10

1K 57 0
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

      Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

             1⃣0⃣

   A ranar lecture biyu Rayyan yake dashi, 4:pm ya gama duka ya dauki hanyar birnin kebbi ranar jikinshi yayi matukar sanyi sanin lecturern bai da tausayi.

  Ya isa yayi parking ko kashe motar baiyi ba ya hango Zaynah ta fito a guje ta nufosa ( haka take batada riqo kome ka mata 20 mnts yayi yawa zaku shirya)

  Bude motar yayi ya fito lkcn yayi dai2 da karasowan Zaynah, rungumeshi tayi tare da fadin "yayana oyoyo"

  Rabata yayi da jikinshi yace " wai ke baki san kin girma bane daga yau sannu da zuwa kawai zakina cemin ki daina hawa jikina"

   Baki bude Zaynah take kallon Rayyan dan tunda take bai taba hanata hawa jikinsa ko yi mishi oyoyo ba,

shikuwa missing test din da yayi akan kafewan Zaynah yasa kawai beson damuwa shiyasa yace Mata haka.

   Hannunshi ta riqo bai hanata ba,suka shiga ciki sun saba duk wanda ya riga dawowa ba zai ci abinci ba sai ya jira daya amma yau Rayyan part dinshi ya nufa maimakon dinning, still hannunsu na hade.

   Zaynah tayi karfin halin fadin "yaya yunwa fa naki ji muci abinci kafin kayi wanka" sakin hannunta yayi yace,

  " jeki ci abinci auta ni banda appetite ne yau" yana gama fada ya cigaba da tafiya, itama bin bayanshi tacigaba dayi dai2 zasu shiga dakinshi sukaji muryar Hafsat tana cewa.

   " ke ina zaki ba an hanaki shiga dakin besty ba?" Tsayawa sukayi su duka Rayyan da Zaynah.

   Hafsat ta qara da fadi " besty wai meyasa baka son tsawatar ma Zaynah sanin kanka ne su Mamie sun hanata shiga gurinka amma kai idan kaga zata bika ba hanata"

   " zan kiyaye besty ISA na gode da tunatarwa"  Rayyan ya fada tare da shiga dakinshi ya rufe.

  Ko kadan bai ji haushin abunda Hafsat tayi ba sbd yasan hakanne ya dace, Zaynah ta bar shiga dakinsa sbd shaitan ba raggo bane musamman shi da yake son Zaynah  koda ma kanwarshi ce na ciki daya ba koda yaushe ya dace tayita zuwa dakinshi ba sbd gudun bacin rana shaitan yazo ya rinjayi zuciyarsa.

  Har bayan magrib ba wanda yaci abinci cikinsu, shi Rayyan bai da masaniyar cewa Zaynah bataci abinci ba sai da ya dawo daga masjid Salmah ke fadi masa. Tambayarta  yayi.

   "Ina autar take yanzu?"

   " tana can part din Mamie,wai fushi take da Ummie" Salmah ta fada.

   "Fushi kuma? Me Ummie tayi mata?"

  "Da taga bata ci abinci ba sai tayi mata fada maimakon lallashi,ana cikin mata fada Abba ya dawo shima ya qara da nashi"

   "Kai kai kai yau kam dole ayima su Ummie tawaye" ya fada tare da mikewa ya nufi kofar da zata sadashi da part din Mamie.

   Yana shiga dinning area ya nufa dan yasan Baffa ya dawo suna having dinner.

  Baffa Mamie yan biyu Hafsat da Zaynah ke a dinning ko wanensu nacin abinci idan ka cire Zaynah dako spoon babu a hannunta,ba yadda ba'ayi da ita taci abinci amma taqi.

   Gaida Baffa da Mamie yayi tareda jan kujerar kusa da Zaynah ya zauna.

   Ba tareda yace da ita komai ba ya bude warmer ya debi abinci a plate ya saka cokali biyu ya kai plate din a tsakiyarsu shida Zaynah.

   Hafsat ne tace " kai besty bamu fa dafa abincinmu daku ba amma kazo ko tayi bamuyi maka ba ka cika plate" dariya duk a ka sa .

   Rayyan yace"Allah dai yaso muma Ummienmu ta muna abinci, ba dun Auta da tayi fushi ba da baki ganmu nan ba" dariyar aka kara yi.

  Be kara bi ta kan Hafsat ba ya mika ma Zaynah spoon amma taqi karba yayi2 amma taqi a hankali tace " kabani a baki"

  Ba bata lkc ya fara bata, bayan sun kammala sukayi sallar isha'i sannan suka dauko skull bag aka hau karatu.

          *HOMEL*

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now