38-40

847 54 1
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

      Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

  *MssHussaynah@wattpad.*

   
     *A duk lkcn da na d'auki wayana da niyyar typing nakan tuna dake nakan tuna lkcn da muke karanta novel d'in da kika rubuta a buk nayi matuk'ar kewanki zan kuma so naji daga garek.Dan Allah 'yan birnin kebbi inda wacce tasan Amina Umar Faruk wacce tayi graduating a F.G.C. Birnin yauri 2014, fara bafulatana, pls tayi contacting d'ina ga no.na 08133268581, sannan ku tayani sharing a groups naku.*     

     3⃣8⃣ ➡ 4⃣0⃣

     
      *_Bayan sati uku_*

     

         A yau Baffa zai dawo,kuma a yau Zaynah ta gama exams.

    Su Anty Amina,Anty Beelki da Anty Hafsat duk sun iso.

    Bayan Zaynah ta dawo daga skul taci abinci tayi wanka, sai ta sauko xuwa parlor inda Ummie da sauran yayanninta ke jiranta.

      Samun wuri tayi ta zauna tare da fadin "gani"

     Tambayarta ya exams sukayi sannan suka d'ora dayi mata Allah ya bada sa'a.

    Anty Amina ce tace "Zaynah,Ummie ta fadi mana duk abunda kenan, ta kuma sanar damu daga ita har Hafsat da Salmah sun lallasheki amma kin qi.

     Shiru Zaynah tayi ba tace komai ba tana saurarenta.

     Cikin sigar lallashi Anty Beelki  da Anty Amina suka shiga ba Zaynah shawarar ta bar batun Majeed.

     Nan ma shiru Zaynah tayi kamar mgnr na shigarta sai da ta bari sun kai aya sannan tayi mgn.

    Kiran sunayensu daya bayan daya tayi kamar abun arziki.

     "Anty Beelki"

      "Na'am Zaynah"

      "Anty Amina"

       "Na'am auta"

        "Anty Hafsy"

         "Na'am"

"Inace dukkanku a lkcn aurenku babu wanda ya zab'a  muku mazajen aurenku, ku kuka zab'a da kanku?"

    "Eh" suka amsata gaba d'ayansu.

     "Toh ni meyasa bazaku bani wannan damar ba?"

  "Ke kuwa aka ba wannan damar sbd tun kina k'arama kuke tare da besty,kina ganin idan kika guje shi a yanxu kin mishi adalci?" Fadin Hafsat.

    Kafin ta amsa Anty Amina ta qara da fadin "Zaynah ke ko kunyar sab'a alqawari ba kya ji? Mutum shekara da shekaru yana zaman jiranki sai da lkc yayi kice baki sonshi kuma".

     "Toh ai kuma kun fadi tun ina k'arama ne lkcn bansan meye so ba, yanxu kuma na girma nasan meye so kuma na samu wanda nike so"

   "Koma dai meye autana ki tausaya karki bamu kunya ki auri d'an uwanki dake matuk'ar sonki tun kina yar jinjira" Ummie ta fada Tana mai shafa kan Zaynah dake kusa da ita.

    "Ummie sai dai kuyi hkr wlh yanxu bana son yaya Rayyan kwata2, Majeed nike so.

  "Ke wai wace irin marar kunya ce ace kowa yazo yana lallab'aki amma kinqi,ko kin dauka muna jin tsoron kine? Toh bari kiji ko zaki mutu dolene ki auri Rayyan" Anty Beelki ta fada a hasale.

    Salmah da tunda ake mgn bata sa baki ba sai yanxu tace "take it easy Anty  Billy pls".

       Salma bari ta fad'i mata,wlh yarinyar nan har mamakinta nike yi ace duk mun taru muna rok'onta amma tak'i. Bari na k'ara jaddada miki,ko zaki mutu sai kin auri Rayyan" Fad'i Ummie a hasale.

    Tashi  tsaye Zaynah tayi a zuciye ta fara mgn "a gidan nan ba wacce akayi ma auren dangi sai a kaina za'a fara? Kuma wlh ba wanda ya isa ya hanani auren Majeed har ke Ummie" tana gama fadin haka ta fita zuwa harabar gidan.

   Anty Hafsat ce ta tashi da niyyar binta ta mare ta amma Ummie dasu Anty Amina suka hana.

    Da gudu Salmah ta bita, shan gabanta Salmah tayi tare da fadin.

      Bayan fitan Salmah da Zaynah ne Ummie ta Ummie ta umurci su Hafsat da cewa su share batun Zaynah tunda ta iya bude baki tace duk basu isa da ita ba.

     Sannan tace su bari ta auri wanda take so tunda idonta ya rufe dan koda sun tilasta mata auren Rayyan toh ba zaiji dad'inta ba.

     Nan duk sukayi na'am da hukuncin mahaifiyar tasu.

       *A farfajiyar gida*

     "Zaynah ba mamaki kin haukace,har kika iya bude baki kikace ko Ummie bata isa dake ba koh"

    "Bazan ga laifinki dan kin cemin na haukace ba, sbd baki san so ba tun da kike ba wanda ya tab'a cewa yana sonki dan haka bazaki san dadi da zafin so ba shiyasa har zakiga laifin abunda nayi *Akan so*n kasancewa da masoyina"

    "Enough pls Zaynah da nayi mgn zakice ban san so ba, soyayyar banza! Ke dame soyayyar ta amfaneki in banda karya alqawari da yaudara da kuma rashin kunya da rashin biyayya? Indai har haka son yake Allah yayi min katangar k'arfe dashi"

      "Ina kika ga masoyin balle har ki mayi soyayyar? Yaya Rayyan ne dai nace bana sonsa sai inga mai yimin dole"

      "Ngd Zaynah dad'in abun Allah ke bada masoyi ba wani ba, kuma yaya Rayyan din Allah zai bashi wacce ta fiki da komai"

     "Me zai hana ke ki aureshi tunda duk kun rasa masoya" Zaynah ta fad'a tana d'aga murya

    Karaf kuwa a kunnen Rayyan, daya fito daga ta bayan gidan. bai ce dasu komai ba ya shige part d'in Ummie.

    Itama Salma shiga cikin gidan tayi tana share hawaye.

      Zaynah kuwa part din Mamie ta nufa dan bata da courage d'in komawa part d'insu dan ita karankanta tasan bata kyauta ba.

   

       *_H.N.Ubandiya._*

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now