DGM14

12 1 0
                                    

A yayin da kalubalen rayuwa ya tsananta, hassada, ƙiyayya, rashin aminci da zaman lafiya ke ƙara yawaita a ɓangarori daban-daban na rayuwar mu kada muyi sakaci da zikhirai na safiya da yamma komai zai saukaka garemu In shaa ALLAH.

Yawaitar addu'o'i da zikhirai yasa ni Zaïya Cherif Boulama Allah ya yaye mini sannan ya saukaka min da yawa daga cikin kunci da damuwa da nake ciki. Sosai na yi jinyar zuciyata kafin Allah ya sauka-kamin.

Yayin da MZ ya kira ni washegari bayan da mukayi waya da souley yayi ta bani baƙi akan wallahi shi ko yanzu indai na aminci a shirye yaƙe da ya aure ni.
Ni kuma na nuna masa sam bazan kasance ta biyu a cikin gidan sa ba yayin da ya yi min alkawarin shi kuma ba wata macce da zata shiga cikin gidan da ya gina saboda da Ni dole sai Ni din kuma sai ya aure ni In sha Allah

"Mon amour yanzu saboda kina cikin fushi kike fadin haƙa amma Ni ne mijin In sha Allah nan duniya har ma da lahira"

"In ana auren dole ai sai ka aure Ni din mu gani" cikin tsiwa

"Sha nawa akayi auren dole kuma aka zauna, bare ni da ke muna son junanmu sannan wannan a bunda ya faru tana cikin ƙaddarar mu ce "

"Ƙaddarar ka dai malam banda nawa"

"Haba tawa ban san ki da riko ba da kuma irin wannan fushin"

"Yau ai ka sani, sannan ba zan taba auren ka ba in ka ga dama kasa mata biyar a gidan ba ruwana bane"

"In sha Allah wannan gidan mallakin ki ne"

"Ta ya kake tunanin zan aure ka bayan na ji dangin ka suna iƙirarin na mallake ka tun ban aure ka ba ina sai abin da na fada kake yi.
Ina ga mun yi aure sun rasa ka kenan sannan yana cikin abinda yasa suka baka auren wannan ɗin da suke ganin sun fi kusanci da ita sannan aka saka ƙurarren lokaci gudun kar na na lalata kamar na baya a cewar su. 'Dan su gani suke wancan lokaci da baka auri yar uwar ka Hauwa Ni ce nayi sila shi yasa wannan suka hana ka faɗa mini
ka na tunanin maganganun su baya zo min ne?"

"Dan Allah ki bar wannan shirmen mon amour"

"Shirme ne ma kenan?"

"Yo ban da shirme ai ni kika mallaka ba wani ba su ba, sannan ina sonki ina ruwan ki da maganganun su. Wallahi yarinyar nan ba sonta nake ba sannan ita da kanta tasan da haƙa"

"To na ji zan yi tunani a kai" na fadi haka ne saboda na rabu da shi dan na gaji da wannan magiyar ta sa

"Yau Ni kike cewa sai kin yi tunani chouchou"

"Ummm"

Shiru ya rasa sakaninmu ba wanda ya kuma magana, can na gaji da rike waya a kunne na kashe na shiga harkar gabana.

Shi kuma tun lokacin ya kara damarar bani wata kulawa ta musamman akan wanda yake miki.

Lokaci da labari ya risƙe ki kawayena sun ji ba dadi sosai sannan sun so na amince masa a zuwan ta biyu amma na nuna musu sam banda gidan Zayyan zan iya tafiya a zaman ta biyu gidan ko wane na miji amma banda shi. Suka nuna min dan ina cikin fushi ne amma zan amince ne nan ba jimawa ba saboda irin soyayyar da mukayi da shi ba irin ta rabuwa ɓace ba tare da aure ba.
Nima na nuna musu komai daga Allah ne sannan hakan zai yi iya yiyuwa idan Allah ya ƙaddara da min
Sannan yanzu ma haƙa Allah ya ƙaddara min dole na rungumi kaddamar ta na godewa Allah.

Ina cikin wannan hali na rashin sa'an rayuwa (a cewa ta kenan) Allah ya bude min ɗaya daga cikin kofofin sa na Rahama in da na samu kira cewa an ɗauki Ni aiki cikin mu ukun da muka yi interview. Na yi murna sosai a lokaci da wannan albishir ya risƙeni kai hatta duk
wani ma'kusancina yayi min murna ya tayani jin dadi sannan Ni ma a karan kaina na yi wa kai na murna ko ba komai damuwa zata rage min zan yi sabbin abokai sannan zan kasance kullum cikin mu'amala da mutane daban-daban saɓanin yanzu da nake kullum cikin daki daga kwanciya sai kwanciya da yawan tunani.

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant