©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
💜💜
💜💜💜💜💜💜
💜💜👫
Naɖaʍaʀ Aʊʀɛռa.
Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.
Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ .
Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
Bɨsʍɨʟʟaɦɨʀ Raɦaʍaռɨʀ Raɦɨʍ
0⃣1⃣
Kwankwasa kofar yake ba kakkautawa kamar wanda yayi aiki ba'a biyasa hakkinsa ba daga ciki aka tambaya
"waye?"
"Bude ka gani"na wajen ya amsa,
shiko na cikin dake kokarin kai matarsa bathroom kasancewarta amaryar da aka kawo jiya, jin muryar mahaifinsa yasa ya zaunar da ita ya fita parlor ya bude ma mahaifinsa ba tare da ya kauce daga kofar ba.
"Ya aҡaʏɨ baba"
"Uhnm lfy lau Majeed ya kwanan dadi?"
"Baba wai dan Allah yaushe zaka canja hali ne? kana magana kamar yaro"
"Toh naji ni dai ba ma wannan ya kawoni ba kazar amarcin da kuka rage zaka ban yau da muguwar yunwa na tashi"
ya karashe yana hamma,
yarinya yar shekara 16 dake wanke2 nesa kadan dasu tace
"haba baba idan da kana irin haka yanzu ya kamata ka daina tunda kayi surika"
" rufe min baki sakarya kin fini sanin abunda ya dace ne?"
"Allah ya baka hkr" ta fada tana me maida hankalinta akan wanke2.
sai alokacin Majeed yayi magana
"ban gane in dauko maka kazar amarcin da muka rage ba kai angone ko amarya?"
"Ah lallai ashe gaskiyane aure kan sauya mutum yau har ina fada kana musawa lallai wannan yarinyar ba za'ayi abun arziki dake ba ada in Majeed ya siyo kaza damu yake ci amma jiya kuka kunshe ku kadai"
"Karka damu indan nama ne zan siyo maka baba" Majeed ya fada."Toh ina jira, ina ita amaryar me take da suna Zaynah ko?"
"Eh baba"
"Ta fito ta muna abun kari kafin in dawo daga gidan magajiya"
"Toh adawo lfy" cewar Majeed, sai da yaga ficewar baban nasu sannan ya kira kanwarshi dake wanke2"
"Ke Safina zo nan" da sauri ta karasa wurinsa
" Ina Sajida?"
"Tana daki tana bacci"
"Bacci har karfe tara bayan tasan akwai bakuwa? hanzarta ki tada ita kice ta soya kwai ta dora ruwan tea taba Idris 1k ya siyo bread cikin kudin dake hannunta"
"Toh yaya" ta nufi dakin nasu dan isar da sako*
Nasu dakin ya shige wanda ya kunshi bedroom daya da parlor daya sai toilet dake a bedroom in, kitchen ko a waje yake.
Yana shiga ya tarar har Zaynah ta idar da sallah sai dai har yanzu tana kan sallayar bisa ga dukkan alamu tayi zurfi a cikin tunani,
"Zaynah" Majeed ya kirata a hankali amma bata ji ba
"Zaynah fa" firgigit ta kalleshi dan wannan karan da karfi ya kirata
"Zo nan" ya fada yana mata nuni da kusa dashi
Ba musu taje,rungumeta yayi sannan yace
"Ba inda ke miki ciwo?"
"Eh" ta amsa a takaice, basuji sallama ba sai ganin mutum sukayi a firgice Idris ne yana haki yace
"Yaya Majeed baba da Musa ke fada a gidan magajiya"
"Subhannallah meya hadasu yau kuma?"
"Babane ya ari kudinsa yayi caca aka cinyesa ya rasa kudin biyansa"
Majeed yayi dana sanin tambayar da yayi dan abun kunya ne matarka tasan babanka mutumin banza ne.
Ita kuwa nanata kalmar caca kawai take a ranta, sakinta Majeed yayi yace ina zuwa suka fita da Idris.
Dora hannu tayi akai tana mai fadin
"oh ni Zaynah wani irin gida na fado?" Ta tambayi kanta ba dan ta samu amsa ba.
Ni kuwa Hussaina dake a gefe da iyayina nace bari kiji.
***
Gidan Buba tsohon soja gida ne da yake dauke da dakuna hudu wanda biyu da bedroom da parlor da toilet biyu kuma daki ne da toilet,
Suna zaune a Birnin kebbi, kebbi state a unguwa mai suna rafin Atiku.
Yahanasu itace matar Buba ta rasu tun lokacin haihuwar Safina,
Gidane da ba tarbiya ko kadan kafin rasuwar Yahanasu tana kokari dan ganin ta saita yaran amma abun yaci tira.
Majeed shine dansu na farko sai Idris sannan Sajida da kuma autarsu Safina,Majeed ke dauke da dukkan laluran gidansu dan babansu kurtu ne a soja kuma korarshi akayi ba retire yayi ba
Majeed lecturer ne a Federal University Birnin Kebbi dake a kalgo
Kasancewar ba nisa tsakanin kalgo da birnin kebbi yasa a kullum yakan je ya dawo.
Idris kuwa ya fara karatun diploma a Waziri Umaru polytechnic yana karanta political science sai dai sam karatu ba tsarinsa bane yafi son harkar party da bin yan iskan gari a yanzu haka an koreshi,
Sajida kuwa shekararta daya da gama secondary
Majeed yace ta fidda miji aure zai mata sai dai batada kamun kan da za'a zo nemar aurenta sai abokan shashancinta.
Safina a yanzu tana ss2 ba laifi tanada hazaka duk cikin gida daga ita sai Majeed ne masu lfy dan su basa rashin ji sai dai suma ba tarbiyanne dasu ba suna iya gayama babba magana san ransu.
Gidan Buba nanaye gidane da suke son junansu sosai.
Buba nanaye yana caca da kuma shan giya abunda ke kaisa gidan magajiya kenan amma baya harkan mata.
Majeed yana da kimanin shekaru 30 a yanzu mutum ne miskili na gaske.
Shi kadai ne kannensa basu raina ba amma babansu bai ma isa ya tsawatar musu ba dan shima yana bukatar mai yi masa fada.
Hʊssռaɦ~ʊɮaռɖɨʏa.
YOU ARE READING
NADAMAR AURENA
RandomZaynah kuwa kasa daurewa tayi a yau kuka kawai ta keyi tana fadin innalillahi wa'innah illaihir rajiun, dame zata ji? da baqin cikin da ta gano gidan tsohon saurayinta wanda yake mijin yayarta a yanzu? ko da baqin cikin ganin surikinta akan gadonta...