49

922 49 3
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

      Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

  *MssHussaynah@wattpad.*

     

              4⃣9⃣



       Bayan wasu kwanaki da Zuwan 'yan gidan marigayi Buba gidansu Zaynah.

     Majeed ya d'auki qannin nasa ya kaisu islamiyar dake nan unguwar nasu akayi musu register.

    A ranar suka fara zama aji dan sun riga sun d'inka uniform.

    'Yan unguwar sunyi matukar farin cikin ganin su Idris sun koma islamiya,dmn rayuwar duniya batayi idan ba ilimin addini.

     Dukansu basu sa ma kansu girman kai ba sun zauna ajin da aka basu tare da niyyar maida hankalinsu akan karatunsu.

      *Bayan sati d'aya*

      Hassan ne tafe a cikin motar sa zai je gidan Buba kai ma Zaynah saqon da Ummie tace ya kai mata.

     Yana parking sai gasu Sajeeda sun dawo daga islamiyar yamma.

     Gaishe shi sukayi ( su Sajeeda an fara hnkl) bayan ya amsa ne yake tambayarsu ko Majeed na gida?

     Suka ce ya bari su duba, yace idan yana nan su fad'i mishi yayan Zaynah ne.

     Cikin sa'a sun tarar da Majeed tare da Zaynah suka fadi mishi saqon sai ya fita yayi mishi iso.

    Suna gaisawa da Majeed, Majeed ya fita daga parlorn ya basu wuri.

    Qara gaisawa sukayi ya bata saqon tayi godia,  sannan  tace " Yaya ranar da muka je gida kace zamuyi waya amma baka kira ba"

   "Daban kira ba ke meya hana ki kira?"

   "Yaya gani nayi kai kace zaka kira"

   "Toh naji dama ba wani abu bane qanwar mijin nan naki na gani ina so ko za'a bani?"

     Fuskar Zaynah cike da farin ciki tace "yaya mai zai hana? ai kawai bari na kirata kuyi mgn" ta k'arashe mgnr da niyyar tashi.

    Dakatar da ita Hassan yayi yana mai cewa "ke dai har yanxu yarinta bai bar kanki ba, yanxu sai naje gabar k'aramar yarinya ina fad'i mata ina sonta?"

     "Toh yaya idan baka fad'i mata ba yaza'ayi ta sani har ayi auren?"

     "Kanki baya ja,yanxu kira shi Majeed d'in ki tambayar min inda yake inje muyi mgnr masu hnkl"

    "Au yaya ni banda hnkl kenan?" Zaynah ta tambaya tana k'okarin kiran Majeed.

      Da ya d'auka ne ta sanar masa yaya Hassan ke son mgn dashi yace gashi nan shigowa.

       Ba'ayi minti biyar ba sai ga Majeed Zaynah ta basu wuri sukayi mgn.

    Inda Majeed ya shaida masa ba damuwa ya bashi, sannan Hassan ya karbi numbern Sajeeda ya tafi.

      Bayan tafiyar Hassan ne Majeed ya kira Sajeeda yayi mata bayani, nan take kuwa ta amince.

    Majeed ya yanke hukunci sanar ma 'yan uwan mahaifinsu.

      Cike da farin ciki Hassan ya shiga gida, part d'in Ummie ya fara shiga bai ganta ba.

     Ya tafi na Mamie itama bata nan sannan ya nufi parlorn Baffa, a can duk ya tarar dasu.

    Da sallama ya shiga, kana ganin shi kasan yana cikin farin ciki.

      Samun wuri yayi ta gefen Ummie ya zauna tare da gaidasu suka amsa.

    Ummie ne tace "Hassan surika kasamo min ne naganka cikin farin ciki haka?"

    Sosa k'eya yayi fuskarshi d'auke da murmushi yace "eh Ummie"

     "Alhamdulillah" Ummie da Mamie suka fad'a a tare.

   Ummie tace " A ina take 'yar wani gida ce?"

    "K'anwar Majeed mijin Zaynah Sajeeda"

    "Ah abu yayi kyau Allah ya sanya alkhairi" fadin Ummie.

    Baffa da Mamie suka amsa "Ameen"

    Baffa yace "sai a fadi ma shi Majeed d'in cewa ya fadi ma magabatansu next week 'yan dakin gari zasu je a saka rana"

    Da dariya Mamie tace "Haba Alh.da wuri haka kamar dama ana jirace?"

    "Ah toh mai za'a tsaya jira? Ina ce  duk 'yan uwanshi  sunyi aure saurashi?" Fad'in Baffa.

   Ummie tace "gskyane kam gara ayi komai da wuri"

     Haka ko akayi yan dakin gari sunje sun nema ma Hassan auren Sajeeda.

       Lkcn biki yayi akasha biki.



        *_Hussaina Ubandiya_*

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now