20-22

904 53 2
                                    

©Exզʊɨsɨtɛ Oռʟɨռɛ Wʀɨtɛʀs.
💜💜💜💜💜💜
                    💜💜
    💜💜💜💜💜💜
                     💜💜

            👫

  Naɖaʍaʀ  Aʊʀɛռa.

Wʀɨttɛռ ɮʏ: Hʊssaɨռa Nasɨʀ Uɮaռɖɨʏa.

  Eɖɨtɛɖ ɮʏ: Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

      Iռ ʋɛռɛʀatɨօռ tօ Lʊɮռa Sʊʄʏaռ.

  *MssHussaynah@wattpad.*

            2⃣0⃣ ➡ 2⃣2⃣

A haka rayuwa ya cigaba da tafiya a kullum kara jin son Majeed Zaynah keyi sai dai tun daga ranar da ta kirashi a gabansu Jidda bata kara kiransa ba.

  Kuma bata jin haushin Majeed ko kadan aka abunda yayi mata a waya sbd tasan Allah ne ya kamata daya jarabceta da son Majeed dan tasha yima maza abunda yafi wannan. 

   A bangaren Majeed shima tun ranar da ya taimaka ma Zaynah Allah ya dora masa sonta sai dai yasan tafi karfinshi idan akayi la'akari da gidajen da suka fito,

   Ya fito daga gidan Buba tsohon soja(Buba nanaye) wanda a sojan ma kurtu ne kurtun kuma da aka kora ba wai retire yayi ba.

   Ita kuma diyace ga tsohon minister of transport jika ga mai garin dakin gari.

 
   Yana zaune a office dinshi ga scripts na students a gabanshi bisa ga dukkan alamu test ne yake marking.

   Lecturer Saifullah ya shigo tare da sallama (lecturer Saifullah aminin Majeed ne,Majeed bai da wani aboki bayanshi)

   Amsa sallamar Majeed yayi tare da mik'a ma Saifullah hannu sukayi musabiha.

  Sannan Saifullah ya zauna yana mai fadin "ka kira kace nazo akwai mgn"

   "Eh Wato akwai wani abu dake matukar damuna Saifu ina bukatar ka taimaka min da shawara pls"

  "Ehem ina sauraranka meye damuwar taka?" Saifullah ya tambaya.

   Nan Majeed ya fadi masa komai tun daga ranar da ya taimaki Zaynah har izuwa kiransa da tayi sau biyu.

    Numfasawa Saifullah yayi sannan yace"idan na fahimceka Majeed kana sone ka fada min kana son yarinyar amma ka kasa fadi mata koh?

  Majeed yace "eh, a'a"

   "Bangane eh a'a ba kayi min bayani yadda zan fahimta sosai"Saifullah ya fada cike da kosawar son jin mgnr.

   "Dalilin dayasa nace eh,a'a shine, eh na nufin ina sonta, a'a kuma danace na nufin bawai kasa sanar da ita bane matsalar Saifu"

   "Ina jinka meye matsalar?" Saifullah ya tambaya.

"Na farko kaga ita diyar masu hali ne ni kuma talaka, na biyu kasan ni banason wulakanci, kar inxo na fada mata ta wulakantani" Majeed ya fada yana mai kallon Saifullah.

  Dan buga kafadar Majeed Saifullah yayi yace "kai duk wa'innan ba abun damuwa bane, duba ga lbrn daka bani alamu sun nuna itama yarinyar ta kamu idan ko haka ne kaga ba zancen wulakanci, kuma idan tana sonka ba ruwanta da talaucinka"

   Kallon rashin fahimta Majeed yayi ma Saifullah yace "bangane ta kamu ba?"

    Dariya Saifullah yayi yace "dayake a soyayya kai novice ne shiyasa baka gane ba, toh ina nufin itama tana sonka"

  "Allah koh? Toh yanzu meye abunyi?" Inji Majeed.

   Saifullah yace "ba kace ta kiraka sau biyu ba?"

    "Eh"Majeed ya amsa.

   "Toh kiranta zakayi ku gaisa sannan ka kora mata bayani, kar fa kayi jinkiri kasan a bari ya huce kan kawo rabon wani"

  "Hmm nifa bazan ce ina sonta ba"

   "Toh ai shikenan ni meye nawa? Kaga sai anjima, shawara ka nema na kuma baka ni na tafi" Saifullah ya fada tare da ficewa daga office din.

***

    A daren ranar 9:10pm Majeed ya yanke shawarar kiran Zaynah..................



          😴😴😴 *bacci sai kuma Allah ya kaimu gobe*


          *_HOMEL_*

NADAMAR AURENAWhere stories live. Discover now