07

1.1K 72 7
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

      Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

    *Wannan* *shafin* *naki* *ne* *Anty* *Zarah* *Bukar* ( *cute* *Zarah*). *ngd* *da* *qaunarki* *akan* *NADAMAR* *AURENA* *fatana* *a gareki* *Allah* *ya* *baki* *'ya'ya* *na* *gari*.

            0⃣7⃣

    A աɑյҽ kuwa Majeed yayi mamakin fitowar Zaynah da wuri dan batafi 5mnts da shiga ba, sai daya bari sun fara tafiyan sannan yace.

   "A yanayin da naga kin fito inada tabbacin kinga wani abu a ciki kenan wanda ni sam bana miki,

  Kuma kisani bazan iya bata lokacina akan mace wai ina nuna mata soyayya ba wannan ai shiririta ce, tun kafin aurenmu kinsan halina so karkisa ma ranki samun irinna Salmah"

   Duk maganan nan da yake sauraranshi kawai take bata cemishi uffan ba har yayi shiru.

   A ranta tace mutum baida komai sai tsabar iyayi da girman kai....

  Majeed ne ya katse mata tunani da fadin.

   "Zaynah kina hauka ne? Tun dazu ina mgn kin share ni"

  "Toh me zance bayan ka fadi ra'ayinka kuma na dade da sanin kai baka nuna ma mace soyayya, wlh ka fiye son rigima inda nayi mgn kace na fadi ba dai2 ba yanzun nayi shiru ya zama matsala"

    "Haka zaki ce?"

   "Dan Allah ya isa haka a titi muke kabari koma meye idan mun je gida ayi"

  Shiru sukayi dukansu har suka kai gida.

   Sashensu suka shiga dama basu rufe  ba.

  Kai tsaye suka shiga dakin sai dai ga mamakinsu me zasu gani?.......

    Buba nanaye wato mahaifinsu Majeed kwance rashe rashe akan gadonsu kafarsa sanye da ta kalmi yana bacci.

   A fusace Majeed ya nufe shi ya girgizashi yana fadin "baba meye haka tashi"

  Kara bajewa Buba yayi cikin muryar maye yace "magajiya karo ruwa"

  D'agashi Majeed yayi gaba daya ya tallafo kafadarshi ya nufi hanyar waje dan kaishi dakinshi.

       Zaynah kuwa hawaye kawai take tare da fadin innalillahi wainnah illahir rajiun, a yau kam ta kasa jurewa, da me zataji? da baqin cikin data gano a gidan tsohon saurayinta wanda yake mijin yayanta a yanzu koda baqin cikin tarar da suriki a dakinta a gadonta.

    A haka Majeed ya dawo ya tarar da ita, cikin dakewa yace "meye kuma abun kuka a nan?"

     Cikin muryar kuka tace "ai daman bazaka ga abun kuka anan ba tunda abun kunya gaba kuka bashi ba baya ba..........

    "Zaynah kiyi ma bakinki linzami karki fadi bakar magana akanmu"

   "Koda na fada karya nayi? Daga ku har mahaifinku ba wanda yasan yakamata.........

    Bata karasa ba ya buge mata baki yace "Zaynah dan in dakeki da daren nan ba wani abu bane, kishiga hankalinki"

    Wlh kome zaka mun bazaka hanani fadin abunda ke raina ba, wannan ai zalunci ne kasan mahaifinka mashayi ne dan cac........

 
   Bata kai ga karasawa ba taji saukan cable a bayanta, bata san lkcn da tasaki wata razanan ihun da sai da yayi sanadiyar fitowar su Idris da Sajida har suna rige rigen shiga banda Safina dake bacci dan gobe monday.

  Shikuwa zabga mata yake yana fadin "har kin isa ki zagi mahaifinmu shashasha"

  "Au baba ta zaga? kara ma yar banza,wlh yaya da ka barni da ita na koya mata hankali" Idris ya fada tare da niyyar kai ma Zaynah duka.

   Majeed ya tsaida shi "barta aiko yanzu jikinta ya gayamata"

"Wlh yaya kadan kayi mata,amma bakomai uwarki zaki ci a gidan nan" fadin Sajida

  Ita dai Zaynah kuka kawai take,wanda ba zafin bulalar ke sata ba a'a, kukan NADAMAR kin bin shawarar iyayenta take yi.

   Majeed ne ya katse mata tunani da fadin "tashi ki fita"

    Dago jajayen idonta tayi ta dubeshi sai a lkcn ta kula basu Idris.

   "In fita inje ina?" Ta tambayeshi muryarta na rawa.

  "Ki fita ki bar min dakina tunda ba daga gidan ubanki kika zo dashi ba"

   Cikin sheshekar kuka tace "ai ni ubana yafi karfin wannan gida"

   Biyota yayi kamar zai duke ta ganin haka tayi saurin fitowa daga dakin.

   "Dakin tsaya kin gani idan ban canja miki kamanni ba sakarai" yana gama fadin haka ya rufe kofa.

   Ita kuwa wani mugun tsoro ya dirar mata, da sauri ta shiga kitchen ta rufe kofar ta cigaba da kuka, gabanin asuba bacci ya saceta.

  ***

   Cikin baccinta taji abu ya hau mata kafa da bude idonta taga bera, ihu ta saki ta nufi kofa ta bude.

   Hasken rana taci karo dashi, da hanzari ta nufi dakinsu bata tarar da Majeed ba,bisaga dukkan alamu ya tafi dubanta ta kai kan wall clock inda ke a parlorn ga mamakinta karfe 8:45am.

   Da sauri tashiga daki ta fada toilet tayi wanka ta dauro alwalla tayi sallah, sai a lokacin taji jikinta yayi tsami.

  Gado ta hau ta janyo wayarta ta kira abokiyar aikinta Hajara Habib Jibril.

  Daga can Hajara tayi picking "Assalamu'allaikum amarya an tashi lfy?"

  "Wa'allaikissalam lfy lau, yau bazan samu zuwa aiki ba banda lfy dan Allah ki bada report" ta fada muryarta a dashe sakamakon kukan da tasha jiya.

   "Subhanallah Allah ya baki lfy,inace dai bakya amai?" Ta karashe da dariya.

  "Uhnm Allah dai ya shiryaki Hajara tunda an fada miki abunda ke damuna kenan"

  Dariya Hajara tayi tace "Ameen Allah ya kara lfy sai na kira zuwa anjima"

   Tea ta hada tasha ta koma ta kwanta ta shiga tunanin shekarun baya da suka shude.

  Nima nace bari nabi Zaynah dan ganin me yafaru.

   

   🎶 kai kubani kidan Buba nanaye a saman gadon surika💃🏼💃🏼💃🏼
    
        Masu gudu su gudu 🏃🏽‍♀🏃🏽‍♀

Inka san kai duka 👊🏽 ka gudu 🏃🏽🏃🏽.🎶

  Hʊssռaɦ~ʊɮaռɖɨʏa.

NADAMAR AURENATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang