02

1.3K 93 4
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

     In veneration to Lubna Sufyan.

Facebook: Hussaina N. Ubandiya.

            0⃣2⃣

   Cɨɢaɮaռ ʟaɮaʀɨ,

  Majeed da Idris suka shigo gida rirriqe da mahaifin nasu ba karamin duka yasha hannun Musa kafin suje.

Kuma saida Majeed ya biyashi kudinsa sannan ya bari suka daukeshi.

  Ihu kawai yake kamar karamin yaro, Majeed ya kira Sajida

  "Sajida2 ki fito da tabarma da sauri"

  "Toh yaya"

A nan tsakar gida suka shimfide shi yana ta surfa ma Musa ashar

*

A daki kuwa Zaynah ce da kawayenta Amal da Jidda, Amal tace

"Ina kuka samo wannan kuma sai kururuwa da ashar kawai yake muku a gida"

"Am uhnm mahaifinsu Majeed ne baida lfy muna tare aka zo kiransa wai mahaifinsa ya fadi baida lfy"

  Amal da Jidda suka kalli juna suka sheke da dariya.

  "Ban gane ba, dariyan na meye? in fada muku mutum baida lfy maimakon kuyi masa fatan samun lfy sai ku hau dariya"?

"lallai Buba nanaye baida lfy, ai addu'a ya kamata ya fito bakinsa ba ashar ba" Jidda ce ta fadi haka tana mai kara shekewa da dariya"

  "Gane min hanya kedai ai wanda yaqi ji baya qi gani ba" fadin Amal.

   "Ya isheku haka malamai zuwa gidana kukayi dan ku ganni ko cin mutunci kuka zo"

"Jidda tayani ji wai gidanta fa tace"

"A'a ina fa gidanta gidan Buba nanaye dai"

  "Naji koma dai gidan waye ya isa haka, kunsan Majeed na iya shigowa at anytime kuma ba dadi yaji kuna aibanta mahaifinsa"

"Hakane kuma" fadin Jidda.

Wai ko dan drinks babu ne a gidan ko rowa ake muna" inji Amal.

"A'a wani irin rowa kuma? bai samu zama bane yanata hidimar mara lfy shiyasa bai siyo ba"

  "Hmmm gaskiya ba karamin sakarci kikayi ba Zaynah kuma baza mu gaji da fadi miki hakan ba, ga dan uwanki wanda zaku zauna daga ke sai shi amma kika zabi zama da wannan.......

bata karasa ba Zaynah ta dakatar da ita.

  "Dakata Amal na gaji haka nan meya shafeku da rayuwata ne,ku zaku zauna a gidan koni? koma dai menene ai an gama tunda an riga an daura har komai ya wakana"

Kalmar komai ya wakana da Zaynah tasaka a maganarta shi ya gyara komai har kawayen suka dara daga nan sukaci gaba da hira.

  Basu suka bar gidan ba sai baya azahar.

   A lokacin Majeed ya samu damar shiga sashen,

  Tayi masa sannu da sannan ta gabatar masa da abincin da Sajida ta kawo mata.
   
Zaynah tace

  "Dear tun safe rabon da in saka ka idona"

shiru ya mata ya fara cin abincin da tayi serving insa.

"Dear fa da kai nake magana"

  "Oh Allah Zaynah a garinku in ana cin abinci ana magana ne? na dawo na tarar kawayenki sun zo so kike inzo in zauna cikinsu kome?"

  " bai kai can ba dear Allah ya baka hakuri"

"Ce miki akayi nayi fushi kefa sam bakida fahimta"

shiru kawai tayi bata kara cemai komai ba.

  "Majeed3" Buba nanaye keta kwala masa kira har ya shigo parlor.

Zaynah ce ta gaishe shi "ina yini baba"

"Da ban yini ba kya ganni ace tun wayewar garin Allah baki san kije ki gaida ni ba sai dana zo dakinki"

"Dun Allah kayi hkr baba" fadin Zaynah shiko Majeed cin abincinsa kawai yake kamar baya wurin.

"Wai kai Majeed baka san dani bane a gun?"

  "Toh inna san kana nan sai in hau tsalle ga baba ga baba?"

"Ai kai haka kake sai ka sa yar yarinyar nan ta raina ni"

Ita dai Zaynah kanta a kasa sai wasa take da yan yatsunta.

"Ni fa baba baka fada min dalilin zuwanka ba" Majeed ya fada ba annuri a fuskarsa.

  "Yanzu kuwa zakaji tunda ka matsu in tafi in baka wuri, dama dari biyar kawai zaka ban in tafi gidan magajiya"

Janyo hannun baban nasa yayi suka fita waje yace

"Baba wai meke damunka ne a gaban matata kake tambayana kudin zuwa gidan magajiya?"

"Ah lallai ma kunyarta zan ji ita ta haifar min kai"

  " toh ni dai bani da kudi sai kayi hkr yau"

  "Hkr fa kace Majeed ko ka bani ko in tafi wurin matar taka ta bani, ko kuma in tafi can gidan in amsa bashi a kara dukana" ya fara tafiya da niyar barin gidan.

Da sauri Majeed ya ciro kudin daga aljihunsa ya bashi.

Dukan kirjinshi yayi da wasa "shege Majeed ashe baka son girmana ya fadi" (🙊 wa'iyazubillah wannan wani irin uba ne maimakon ya sanya masa albarka amma da shege ya kira sa)

 
Hʊssռaɦ~ʊɮaռɖɨʏa

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now