08

1.1K 69 4
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

      Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

   Wattpad@Mss Hussaynah.

  _The_ _smallest_ _act_ _of_ _kindness_ _is_ _worth_ _more_ _than_ _d_ _grandest_ _intention_ _tnkx_ _4_ _helping_ _en_ _supporting_ _me_ _always_ *Anty* *Ummie* *Jafar* *en* *Anty* *Aina'u* *(* *dimples* *)* *ur* *aids* *2* *me* *are* *unlimited*. *dis* *page* *goes* *2* *u*.

            0⃣8⃣

     Bari mu fara da asalin Zaynah sannan tushen labari.

    Alh.Suleiman shine mai garin dakin gari,yanada mata uku Hindatu da ake kira da Iya itace matarshi ta farko da sukayi auren saurayi da budurwa 'yace ga kanin mahaifinsa,

   'ya'yansu bakwai da maigari Suleiman amma a yanzu daya kawai ke raye Ahmad Rufa'i, sai matarsa ta biyu Halima suna kiranta da gwaggo danta daya Habib wanda yanada shekara uku kacal ta koma ga mahalicinta sai aka bama Iya riqonsa.

  Wadda ta riqeshi tamkar dan data haifa,shekaru bakwai ne a tsakanin Ahmad Rufa'i da Habib.

  Sun taso a cikin so da kaunar junan su, a lokacin da Habib keda shekara biyar mahaifinsu ya auro wata bazawara da mijinta ya rasu ya barta da ciki,

   Haihuwarta da shekara daya ta tare a gidan maigari.

    Zaman Iya da Inna Salame zamane na lfy tare da girmama juna.

   Bayan kammala primary school din Ahmad Rufa'i anan dakin gari, sai aka kaishi boarding school a birnin yauri (F.G.C) domin samun ingantaccen ilmi.

  Ahmad Rufa'i yana s.s2 aka kai Habib, bayan Rufa'i ya kammala secondary school ya tafi B.u.k inda yayi obtaining degree dinsa a political science.

   A lokacin daya dawo ya tarar har an sanya ranar aurensa da 'yar aminin mahaifinsa Fatima, yarinya fara soul kyakyawa ga diri.

   Bai musa ba ya karbi auren hannu bibbiyu,ba tare da bata lkc ba mai gari ya tura wakilai garin birnin kebbi aka gina musu gida wanda ke dauke da part biyu na Ahmad da na Habib.

  Sai da Fatima tayi haihuwa biyu ta haifi Beelkisu da Amina, shekarar Beelkisu hudu Amina biyu, a lkcn Habib ya auri Rasheeda (diyar inna Salame)

   Suka zauna a part dinsu, maigari ya bama Habib jari kasancewar business administration ya karanta, cikin ikon Allah ya fara kasuwancin sayarda turamen zani da mayafayya Allah kuwa yasa ma abun albarka.

   Ahmad da Habib suka yanke shawarar sanya matayensu a jami'a tunda sunyi secondary already, da suka gayama mai gari yayi na'am da zancen, sukayi karatun likitanci.

  Lkc daya Fatima da Rasheeda suka samu ciki wanda na ukun Fatima kenan, na farkon Rasheeda,

  Bayan wata tara Rasheeda ta haifi danta namiji mai suna Rayyan a ranar sunan Fatima ta kara haihuwar 'yarta mace Hafsat.

  Daga lkcn Fatima bata kara haihuwa ba sai Rasheeda data haifi 'yan biyunta duka maza Hassan da Hussein.

  Ahmad yayi contesting a chairman kuma ya samu, 'yan biyu nada shekara uku Fatima ta kara haihuwar mace mai suna Salmah, kowa yayi mamaki dan shekararta shidda rabonta da haihuwa duk an dauka Hafsat ce auta sai ga Salma, ba'a fi wata biyu da haihuwar Salmah ba Fatima da Rasheeda suka fara aiki a cikakun likitoci a general hospital na birnin kebbi, Fatima Gynecologist Rasheeda dentist.

  Shekara biyu tsakani ta haifi Zaynah wacce itace autarta ita kuma Rasheeda 'yan biyu ne autanta.

  Tsakanin iyalan yan uwan biyu akwai kyakyawar fahimta da qaunar juna da kara.

Ba maganar wannan ne nawa wannan ba nawa ba, dan exchanging ma sukayi Rayyan na wurin Fatima da suke kira da Ummie, Hafsat na wurin Mamie (Rasheeda).

  Sunyi hakanne dan daya batada mace daya batada namiji.

****

   Zan fara lbrn ne a lkcn da Rayyan keda shekaru 22 wato yana university 200l Zaynah nada shekaru 12 tana a jss 2.

   NB. Garin dakin gari garin fulanin asaline.

Nasan page dinnan yayi kadan amma kuyi hkr dashi pls.

Hʊssaɨռa  ʊɮaռɖɨʏa.

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now