Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs
💜💜💜💜💜💜
💜💜
💜💜💜💜💜💜
💜💜👫
Naɖaʍaʀ Aʊʀɛռa.
Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.
Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
0⃣3⃣
Wasɦɛɢaʀɨ.
Bayan ta shirya ta share parlor da dakinsu wanda sam a gidansu ba tayi sai dai yan aiki suyi amma tunda ita tace taji ta gani zata iya aurensa dole tayi.
karfe bakwai ta fito lokacin Majeed ya tafi mrng exercise sbd sun karba leave na sati biyu dashi da Zaynah.
ta tarar Safina na shara.
"Ah Sajida shara kike"
Sai alokacin Safina ta kula cewa Zaynah na gun, tace
"Yanzu Anty har yau ba kya iya banbance sunanmu nifa Safina ce"
"Au sorry auta kin tashi lfy?"
"Lfy lau anty" ta fada da murmushi shimfide a fuskarta.
Suna cikin haka sai ga Idris da Sajida sun fito kamar hadin baki sukace
"Woo matan bro"
Murmushi tayi tace dasu "kun tashi lfy?"
Duk suka amsa lfy lau (dan su a gidan basu gaji gaisuwa ba gara ma idan bako yazo in ya ci sa'a sun gaidashi)
Sajida tace "gaskiya matar bro wannan wankan ya mun, pls kin ara mun su idan bikin kawata Saleemah ya tashi?"
"Karki damu idan na cire zan baki kyauta bama aro ba" Zaynah ta fada.
"Ashe za'a je dake matar bro,ina jira.
Zaynah a ranta mamakin Sajida take yanda zata iya aron abun wani taje biki.
Safina ce ta katse mata tunani da fadin "anty ga kujera ki zauna"
Karba tayi tare da mata godia.
Sajida tace matar bro me kike sonyin breakfast dashi?"
"Ni koma meye zanci Sajida" inji Zaynah
Idris dake daga gefe yana combing sumarshi yace
"Shegiya matar bro kikace koma meye bari mu hadaki da kosan titi da koko kin gane baki da wayau"
Dariya su Sajida da Safina sukayi dansu a wurinsu abunda yace bakomai bane.
Ita ko Zaynah maganar ya mata zafi duk da tasan su d'abi'arsu ne, sai dai ita bata saba da hakan ba.
" kai dai share matar bro bari in soya mata yam balls tasha da tea" Sajida ta fada tare da mikewa ta nufi kitchen.
"Assalamu'allaikum" Majeed ne ya shigo sanye yake da kayan sports na Chelsea fari kal sai ratsin blue dogon wando ne.
Zaynah ce kawai ta amsa tare da yi mishi sannu da zuwa sannan ta shige ciki.
Majeed ne ya tambayi Safina "ke meyasa baki je skull ba yau?"
"Yaya shekaran jiya fa aka gama bikinku ina dan huta gajiya ne kuma fa baka biyamin kudin skull fees ba.
Kafin Majeed yayi magana suka jiyo muryar baba yana fadin
"Ina kuwa zai biya miki skull fees ya dauko waccan jan kosan da tafi karfinshi" yana gama fadi ya fice daga gidan
Idris da Sajida mai suka sani banda dariya.
Sai da Majeed ya tsawatar musu,
Safina tace ku dai Allah ya shirye ku komai sai kuyita biyema baba kuna mishi dariya shiyasa yake jin dadin cigaba da wasu abubuwa.........
Majeed ne ya katseta da fadin "kema ya isa haka gobe idan zaki tafi skull sai na baki kudin skull fees din"
"Toh yaya"
Dakinsu ya shiga yayi wanka ya shirya suka jira Sajida ta kawo musu breakfast.
*⃣*⃣
Karfe 6:45pm.
Zaynah na a dakinta ta fara jin sautin wakan Buzu na 🎶Zata yaga Zanin🎶 a mp.
Fitowa tayi dan ganin meke faruwa, Sajida da Safina keta kwasar rawa a tsakiyar gida.
Idan ka saurara zakaji an fara kiraye kirayen sallah amma bai sa sun kashe ba.
"Sajida.... Safina....." Zaynah ta kirasu da karfi.
Sajida ta rage karar mp tace "ya akayi matar bros ko zaki taka ne kema?"
"A'a nace ko zaku kashe kidan har a idar da sallah"
"Toh kice yar gidan liman aka auro muna,mun saba kunna abunmu ba wanda ya taba hanamu sai ke zuwan jiya2 ni iyayi ne bana so" Sajida ta fada tare da k'ara volume in mp.
Komawa daki tayi a ranta tace "wannan gida ya wuce duk yanda mutane ke fada min"
Bayan sallar isha'i Buba nanaye ya tarasu duka anan tsakiyar gidan,
Ya raba musu aikin gida inda yace da gari ya waye Zaynah zata fara girki Sajida da Safina suyita wanke2.
Majeed yayi korafin cewa Zaynah na zuwa aiki amma Buba yace kafin ta tafi sai tayi abun kari inta dawo tayi musu na rana acewarsa inda basu Sajidan fa.
Hʊssռaɦ~ʊɮaռɖɨʏa.
YOU ARE READING
NADAMAR AURENA
RandomZaynah kuwa kasa daurewa tayi a yau kuka kawai ta keyi tana fadin innalillahi wa'innah illaihir rajiun, dame zata ji? da baqin cikin da ta gano gidan tsohon saurayinta wanda yake mijin yayarta a yanzu? ko da baqin cikin ganin surikinta akan gadonta...