14-16

1K 59 2
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
💜💜
💜💜💜💜💜💜
💜💜

👫

Naɖaʍaʀ Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

*MssHussaynah@wattpad.*

*A jiya 23/3/2017 na shiga gidansu sai dai na tambaye mahaifiyarta "ya mai jiki?" Ashe ba rabon inyi mata ganin karshe, dan adaren jiyan ta amsa kiran ubangiji. Allah ya gafarta miki kanwata HUSSAINA, Allah yaraya abunda kika bari.*😭😭😭

1⃣4⃣ ➡ 1⃣6⃣


Tun shigar Zaynah motar batace da Rayyan uffan ba sai kallon window take da alamar damuwa a kan fuskarta,

Rayyan kuwa samun kanshi da shiga damuwa yayi shima ganin yanayin da Zaynah ke ciki, suna dab da shiga bk Rayyan ya kira Zaynah cike da kulawa.

"Autar Ummie" ( haka yakan kirata a lokutan da ya karanci damuwa a tare da ita)

Sake kiranta yayi sai dai sam batasan yana yi ba ma.

Sauka yayi daga titin ya samu gefe yayi parking sannan ya kirata da dan karfi.

"Zaynah ! "

A dan firgice ta amsa "na'am yaya, ya muka tsaya anan? Motar ta samu matsala ne?"

Girgixa mata kai yayi alamar a'a sannan yace "meke damunki autar Ummie?

"Laah bkm yaya meka gani halan"

"Kar kiyi mun k'arya Zaynah so nawa ina kiran sunanki amma bakiji ba kinyi nisa"

"Kaina kawai ke ciw........ Sauran maganar ya makale a fatar bakinta ganin Majeed ya wuto da farar rubber2 dinsa.

Binshi tayi da kallo har da leqawa ta window, mamaki ya kama Rayyan shima ya kalli direction din da take kallo yako ga abunda ya dauke mata hankali.

Ranshi yayi mugun baci cikin tsawa ya kirata.

Sai a lokacin hankalinta ya dawo jikinta kunya ya rufeta.

Nan fa Rayyan ya hau yi mata fada, tace yayi hkr amma kamar kara zugashi tayi yacigaba.

Nan fa ran Zaynah itama ya baci ta ciro wayarta ta kunna waka ta saka earpiece, ai Rayyan be san lkcn da hannunsa ya mari Zaynah ba.

Nan ta fashe da matsanancin kuka dan tunda take Rayyan be taba daga hannu da sunan dukan taba sai a yau.

A bangaren Rayyan kuwa tsantar *NADAMAR* marin Zaynah yayi yana Allah waddai da zuciyar data ɖibe shi har ya aikata hakan.

Cike da lallashi ya kira sunanta.

"Zaynah dan Allah kiyi hkr kinji daina kukan,idan kuma marin zaki rama bismillah indai har zai sa ki huce"

Kyaleshi tayi ta cigaba da kukan, gajiya yayi da bata hkr yaja motar suka bar wurin.

**

Suna isa gida yayi parking sai Zaynah ta bude motar ta fita, da gudu ta shiga parlorn ta haye upstairs ta shiga dakinta ta sama kofa key, tayi hakanne dan idan su Ummie sukaji dalilin kukanta kara marinta zasuyi.

A ranar dai golden morn Zaynah ta wuni sha har dare.

Washegari tana tashi tayi wanka ta dauro alwalla tayi sallah,sanin Rayyan na masjid har lkcn yasa ta sidada ta shiga dakinsa as expected asaman dressing mirror taga car key dinshi dauka tayi ta fice da sauri.

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now