Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
💜💜
💜💜💜💜💜💜
💜💜👫
Naɖaʍaʀ Aʊʀɛռa.
Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.
Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.
0⃣4⃣
Baʏaռ satɨ ɮɨʏʊ.
Raʍʟat a kitchen tana ta hidimar hada breakfast gashi tayi late yanzu batun karfe tara ake ita da ya kamata ace tun 8 tana office.
Tunawa tayi lokacin da take gida anything 7:30 an riga da an shirya mata table amma yau gashi ita keta fama ga masifa da tasha gun Majeed wai ta bari kanwarsa ta tafi ba tare da tasamu karyawa ba.
9:15 ta kammala ta nufi dakinta da nasu a hannunta.
"Dear ina kake shirin zuwa bayan gashi na kammala"
" kin dauka zan iya cin wani abune bayan Safina haka ta fita ai kawai ki zauna kici kayanki, ni na tafi"
"A dawo lfy" ta fada barin abincin tayi itama ta nufi daki tayo wanka.
Tana fitowa ta tarar da Buba nanaye na kari gaishesa tayi.
"Baba ina kwana"
"Lfy lau" ya amsa a dakile ya dora da cewa,
"Na fuskanci baki kware a harkar aikin gida ba aikin da Sajida ta sabayi cikin minti 30 shi ya dauke ki awa uku toh kisani bazan juri ganin auta na tafiya makaranta da yunwa ba"
"Baba ayi hakuri inshaa Allah zan gyara"
"Da dai yafi miki"
Ta tashi da niyar wucewa ya tsaida ta "ke ban aron dubu idan Majeed ya dawo ki karba"
2 thousand ta ciro tace " Baba gashi basai Majeed ya biyani ba ai nima yarka ce"
Budewar bakin Buba ke da wuya yace "oh ni Abubakar mata da kisisina kuke yanzu nasan shi za'a ce masa na ranta dubu uku amma ni ance kyauta aka ban dan neman gurin zama" ya karashe yana mai riqe haba.
Ramlat dai batace dashi komai ba a ranta take tunanin har nawa Majeed yake dashi dazata masa cuwa2.
Da wannan tunanin ta nufi gida makwabtansu inda aka ajiye mata motarta dan gidansu Majeed ba space.
Ba ita ta isa wurin aiki wato NTA television ba sai 10:30,
Nan fa aka hau tsokanarta amarya3, wata abokiyar aikinta mai suna Hajara Habeeb Jibril da yake ita tana da aure take ma Ramlat tsiya da cewa.
"su Ramlat sabon shiga watan sai 10:30 ake isowa lallai dole ince dake dadi miji"
Dariya kawai Ramlat tayi ta nufi office inta domin ta shirya dan ita zatayi casting news yanzu.
****
Karfe 2 ta nufi gida, bata tarar da kowa a gidan ba, sallah kawai tayi ta shiga kitchen rasa ma abunda zata dafa tayi can dai ta yanke shawarar dafa macaroni dan tasan shi zaifi mata sauri.
Cikin awa daya ta kammala ta zuba ma Buba nashi a wani madaidaicin warmer shima Idris haka sai Sajida da Safina ta hada musu sannan ta zuba nasu ta tafi dashi.
Tana shiga ta hada duk abunda zasu bukata wuri daya sannan taje tayo wanka tare da dauro alwalla ta fito.
Tana sallah taji alamun Idris da Sajida da Safina sun dawo, bayan ta idar tana shafa mai Majeed ya shigo ba Sallama baice da ita komai ba yaja hannunta dama bata cire hijjab inda tayi sallah ba.
Inda su Sajida ke zaune sun tasa abinci gaba ya kaita sannan ya saki hannunta ya mika mata plate in Safina.
"Gashi kiyi tasting" ya fada da daga murya,
Ba musu tasa spoon ta diba ta kai bakinta kasa hadiyewa tayi dan abincin yayi mugun gishiri da wuri ta zubda na bakinta.
"Keda kika dafa kenan kin kasa ci ina ga sauran mutanen gida?"
"Wlh kuskurene Majeed" ta fada muryarta na rawa.
"Ramlat matsalarki yawa ne da ita baki gama aiki cikin lokaci kuma da kyar ake iya ci toh kisani bazan dau wa'innan iskancin ba yanzu duk yawan abincin nan sai dai a zubar ga yara na fama da yunwa"
"Dun Allah kayi hkr bari na dafa muku ko indomie ne" ta fada tare da kama hanyar kitchen maganar Sajida ya tsaida ta.
"Matar bros da kin barshi dan nasan sai kin dau fiye da awa sannan yazo ya kasance ba biyan bukata"
Juyowa Ramlat tayi tace "Sajida bana son rashin kunya ni sa'ar kice da zaki fada min magana son ranki?"
"Dakata Ramlat bana son rashin gaskiya ina rashin kunya a maganarta? Inace duk abunda ta fada batayi karya ba in kin gyara ki gyara" Majeed ya fada sannan ya koma kan Sajida.
"Jeki dafa muna indomie in.
Ran Ramlat a bace ta shige sashensu.
Ni dai nace kome akayi miki ke kika ja ma kanki kuma kadan kika gani 😜.
Hʊssռaɦ~ʊɮaռɖɨʏa
YOU ARE READING
NADAMAR AURENA
RandomZaynah kuwa kasa daurewa tayi a yau kuka kawai ta keyi tana fadin innalillahi wa'innah illaihir rajiun, dame zata ji? da baqin cikin da ta gano gidan tsohon saurayinta wanda yake mijin yayarta a yanzu? ko da baqin cikin ganin surikinta akan gadonta...