DGM 15

7 1 0
                                    

Bayan sun zazzauna na juyo gaba-daya muna fuskantar juna yayin da ya zuba min wannan manyan idanunsa masu guba yana ta kallona sai kace wani maye ko 'dan saboda shi aka aikoshi.

    "Kamar yadda ya fada miki Ni bana jin French sai kanuri, haussa da kuma English wannan yaren ukun duk wanda kika min magana da shi zan amsa miki In sha Allah "

    "Uhmm" har lokacin ban iya ce masa komai ba 'amma tunda yace yana jin kanuri me zai hana mu yi maganar da kanurin' na fadawa kaina

  "Sunana Idriss Hamza ni ba asalin ɗ'an garin nan bane neman kuɗi wato business ne ya shigo da Ni ƙasar ku har na sinci kaina a wannan gari mai tarin albarka da ni'imomi"

Ya dan sagaita kafin ya daura, yayin da Ni kuma nake ta kada kai awa wata kadangaru wa ina sauran sa da jin abinda ya kawo shi waje na tunda zuwa yanzu na fahimci wani abu

    "Wato kamar yadda nake fada miki ne ina business din canji anan gaba kaɗan da ma'aikatar ku nima office dina yake"

     "Uhmm"

     "Yauwa sannan Ni dan ƙasar Nigeria ne nan cikin jahar Maiduguri kusa da ku kenan"

Ban san lokacin da na zabura na mike ba ina  "Me? me kace? Sai nayi saurin komawa na zauna

'Ɗan Nigeria fa? Ɗan Nigeria kuma ? Ummm ina jin ina ba ɗan mafiya ba ne to 'dan 'yan kan kai ne saboda 'yan Nigeria haka suke' . Ina can maganar zuci yayin da shi kuma yake kallona cikin mamakin abin da yasa ni mikewa tsaye kafin ya ci gaba da fadin

      "Eh abin da kika ji na fada gaskiya ne Ni ɗan asalin ƙasar Nigeria ne sannan duka dangina suna can, sannan zan iya cewa  ɗan Niger ne tun da komai nawa yana nan sannan ina sa ran zan auri yar nan" yana wannan furicin ne yayin da fuskarsa take shinfide da wata irin murmushi sannan ya kafe Ni da ido

Wanda suka shigo tare da shi kamar ya karantar abin da yake zuciya ta ya amsa da "Kamar yanda ya fadamiki ne shi ba dan kasar bane amma ya jima a garin nan sannan zamu iya cewa ya zama ɗan ƙasa kamar yanda ya faɗa yanzu, dan haka ki kwantar da hankalin ki sannan shi abokina ne kuma mutumin kirki ba ina yabansa ba ne ah ah halinsa nake fada miki, Ni kuma sunana Adam wan Aïda ɗan ƙasa kuma haifaffen wannan gari" ya kara sa da murmushi

   'Tabass na san Aïda farin sani ma kuwa tunda mate dina ce sannan mun yi makaranta tare amma ban san wani wan ta mai suna Adam ba'

Kamar yasan abinda yake wakana a zuciya ta ya daura da

    "Lokacin kuna ƙanana na tafi karatu Niamey hakan yasa ba lalle ne ki gane ni ba amma Ni tunda na gan ki na shaida ki, sannan muna tafe ne babban alkhairi wajen ki Zaïya Chérif Boulama"

Nayi saurin daga kai na kalleshi
Shi kuma ya daga min gira tabbacin ya sanni kenan tun da har sunan iyayena ya faɗa
Sai gani ba bakin magana sai nake jin duk sun ta kurani da kallo sai matse hannayena nake cikin junansu

    "Ranki ya dade na zo miki ne da alkhairi kamar yadda babban abokina ya faɗa" ya dan sagaita yana kallona yayin da Ni kuma jin ya yi shiru na dago da kaina dan ganin abin da yasa shi yin shiru daidai lokacin shima yana kallona
idanun mu ya sarke cikin na juna yayin da na ji yayi min kwarjini sosai nan da nan na sadda kaina kasa ina jan gelen dake jikina duk na daburce. Ban an kara ba na ji amon muryarsa yana tashi cikin ƙwaƙwalwata

    "Na zo gareki ne dan neman soyayyar ki da kuma yardar ki, sannan Ni ba da wata mummunar manufa nake sonki ba illa ta auren ki ko yanzu ne Ni a shirye nake. Tarbiyyar ki, nutsuwar ki, kamun kanki... abubuwan da suka ja hankali na a kanki da kodaitamin suna da yawa amma kaɗan daga cikinsu kenan"

Nan da nan naga abokinsa ya mike yana ƙoƙarin fita daga office din ya bar mu mu biyu. Nayi saurin dakatar da shi ta hanyar

    " 'Ya haka ina zaka ne ?"

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant