44-46

938 55 1
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

      Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

 
  *MssHussaynah@wattpad.*

   
    *_Daughter Jidda kina ina ga page dinki._*

       *_Allah ya nuna muna ranar bikinki, wai wayaga Hussaina na aurar da d'iya 😁. Though kince ni fake mum ce 🙁._* 

     4⃣4⃣ ➡ 4⃣6⃣



*_Bayan shekara d'aya da wata bakwai_*

    
        Abubuwa da dama sun faru,ciki kuwa harda kammala karatun Zaynah har tayi service watanta d'aya da fara aiki da *NTA* na bk.

     Rayyan da Salmah kam shaquwa sosai ya shiga tsakaninsu tare da soyayya mai tsafta.

   Zaynah da Majeed kam ba wani abun burgewa a soyayyarsu dan ko kiranta yayi a waya sai dai yace yana jinta itama tace tana jinshi har su gaji su katse wayar.

     A ranar thursday akayi *walimar* maza zalla a  *Shagalinku*               hall inda aka gayyato *Dr Maqari*.

     Ranar friday kuma akayi *Arabian night* a  *Saffar hotel*.      
   Amaren na sanye da sky blue Arabian gown wanda akayi ma ado da dark pink stones, sai akayi musu rolling da veil din kayan daya kasance dark pink.

  Angwaye kuma na sanye da grey jallabiya.

     Sauran jama'a ma duk matan na sanye da abaya mazan da jallabiya.

   Haka dai akayita gudanar da shaglin har akazo lkcn da matayen zasu ciyar da mazajensu nan Salmah taba Rayyan,Khairat taba Hussein, koda akaxo kan Zaynah ita kam ba ango.

    'Ya'yan itatuwa ne da shawarma sai shayi.

     Dan ya shirya zai je sai gashi an kirashi a waya cewa yaje yayi bailing Idris a station yayi fad'a da wani akan budurwa.

     Koda ya dawo lkc ya qure sai kawai ya fasa zuwa.

     A can kuwa Zaynah bata san lkcn da hawaye ya zubo mata ba, dan aganinta tozarta ta kawai Majeed yayi niyyar yi shiyasa bai zo ba.

   Dan dama daqyar ta samu ya amince zai je,dan ce mata yayi bazai yiwu yana bare yaje cikin danginsu a wulaqanta shi ba.

    Da lallashi ta samu ya yarda zai je sai gashi kuma lallura ya gifta kuma bai samu kiran Zaynah yayi mata bayani ba shiyasa ta dauka ko ganin dama ya hanasa zuwa.

     k'arfe 9:00pm taron ya watse kowa ka kalla yana cike da farin ciki idan ka cire Zaynah.

      Suna komawa gida da gudu ta nufi part din Mamie tana shiga ta zarce d'akin Hafsat daya koma nata tun da dadewa,ta rufe sannan ta fad'a kan gado tana kuka.

     K'arar wayarta ne ya katse ta ta duba wayar taga Majeed ne ke kira taki d'agawa.

Sai da ya kira sau hudu ana biyar ta d'auka tayi mishi shiru.

    Nan dai ya lallasheta yace mata wani babban uziri ne ya taso mishi a lkcn, a haka dai har ta haqura yayi mata sai da safe suka ajiye wayar.

    Washegari *Daurin aure/yinin biki* aka d'unguma xuwa Dakin gari inda za'a daura auren su Rayyan dana su Zaynah sannan a dawo bk a d'aura na Hussein tunda Khairat iyayenta yan bk ne.

   An d'aura na Rayyan da Salmah sannan aka buqaci waliyen Majeed amma babu sai frnds d'inshi.

    Hankalin Majeed idan yayi dubu ya tashi ya rasa yanda zai yi.

  *Bk gidan magajiya*

      Buba nanaye ne zaune da abokanshi yana fadi musu yau karsu bugu dan zasu tafi d'aurin auren Majeed a dakin gari.

