayin da shi ma ita yake kallo. Sai ta kara da fadin
"kwantar da hankalin ka yaro na. Kwanan nan masoyiyar ka zata shigo gari, ba kai ɗaya ba har mu muna kewarta wallahi."
"Wallahi kamar ko kin sani Allah Allah nake Ayah ta shigo gari, gashi na kira ta ma taki gayamin yaushe zata zo, duk rashin samun BAC din nan yasa har yanzu taki sakewa. Allah nima ban ji dadi ba kiga fa irin kwazo da ƙoƙarin ta wajen karatun nan."
"Haka ne Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare ta. In kin gama shayar da Khalifa ki ban shi tun da dai yau na Zaïya baya yi na gashi ko magana ban samu arzikin sa ba, ya kafe ni da ido sai kallona yake, miskilin yaro kawai."Tana masa harara na meka mata yaron yayin da nake fadin
"Yauwa karbi babana shi kam ba wani ƙiwuya gare shi ba kowa nashi ne ba kamar su alaramma Ibrahim ba. Gaskiya kin taimaka min ma dama ina son tashi nayi aiki gashi yaki ya bar ni na tashi sai tsotso yake. Ibou kam ai kun fi kusa tunda kema kinfi yin sa akan sauran y'aran".
Haka dai sukayi ta tattauna sakanin su suna zolayar juna kamar ba kishiyoyi ba. In ka gansu gwanin sha'awa suna zaune kalau.
Sadiya ta shiga kitchen ta fara aiki, tana cikin aikin ne ta tuna da lokacin da Ayah ta koya mata yadda zata sarrafa shi, dan ita da farko gaskiya bata iya sarrafa abinci ya zama kala daban daban ba saida Allah ya hada da bayin Allahn tasan da lalle dafa abinci ma iyawa ce. Tana cikin aikin ta tuno da lokacin da ranar farkon sallahn su a unguwar (wato karamar sallah) bata iya gâteau (cake) ba sai biscuits (cin cin) a na gobe salla ina da azumi a bakina ina ta aikin cin-cin haka Zaïya ta same ni takama min muna cikin aikin ne take tambaya meyasa banyin su gâteau ne, su alkakine su dubulan ne, su gyrebiya ne da dai sauransu dangin fulawa Masha Allah ta iya sarrafa fulawa sosai yarinyar. Cikin dadin jin ta iya duk wadan nan abubuwan nace mata"Ni gaskiya ban iya duk wadan nan ba sai cin-cin kadai shima baban Mahamadou yana son gâteau sosai to da nace masa ban iya ba sai ya bar maganar kin san shi baya bari na fita ko ina, balle na je na koyo amma yanzu alhamdulillah tunda kin iya ai kamar na koya ne. Ina ta jin dadi har a zuciya ta"
"Ai wannan ba wata damuwa ko yanzu in akwai ingrédients yin cake din zan miki ne"
Cikin zumudi nace ta lissafa min su yanzu zan kira Ali ya bada a kawo mana. Tana gama lissafa min.
Hakan ko a kayi na kira sa na fada masa ga abin da muke buƙata na yin cake cikin mamaki yake ce mun"Ba kin ce baki iya ba tun da dadewa ba"
Nace mishi haka ne amma a da kenan na labarta mai yadda muka yi da Zaïya nan yace yanzu kuwa za a kawo kayan hadin.
Kai ranar mun sha a zaba don mun aikatu sosai bayan musha ruwa muka ci gaba da aiki mune bamu gama sai wajajen sha'biyun dare gashi anga watan shauwal daren sallah kenan an kara kawo min kayan aikin sallah kuma, haka nace da Zaïya dan Allah ta kamamin muyi gashi gidan su sai neman ta ake dan ma na tambayi maah nace dan Allah ta barta ta tayani yin gâteau, sai wajajen ɗaya da wani abu muka kammala ta wuce gidan su. Ni da wadannan bayin Allah sai addu'a dan sun taimaka min sosai wajen inganta rayuwata.
Haka rayuwarmu yayi ta tafiya cikin aminci da nishadi gashi a dalilin su na koyi abu dayawa.
VOUS LISEZ
DAGA MAKWABTAKA
Non-FictionInna lillahi wa Inna lillahiraj'un abin da yawancin mutanen dake gurin suke fada kenan duk inda ka ƙalla sai dai kaga bakin kowa na motsi bi ma'ana kowa da abin da yake fada kenan... Mutane kewaye da ita kowa idanunsa cike da hawaye hanci sai zuba r...