41-43

861 55 0
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

      Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

  *MssHussaynah@wattpad.*

     

     4⃣1⃣ ➡ 4⃣3⃣



*karfe 3:50pm* Baffa ya iso,duk da gajiyar dake tattare dashi 5:00pm  yayi kiran duka yan gidan zuwa parlorn shi dan aji shawarar da Zaynah ta yanke.

     Sbd yana so ayi komai a gabansu Anty Beelki.

     Hussein ne ya bude taron da addu'a sannan Baffa yayi ma Allah godiar dawo dashi lfy.

    Ya d'ora da fadin"kamar yanda nace a baya ke Zaynah na baki lkc kiyi tunani,

na kuma yi miki alqawarin duk abunda kike so shi zan yi miki dan haka muna saurarenki, shin kin yarda da auren d'an uwanki ko kuwa shi wancan d'in kike so?"

    Kafin ta amsa Rayyan yace "Baffa ina ganin ba amfanin ma a tsaya tambayarta danni a yanxu Salmah nake so,ita zan aura"

   Tsabar farin ciki su Ummie dasu Anty kamar hadin baki sukace "Allahu Akbar Alhamdulillah"

      Baffa ne yace "toh Alhamdulillah abu yayi kyau shikenan gsky nayi matukar farin ciki da jin haka abu yazo cikin sauki toh madallah"

     "Alhamdulillah kinso ki kunya tamu Allah ya nuna miki ya fiki" inji Ummie tana kallon Zaynah.

  Baffa ne yace  "Haba Fateema wacce irin mgn ce haka? Bana son sake jin makamanciyar shi a gidan nan"

    "Toh inshaa Allahu Alhaji baxan k'ara ba" Ummie ta fad'a.

    "Yauwa, sai dai inada sharad'i d'aya Zaynah kina jina?"

       "Eh Baffa"

    "Zan sa ayi min bincike akan halayyar shi wanda kike so,zan bashi aurenki ne idan har yanada aiki sannan baya shaye2, baya sata da bin mata.

    Indai baya yin ko d'aya daga cikin abubuwan dana lissafa toh nayi alqawarin bashi aurenki"

     "Toh ngd Baffa" ta fada daga nan ta tashi da niyyar komawa part din Ummie.

    Cikin d'aga murya Ummie tace "ke Ina xuwa? Badai sashe na ba? Tun wuri kisan inda dare yayi miki tunda ban isa dake ba"

     "Mamie ne tace "d'adin abun bake k'adai keda sashe ba, Zaynah maza tafi nawa sashen anjima su yan biyu su kwaso miki kayanki kinji"

Kunya ne ya lullub'e Zaynah jin Mamie batayi fushi da ita ba,nan take wata zuciya ta raya mata cewa ba tayi ma kanta adalci ba sai kuma tayi saurin watsi da tunanin har ta qarasa part d'in Mamie.

      D'akin ya Hafsy na da nan ta shiga ta kwanta dan tana kyautata zaton nanne zai koma d'akinta.

      Hassan ya rufe taron da addu'a sannan suka watse.

    Baffa ya umurce duk matan auren su koma gidajensu bayan ya basu tsarabarsu dana 'ya'yansu.

       Na sokoto suka kama hanya itama Hafsat ta kama hanyar gidanta.

   
Dama duk basu zo da yaransu ba.


*Bayan wasu kwanaki*

    

Baffa yasa a bincika masa halayyar Majeed,kuma ba'a samesa da dukkan abubuwanda Baffa ya lissafa ba sai dai an shaida masa yaran gidan basu da tarbiya duk da an b'oye masa mahaifinsu na shaye2.

     A ranar da Baffa ya samu lbrn ya qara tara iyalansa amma bada masu aure ba, ya sanar dasu halin da ake ciki ya kuma qara tambayar Zaynah har yanxu tana son Majeed tace eh.

        Saboda sanin muhimmancin alqawari kawai yasa Baffa zai ba Majeed auren Zaynah.

     Amma ya bata sharad'in sai ta fara aiki sannan zata aureshi i.e  approximately shekara daya da rabi.

    Kuma ta yarda, da Baffa ya tambayi Rayyan ko za'a fara yin nasu ne? Yace a'a yafi so a hada gaba d'aya.

      Toh sai muyi fatan Allah ya kaimu lkcn.

      Hussein ma ya gabatar ma Baffa da mgnr aurenshi kuma yana sone a hada dana su Rayyan.

      Wata d'iyar kawar Mamiensu yake so Khairat.

     Aka tambaye Hassan shifa? Yace bai tashi ba tukunna.

   An aje akan ranar da Majeed ya turo ranar za'a tura gidansu Khairat.

 

 
       *_H.N.Ubandiya_*

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now