   D'aya daga cikin abokan ne yace "nan dai da dakin gari ai ba nisa nasan kuma sai k'arfe biyu za'a d'aura auren dan haka muyi salabiretin(celebrating) kafin lkcn.

      Buba dai bai yarda ba daqyar sukayi convincing dinshi yasha nan suka bugu har lkcn d'aurin aure yayi basu sani ba.

   Gashi baya shiri da 'yan uwansa shiyasa bai fadi musu batun auren Majeed din ba a ganinshi lalatattun abokanshi sun isheshi.

   Kuma ya yanke ma su Majeed alaqa da yan uwan mahaifiyarsu.

   *Dakin gari*

Na'ibi naji yana qara maimaitawa "waliyan d'ayan angon su karaso kusa lkc na qurewa"

     Saifullah ne yaja Majeed gefe dan suyi shawara basu kai ga farawa ba sai ga motoci uku sun parker dan haka sai suka tsaya da mgnn.

   "Saifullah yace kamar nasan motocin can" bai rufe baki ba sai gashi masu motar sun fito.

      Co-lecturers dinsu ne kuma wa'inda suka isa haihuwarsu.

    Saifullah bai bi takan Majeed ba ya qarasa wurinsu suka gaisa ya sanar dasu halin da ake ciki nan suka yanke shawarar prof.Shehu Khaleed ya amsa auren.

   Ana gama d'aurin aure aka koma Bk aka d'aura na Hussein da Khairat.

    *A gidansu Zaynah*

       Ko ina ka duba gungun mata ne wasu a farfajiyar gidan inda aka sa canopies da kujeru wasu kuma a cikin gidan.

Anyi rabon abubuwa sosai wa'inda duk a *Heenat digital print & ICT business solutions Ltd* akayi printing dinsu.

    Daga gefe na hango wasu mata uku tun daga nesa nace kamar nasansu sai dana k'arasa naga ashe Anty Lubna Sufyan,Anty Ummie jay,Anty Aynarh dimples suna cin tuwon amala da miyar kubewa yaji ganda da akayi serving dinsu.

   Dana k'ara kallon gefe kuwa Anty Ummie kay,Anty Zeenasir , dota Jidda,In-law Fiyya galadanci ne da Anty Beelkisu Suleiman sai yagar kaji suke.

    Nima samun wuri nayi dan a kawo min nawa,sai ga lady of d rose kuwa ta kawo min, Zuwaira yawale ta bani drinks.

    Ban tab'a ba sai na tashi domin zuwa daukar rahoto, tun daga nesa na hango in-law da Anty Beelkisu Suleiman suna kokawa akan namar dake a plate dina.

    Ban tsaya sanya ba nazo da gudu amma kafin in karasa har sun gama dashi, abun takaicin kuma Fiyya in-law dina ce bana iya mata rashin m Anty Beelki kuma Allah sauke lfy ce.

        Can na hango yan Ummie jay novels, dimples, Taskar novels, Homel&Sofie G novels,Hussaina N Ubandiya novels suna wawaso banyi kasa a gwiwa ba naje nima na saka hannu cikin ikon Allah na samu d'an jajjagen pepper chicken din na dan lashe hannun nawa.

    Kamar daga sama na hango Anty Zarah Bukar ta ajiye plate dinta da alama bata tab'a komai a ciki ba nako garzaya na samu ta bani.

     Na d'an tafi ta gefe dan in d'an b'oye ashe Anty Hassana Magaji da Anty Aina'u(mmn Abdul Nasr) da Anty Huraira yabo sun ganni suka karbe plate din ba tare dana ci komai ba.

      A haka taro ya watse bayan sallar isha'i aka kai amare gaban iyayensu dan neman gafara.

    Nan duk suka nema kuma suka yafe musu, Zaynah harda na yanninta ta nema kuma duk sun yafe mata.

      Baffa yaba amare kyautar motoci, har da amaryar Hussein.

     Magajiya da kawayenta sune suka zo daukar amarya Zaynah.

      
        *Cigaban lbr*

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now