©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
💜💜
💜💜💜💜💜💜
💜💜👫
Naɖaʍaʀ Aʊʀɛռa.
Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.
Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
*MssHussaynah@wattpad.*
*Shin na kyauta kuwa 🤔 idan har banyi miki godia da irin k'aunar da kike nuna min nida NADAMAR AURENA ba.*
*_Na'eematoo Abdul'azeez_*.
3⃣2⃣ ➡ 3⃣4⃣
Suna komawa part dinsu kowa ya shige dakinshi.
Da kuka Zaynah ta shiga ta fada a jikin Salmah, a rikece Salmah ta fara tambayarta dalilin kukanta amma ta kasa fadi mata.
Daina tambayarta tayi ta shiga lallashinta, sai da taga ta tsagaita da kukan sannan ta fita daga dakin taje dakin Ummie.
Cikin damuwa ta tarar da Ummie ta kasa tsaye ta kasa zaune,cike da ladabi ta jawo hannun Ummie suka zauna a gefen gado.
Sannan ta tambayeta dalilin kukan Zaynah da dalilin shigarta damuwa.
Nan Ummie ta sanar da Salmah komai, tare da nemar alfarmar ta lallashi Zaynah kar ta kunya tasu.
Salmah bata bar dakin ba sai da ta tabbatar da ta kwantar ma Ummie da hankali.
Koda ta koma dakinsu ta tarar Zaynah tayi bacci, itama kwantawa tayi a gefenta cike da tunanin ta inda zata bullo ma kanwar nata.
haka har bacci barawo ya sace ta.
*Washegari*Tafiya ya kama Baffa zuwa china zai kai ak'alla 3 weeks koma fiye da haka.
Zaynah taji dadin tafiyar da Baffa yayi, sbd zata fi son ta gama exam dinta idan yaso ko wani rikici za'ayi ayi.
Dama gobe zasu fara jarabawar.
Bayan sun dawo daga yima Baffa rakiya, kai tsaye dakinsu ta shige.
Bata dade da shiga ba sai ga Salmah ta shigo itama.
A gefen Zaynah dake zaune akan gado itama ta zauna.
Sannan ta kirata cike da kulawa.
"Cwt sis (wani lkcn haka takan kirata)
"Na'am Anty Salmah"
"Yanzu ke a ganinki abunda kike sonyi ya dace? Shekara da shekaru yaya na zaman jiranki sai yanxu da rana tsaka kice baki sonshi?"
"Hmmm Anty bazaki taba fahimta ba shiyasa"
"Ban gane bazan taba fahimta ba,kin sanar dani ne ban fahimce kiba?"
"Uhnm Anty mu barshi akan bazaki gane ba kawai,sannan ni nagama mgn bana son yaya Rayyan karki bata bakinki da lkcnki wurin shawo kaina"
"Naji Zaynah amma ina son ki sani koma me yaya Rayyan yayi miki bai dace ace kin guje shi ba, ki fad'i mau laifinshi dan ya gyara kinji cwt sis ki qara tunani"
"Toh naji ngd" daga haka ta juya ma Salmah baya ta dauki wayarta.
Tashi Salmah tayi ta fita daga dakin dan ta gane me Zaynah ke nufi da bazata fahimta ba, ma'ana tunda ba wanda ya taba cewa yana sonta kuma bata taba soyayya ba toh bata san zafin so ba kenan.
Girgiza kai Salmah tayi tare da share hawayen da ya gangaro mata.
Tunda take rashin masoyi bai taba damunta ba dan a ganinta nata *kaddara*r kenan. Kuma tanada yaqinin akwai kyakyawar tanadin da Allah yayi mata.
Da wannan tunanin ta kai dakin Ummie.
Da sallamarta ta shiga, Ummie ta amsa sannan ta samu wuri ta zauna.
Ummie ce ta fara mgn "ya akayi Salmah kin samu shawo kan kanwar taki?"
Girgiza kai Salmah tayi alamar a'a sannan tace "Ummie me zai hana ke kiyi mata mgn da kanki? A nawa ganin zata fi jin naki fiye da na kowa"
"Hakane Salmah inshaa Allahu zan zauna da ita idan na dawo anjima daga asibiti.
"Au yau na dauka baza kije ba naga har yanxu baki shirya ba"
"Eh sai 12:00pm nake so naje"
"Toh Allah ya kaimu" Salmah ta fad'a a lkcn da zata fita daga d'akin.
"Ameen" Ummie ta amsa.
*_H.N.Uɮaռɖɨʏa_*
YOU ARE READING
NADAMAR AURENA
RandomZaynah kuwa kasa daurewa tayi a yau kuka kawai ta keyi tana fadin innalillahi wa'innah illaihir rajiun, dame zata ji? da baqin cikin da ta gano gidan tsohon saurayinta wanda yake mijin yayarta a yanzu? ko da baqin cikin ganin surikinta akan gadonta...