Cikin zumudi farin ciki da murna yau na wayi gari safiyar juma'a saboda sanin cewa yau ne ranar da CEO yace naje zai yi min entretien d'embauche (job interview) sannan ina kyautata zato za'a dauke Ni. Sabar farin cikin da nake ciki yasa yau ban bi ta kan munanan mafarki na ba ba wai dan ban yi ba a'a sai dan tsawun Giwa ya take na raƙumi. Bayan nayi wanka na daura arwallah (yana cikin abin da Abba ya koyar da mu, mu kasance kullum cikin arwallah ba sai zamu yi sallah ba hakan yasa wasu lokuta kullum nake cikin arwallah balle idan na san cewa zan fita) na je na shirya cikin riga da skirt ta atamfa kalar ja da baki daidai jikina ma'ana bai yi matseni ba, na shafa yar poda da man baki kawai sannan na sa wa idona farin kwalli irin wanda ake sa wa jarirai kasancewa ta mai larurar ido yasa bana sa kwallin zamani sai irin wannan kafin na fesa jikina da turaruka masu dadin kamshin da sanyi na dau gele da takalma kalar baki kasancewar bakin tafi kaɗan a jikin kayana na ɗauki wayata na nufi dakin Maa kasancewar Ni ba ma'abociyar son ɗauka jaka bace yasa ban ma wai wayi inda nake tanadar su ba duk da ma ba wani abun a zo a gani ne da Ni ba.
"Yau dai kin yi abun kai, har kin shirya ke nan?"
Cikin dariya da sunkuyar da kai ina wasa da gelen da na yafa na ce "Eh Maa na yi sauri ko?".
"Kin yi wani abu dai tunda takwas din saura kadan, ji irin sammako da kika yi amma bai hana kije a makare wajen ba"
Cikin shagwaba ina bubbuga kafa a kasa nace
"Kai Maa duk kokari da nayi wajen ganin na shirya da wuri amma ba za'a yaba min ba"Cikin murmushi mai burge wa da sanyaya zuciyar wanda yake tare da ita kuma mai sauraro ta ce
"Ai na yaba miki sanin cewa ke din mai nawa ce amma ga wanda bai san ki ba cewa zai yi kin kashe lokaci sosai tunda tun shida kika tashi kina abu guda sai yanzu fin bakwai kika gama. Yanzu dai hanzarta kije kar ki ƙara jan lokaci. Allah ya baki sa'a idan alkhairi ne ga kowa ya tsare min ke sannan ya shiga cikin al'amurran ki.""Aameen ya Rabbi In sha Allah ba zan makaraba wajen isa office din"
"Allah yasa! Allah ya yi muku albarka!"
"Aameen! Abba fa bai tashi bane (cikin shagwaba tayi tambayar)"
"Ina jin ya tashi , je ki gani"
"To Maa daga wajen shi zan wuce, sai na dawo"
"Ga shi kuma baki karya ba haka zaki fita?"
"Ni gaskiya ko na tsaya ba zan iya karyawa ba saboda ji na nake a koshe"
"Tsabar kina zumudi dai, ban da haka me kika ci da zai sa ki ji ki a kashe... Allah ya shirya min ke"
"Kai Maa kamar ko kin sani Allah Allah nake na gan ni a can"
"Kar ki manta Ni fa na haife ki. Maza je ki tunda magana bata wuce ki"
Na yi mata sallama na shiga wajen Abba na taras yana kishingide yana lazimi shima nayi masa sallama ina zolayar sa irin ta y'a da mahaifin ta
"Abbana ni ake rokawa Allah ko"
"Eh mana yar Abba ai duk addu'ar mu kullum ku muke wa."
"Ayya Abba har kasa naji hawaye sun taru a idon zuciya ta yanzu Abba kullum tashin da kake cikin dare kana ta sallah dama saboda mu ne?"
"Eh mana saboda ku da maman ku dan ba wanda ya fi min ku. Sannan na yi wa iyayena da suke kwance kasa da al'ummar musulmi da kai na"
"To Abba me yasa sai a karshe kake wa kan ka?"
"Saboda hakan yakamata duk mai addu'a muminai ya yi sai ka rokawa al'umma sannan ka rokawa kan ka kuma ke ma haka nake son ki ringa yi"
"Hum Abba kamar ko ka sani sai na fara yiwa kai na sannan na yi muku da Maa sai na yi wa kannaina shi kenan"
"A'a son kan ya yi wa, ke nan baki ma al'ummar musulmi da waɗanda suka riga mu gidan gaskiya?. To daga yau kisa har da su kin ji"
"To Abba In sha Allah zan sa har su." Yayin da nake ƙoƙarin barin dakin sa
"Allah ya bada sa'a yasa albarka cikin neman ki ya yaye miki duk wani damuwa yasa ku zamto masu share mana hawaye"
"Ameen Abba In shaa Allah idan na samu aikin nan har Makka sai na kai ku kai da Maa".
Bayan na gama saka takalma na na yi gaba ban tsaya jin amsa ba saboda naga fitowar Maa kuma dakin Abba za ta zo sannan sanin kai na ne sai tace har lokacin ban bar gidan nan ba. Hakan yasa ban jira sai ta yi magana ba na yi sauri sauri gudu gudu na fita a gida. Bayan na samu abun hawa ban saya ko ina ba sai kamfanin.
VOUS LISEZ
DAGA MAKWABTAKA
Non-FictionInna lillahi wa Inna lillahiraj'un abin da yawancin mutanen dake gurin suke fada kenan duk inda ka ƙalla sai dai kaga bakin kowa na motsi bi ma'ana kowa da abin da yake fada kenan... Mutane kewaye da ita kowa idanunsa cike da hawaye hanci sai zuba r...