A rayuwa duk wanda yayi hakuri yayi juriya ga yadda rayuwa ta juya da shi In shaa Allah zai ji dadi kuma a ko wane yanayi ka sinci kanka ka zamo me godiya ga mahaliccin ka da yawaita addu'o'i da zikhirai da karatun Alqur'ani mai girman In shaa Allah komai zai zo maka da sauki kuma ya wuce cikin gaggawa saboda karfin ayoyin Allah da kake ambato.
Kamar dai ni Zayya wacce Allah ya jarabceni da kalubalen rayuwa daban-daban wanda a ciki harda na rashin samun cikakken kwanciyar hankali na yin bacci sakamakon mummunar mafarkin da neke wanda hakan ya haddasa kullum ina cikin firgici da tsoro na rashin sanin abin da zan tarar in na kwanta barci hakan yasa har ya kai ga bana son kwanciya.
Ga rashin samun BAC da kuma maganganun da Zayyan yayi min su wanda hakan yasa na dan janye da shi, abubuwa ne duk sun dabaibaye ni, na rasa kwanciyar hankali da na zuciya baki daya na rasa mece ce mafita a yanzu gashi dai ban daina addu'a ba, amma al'amurra ta sai kara tabar-barewa suke min. Iyaye da yan uwa suna bakin ƙoƙarin su wajen faranta min amma zuciya taki bani daman hakan.
Sannan hakan bai hana ni samun makiya da ma hassada ba daga gefe na wanda ni ban san da zaman su ba amma wanda sun suka san da tawa.Rayuwa ta a yanzu gaskiya ya banbanta sosai da wacce nayi a baya wanda nake cikin kwanciyar hankali, natsuwa da farin ciki, ko yaushe zanyi bacci cike da nishadi na farka cikin nishadi babu wata fargaba duk wannan babu shi yanzu.
Duk wani wanda ya sanni a da yanzu ba zai taɓa cewa wannan Ayahn Zayyan ce ba saboda na rame sosai abinci ma sai anyi da gaske.
Hakan yasa nayi wa Tanti maganar komawa ta gida walaAllah ganin iyayena da yan uwana kusa da ni zai sa na rage yawan tunanin da nake, sannan zai bani daman nisanta da MZ ta yanda zuciyata zata samu sassauci daga abin da nake ji daga gare ta...
Bayan mun sha tafiya da gajiya da zaman mota Allah cikin ikon sa na sauka gidan mu cikin iyayena da yan uwana lafiya. Bayan nayi wanka da ruwan dumi dan sosai a gaje nake amma bayan wankan na dan wartsake sosai. Na shirya cikin kaya mara nauyi sosai na zuba turare na shigo dakin Maah bakina da sallama na sake gaishe ta ita ma ta yi min ban gajiya da hanya nan muka dasa yar hira nida ita ita, muna cikin hirar ne take nuna min da yanzu lokaci ya yi da yakamata na bawa MZ dama ya fito hakanan ya isa tunda yanzu ya kamata ace nima nayi aure kamar ko wacce mace tunda karatun Allah baisa na samu abinda nake nema ba, yakamata yanzu na karkata aure.
"In sha Allahu".
Shine abin da na iya cewa dan ni dai a yanzu ban san ta inda zan fara ce musu ga yanda mukayi da MZ ba. Nan nayi saurin mikewa nace da ita zan shiga gidansu Sadiya.
" Dama kince musu kina hanya ne?"
" Ah ah ban fadawa kowa ba, zan musu ba zata ne kawai saidai su ganni"
" Kenan dai baki gaji ba. Ki gaishe su!"
SADIYA
Ina kitchen ina dafa mana abincin dare wajen biyar na yamma sai ji nayi ihu da maganar Zaïya ta na cewa
" Kunaaa ina! ku fito labari da dumi-duminsa"
Cikin mamaki na jin muryarta saboda bata gaya mana ba tana hanya ba kuma dama mun saba idan muna da labari wa juna sai an shelanta kafin a fada sannan ayi ta jan rai sai an baki abin motsa baki kafin ki fadi labari hhh (shiriritar iri-iri ce idan na tuna da wannan irin moment din na kan yi dariya me hade da hawaye meyasa na zama silar komai)
ina jin muryarta da hanzari na fito in cewa...
amma me?kafin nayi maganar sai naga abin mamakin ganin ibou rungume da ita ya riga mu tarban ta yana ta wangale mata baki yana dariya kamar ba shi ne tun dazu muke mai magana yaki kulamu ba wannan soyayyar tasu daga Allah ne da kuma yadda Zaïya take nuna mai kulawa sosai yanzu haka tana cilla shi sama tana cabewa yana ta dariya harda kylkyalewa.
VOUS LISEZ
DAGA MAKWABTAKA
Non-FictionInna lillahi wa Inna lillahiraj'un abin da yawancin mutanen dake gurin suke fada kenan duk inda ka ƙalla sai dai kaga bakin kowa na motsi bi ma'ana kowa da abin da yake fada kenan... Mutane kewaye da ita kowa idanunsa cike da hawaye hanci sai zuba r...