DGM 24

4 2 0
                                    

<< WAJEN 'YAN SANDA >>

Ya yi y'an rubuce-rubuce ya daga kai ya gama kallon su daya bayan daya ya dawo da kallon sa kan Ali kafin ya dakatar da rubutun ya fara da faɗ'in

"Me ku ke son ayi muku kenan? Bayan an kashe magana tuntuni"

"Maganar gaskiya magana ta mutu ne a inda aka kashe shi"

DPO ya kura masa ido yana kallon sa cikin mamaki, me ya ke nufi da ya mutu ne a inda aka kashe shi, ke nan a wajensa har yanzu maganar tana raye.

Ya ci gaba da fadin
"Sarki ya kashe wancan maganar, Ni yanzu na shigar da kara ne kan neman kashe min mata da y'arsu ta yi yunkurin yi dan har cikin gidana suka shigo da ita dan kawai kashe min mata"
Ya kai aya yana kallon Abba da Dpo wanda suka sura masa ido suke saurasron sa yayinda Abba yake cike da mamaki da al'ajabi, daga makwabtaka sai mutum ya bibiyesu da sharri daga an gama wannan case ya fito da wata kawai dan baya son ganin su cikin farin ciki, me ya canza Ali ne sanin da ya masa ba haka yake ba, ko da yake dama baka taba sanin masoyi da makiyi ko mutumin kirki sai wani abu ya hada ku ko wani ciwo ya taso maka.

Nan da nan maah dake zaune opposite da shi ta yi saurin daga kai ta ka yi duban ta ga mai maganar,
Tuni ta daina mamakin abin da Ali zai aikata saboda ya shayar da ita da manyan abubuwa na ban mamaki tun faruwar wannan kaddarar wanda yasa yanzu sam bata mamaki ga duk wani abu da zai bullo musu dan kawai a kulle su a cell, burin sa kenan.

Ita yanzu lamarin Ali ya daina bata mamaki sam-sam sai dai tace ko dama yana kullace da su ne? wai an yi yunkurin kashe masa mata, lalle mutumin nan neman mu suke da sharri bilhakki...

'Wai neman kashe masa mata! Kashe masa mata fah? Allah ka raba mu da kashe rai. Da gaske dai karar da ya shigar a kan mu kenan dama, duk gudu na da abinda ya shafi hukuma sai da mutanen nan sukai silar kawo mu wajen nan sannan hakan bai ishe su ba suka kara da wai mun nemi kashe masa mata. Da farko yace mun lakabama matarsa sharrin maita yanzu kuma yace mun nemi kashe masa mata. Ban taba da-na-sanin haduwa ta da bayin Allahn nan kamar yau ba.
Tunda nake a rayuwata ban taba zuwa na tsaya a station ba da sunan shari'a amma yau an wayi gari anyi karar mu ance mun yi laifi bayan mu aka cuta aka zalunta. Gamu zaune muna amsa tambayoyin da wai ake zargin mu da shi na kashe matar makwabcin mu wanda nake musu kallon yan uwana kuma kannena. Ba komai laifin Zaïya ce duk ita ta ja mana da bata....sai tayi saurin fadin Astagfirllah tuff tuff Allah na tuba kaddara ce'

Ali ba abin da yake so ya gani kamar an kule iyayen Zaiyah a cell na wani lokaci hakan ne kaɗai zai sa zuciyar sa dadi. Saboda yasan ko ba komai an hukunta su sannan sun kwana cikin cell mai cike da zarnin fitsari da wari.

Maganar Dpo ne ya dawo da Maa cikin tunani da ta lula

"kun dai ji abinda suke tuhumar ku a kai, me zaku ce?

Abba ya yi murmushi irin ta manya cikin kwanciyar hankali ya amsa masa
"Gaskiya mu dai ba mu da masaniyar wannan maganar saboda ba mu san wanda ya nemi kashe masa mata sai yanzu da muke ji. Amma tun da sun ce mu suke tuhuma a tambaye shi da wane irin makami ko kuma ta wacce hanya muka shiga gidansa wajen yunkurin kashe masa mata kamar yadda ya furta.
Ina ce wannan ita ce matar tasa (ya nuna Sadiya da hannu) ta ya wanda aka nemi kashe ta take nan zaune cikin koshin lafiya?"

DPO ya juya duban shi ga Ali yace
"Kai muke sauraro, kace sun nemi kashe maga mata! to cikin su wane ya nemi kashe maka matar, ko dukkan su ne? Sannan da me suka nemi kashe ta ina kuma shedar inda aka illata ta din?"

Cikin in-ina ya fara fad'in
"Umm... um... Yallaabaii..... daa..daaama....ayi cewa na yi yarinyar su...ba ...wai nace... su ba..."

DPO ya buga table cikin ɓacin rai yace
"karka nemi raina mana hankali mana! Kasan ba su bane kuma kai karar su, da kazo sunan wa ka ambata?

DAGA MAKWABTAKA Où les histoires vivent. Découvrez maintenant