©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
💜💜
💜💜💜💜💜💜
💜💜👫
Naɖaʍaʀ Aʊʀɛռa.
Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.
Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
_I_ _want_ _2_ _wish_ _an_ _anniversary_ _day_ _2_ _a_ _couple_ _who_ _is_ _beautiful_ _in_ _entire_ _land_. _May_ _ur_ _anniversary_ _enhance_ _ur_ _luv_ _&_ _understanding_. _Once_ _again_ ɦaքքʏ ~aռռɨʋɛʀsaʀʏ~ Fatʏ Aҳɭaŋɖ (Aųŋŧყ 'ყąř MıŧŞıٳą).
0⃣6⃣
Majeed ne da Zaynah kwance a saman gado kowannensu yayi shirin bacci Zaynah ce ta taba kan Majeed tace.
"Dear na"
"Uhnm meye kuma Zaynah bacci fa nake ji" ya fada idonshi a rufe.
"Dama Ummie ke sanar dani daxu dana je take cemin wai Anty Salma ba lfy"
"Akan Salma ba lfy zaki hanani bacci toh naji Allah bata lfy shikenan abunda kike son kiji nace koh?"
"Eh sai kuma batun zuwa in duba ta"
Ba shiri Majeed ya miqe zaune yana kallonta sannan yace.
"Meyasa baki abu da tunani ne? from Monday to Friday fita kike aiki yau Saturday kin fita kuma kina expecting ki fita gobe?"
"Haba dear karka manta Anty Salma yar uwata ce uwa daya uba daya a ganinka ya dace tayi ciwo banje na duba lfyarta ba?"
"In dai har nike da iko dake ba inda zaki ki bari next week kin tafi"
Nan dai ta hau shi da magiya da roqo har ya yarda zata je amma inta gama girkin dare datayi mai complain cewa bata tukin dare yace ya kaita saman rubber rubber insa.
Har ya juya zai kwanta ta sake riqo hannunsa."Dear" ta fada kamar mai shirin kuka.
"Meye kuma wahalarki tayi yawa Zaynah kin fiye damuwa me kike so kuma?" Ya tambaya a hasale.
"Dear nace ba ko inyi ma Ummiena mgn ta bani mai tayani aiki cikin yan aikinta?"
Da mamaki ya kalleta yace " yan aiki a gidan nan? A ina kike so ta zauna? Bayan ma haka ni bazan iya biya ba sanin kanki ne inada lallurori a kaina.
Riqo hannunsa tayi "dear bafa anan zata zauna ba za'a kawota 6:30am ta koma 2:pm sannan Ummiena zata biya ba kai ba"
"Ke dai Zaynah Allah yayiki da karancin tunani mahaifiyarki ce zata biya muna kudin yar aiki salon ta rainani koh?"
"Haba dear kasan yadda zakayi mgn mana mahaifiyatace zata rainaka""Toh koya min yadda zanyi mgn mahaifiyarki mahaifiyata ne?"
"Koda yake nima meye abun damuwa tunda ko naka baka girmamawa" ta fada tare da dauka pillow ta nufi parlor,
Bai ce da ita komai ba illah rufe ido da yayi yana son bacci ya daukesa, ko kadan mgnarta bata bashi haushi ba.
Zaynah kuwa a parlor tunanin abubuwan da suka faru kafin aurenta da Majeed kawai ta hau yi.
***
Washegari kamar yanda yayi mata alkawari bayan sallar isha'i yace ta shirya.
Cikin minti 15 suka dauki hanyar gidan Anty Salma dake a G.R.A.
Suna isa Majeed yayi parking rubber rubber insa a wajen gate din gidan yace da ita.
"Sauka"
"Ban gane in sauka ba ba ciki zaka shiga da mashin inba ko waje zaka barshi?"
"Dani da mashin ina ba me shiga gidannan"
"Sbd me dear, bazaka shiga ka gaida yayata ba?"
"Bakida hankali Zaynah da har kike tunanin zan shiga gidan Rayyan? kedai da yazama miki dole kishiga kuma 10mnts kawai na baki idan kika wuce haka karki fito ki kwana a can kawai"
"Toh" kawai tace ta fara tafiya kamar wacce kwai ya fashe ma a ciki.
Da sallama ta shiga parlorn sai dai mutanen dake a parlorn sun shagala basuji taba.
Idonta yayo mata mugun gani dan kuwa Rayyan ne zaune a kasa bayansa jingine da cushion yayinda ya mike kafarsa Salmah na a tsakiya kafafunsa duka jikinta na a jikinshi hanunshi riqe da bowl wanda cornflakes ne aciki yana feeding Salmah ita kuma sai zuba mishi shagwaba take.
"Assalamu'allaikum" ta daure ta kara fada da karfi.
Sai a wannan karan suka ji sallamar, Rayyan kadai ya iya amsata ita kuwa Salma kunya ya rufeta sai kokarin barin jikinshi take yi amma ya hana.
Dakyar kafafun Zaynah suka iya daukarta har ta karisa ta zauna.
Suka gaigaisa ta ma Salmah ya jiki ta dora da fadin "sai da safenku Allah ya kara sauki Anty" ta fada tare da mikewa.
"Cwt sis ko minti biyar bakiyi ba zaki tafi?" Salmah ta fada a marairaice.
"Eh tare da Majeed muke kuma yanada uziri shiyasa, Allah dai ya kara sauki"
"Ameen amma Allah ya inganta zakice auta" Rayyan ya fada fuskarshi dauke da murmushi.
Da hanzari Zaynah ta fita daga parlor ta nufi gate.
A ciki kuwa Salmah ce ta kai ma Rayyan dukan wasa a kirji tana fadin.
"Me kenan kayi yaya nasan dan kaba cwt sis haushi kaqi barin intashi daga jikinka kuma ka fada mata cikine dani koh?"
" eh cwt Honey kuma naci nasara ba tunda gashi ta kasa zama ganin yadda muke sannan jin nace tace Allah ya inganta yasa ta fice kamar me shirin tashi sama" ya fada yana dariya itama Salmahn dariya tayi tace.
"Toh ai yaya ba ganinmu haka yasa ta kasa zama ba kasan iyakar wanda sukeyi da Majeed? Ciki kuma maybe itama tanada shi"
"Waya fada miki Majeed ya iya soyayyar da har zai nuna ma auta hmm kedai abar maganan kawai, na yarda da akace wani hanin ga Allah baiwa ne, ngd ma Allah daya hanamin Zaynah ya bani Salmah"
"Uhnm" kawai Salmah ta fada.
A waje kuwa............
Hʊssռaɦ~ʊɮaռɖɨʏa.
VOCÊ ESTÁ LENDO
NADAMAR AURENA
DiversosZaynah kuwa kasa daurewa tayi a yau kuka kawai ta keyi tana fadin innalillahi wa'innah illaihir rajiun, dame zata ji? da baqin cikin da ta gano gidan tsohon saurayinta wanda yake mijin yayarta a yanzu? ko da baqin cikin ganin surikinta akan gadonta...