TAWA KADDARAR 2

2.2K 105 7
                                    

💧💧 *TAWA K'ADDARAR....💥*

💥

*HASKE WRITER'S ASSO💡*
(Home of expert & perfect writers)

*NA FEEDOM*💞

*Bestowed to Aunty Sis💕*


*02*

Banza ya mata ya cigaba da driving dinshi cikin natsuwa yayin da Anup tayi lamo a jikinshi tare da zagaye shi da hannunta tana zare idanu......

A Haka suka isa Nigerian Turkish Nizamiye Hospital plot 133 Sector S.Candastral Zone Abuja.......Ya shiga har ciki kusa da Central EM Sannan yayi parking a Parking space d'in ya saka hannunshi ya janyeta daga jikinshi tare da dungure mata kai ......Kara ta saki tana harba kafafuwa sannan ta koma rungumeshi taki saki!zama sukayi a motar shiru sannan ya dan kalleta ya kau da kai ya dauki wayarshi yayi dialing number "Soul......"

Tana dauka cikin kwantar da murya yace "Madam muna jiranki fa......"Daga yarda yayi maganar zaka gane tsantsar kaunar dake tsakaninsu ......

Yana jin lokacin da Anup ta kwaikwayeshi tana turo baki tare da wurga idanu kasa kasa ......
Dariya yayi kasa kasa Sannan ya yanke wayar yana kallon Anup da ta dago kanta tana kallonshi !Hararan ta yayi yana fad'in "Ba ruwana da Anup......"

Tayi rau rau da idanu tace "Sorry ......"

Tab'e baki yayi ya bude motar ya fita hango wata kyakykyawar Mata ta nufosu cikin shigar likitoci da katon ciki a gabanta wanda yayi mata masifar kyau......

Har ta iso kusa dashi tana sakar mashi tsadaddan murmushi a fuskarta ba tare da yayi magana ba ya bude mata bayan motar tare da ja baya kad'an ta shiga ta zauna tana aika mashi da kallo na musamman......

Sae da ya tashi motar sannan ta kalleshi cikin kulawa tace "Yau ma gudowa kayi office ko ......?

Ta cikin madubi ya kalleta tare da kashe mata Ido ba tare da yayi magana ba ya nuna mata Anup da ke tallabe da kumatu ta turo baki ......

Matsowa tayi jikin kujeran sossae tana kallonta tace "Anup ba magana ko......?

Ta K'asan ido ta hararin Ummi din sannan ta turo baki tana waro manyan idanunta ......

Yar dariya tayi tace "Wa ya taba man Anup dinta ......Kaine ko Oga?ta karashe maganar tana kallonshi ......

Harara ta sakar mata tana fad'in "Ko shine d'in me zaki mashi Ummi?Sae na fad'a maki abunda ya man sannan ki koma bayanshi ......"

Dariya sukayi baki daya banda Anup dake ta faman mazurai ......Sannan Ummi tace "Fad'a man Anup wannan karan bayanki nake kin ji ko......"

A Takaice tace "2nd position nayi shine Dad yace na 32 nayi ......"

Bude baki yayi yana kallonta sannan yace "Anup baki da kunyar karya ko?
Turo baki tayi tace "To ba kai kace nayo maka na age dinka ba!kuma na taimaka na fidda ka kunya nayo ka dakeni ......"

Itakam Ummi dariya tayi tace "Kenan dai na ages dinshi kika yo......?
Ta Washe baki tana gyada kai ......
"Anya Anup ba asarar school fees muke ba?Ummi ta tambaya tana kokarin daure Fuska ......

Baki daya Anup ta juyo tana kallonta kafin ta bare baki ta fara kukan da babu ko digon hawaye a ciki sai azabar kara......

【】

"Uncle Jawwad......"
Sae da ya hadiye lomar sakwaran da ya kai baki sannan ya dago yana fad'in "Ya akai Fadila......?
"Ina zaka je yanzu ......?ta fada kamar mai rad'a
Shima kasa yayi da Murya yana jefa mata harara sannan yace "In da kika aikeni......"

"Allah ya baka hakuri !dan Allah idan gidansu Anup zaka ka tafi dani......"ta karashe maganar tare da langwabe kai ......

Hararan ya sake jefa mata sannan yace "Idan ba can zan je ba fa?
Shiru tayi tana kallonshi!Ya juyar da kai ya cigaba da cin abincinshi har ya koshi sannan ya mike ya barta ......Upstair ya nufa yayin da ta shiga part din dake gefen kallon falon ......
Dattijuwa ce mai matsakaicin shekaru sanye da medical glass tana duba wani katon littafin na Anotomy......
Kusa da ita ta zauna tayi rau rau da ido tana fad'in "Granny dan Allah kiwa Uncle Jawwad magana ya kaini gidansu Anup yau......"

Kallonta tayi na yan mintina sannan ta gyada kai a hankali tace "Je ki ce ya tafi dake ......"
Rungumeta tayi tare da sakin dariya tana fadin "Thanks......"Sannan ta kwasa da gudu ta nufi Upstair din ......Duk kyarmarta a bakin kofa ta tsaya tana knocking yayin da ta kasa tsayar da kafufunta guri daya ......

Sae da ya gama saka kaya ya dauki keys da wayarshi sannan ya bude kofar yana kallon kafufunta da ta kasa tsayarwa ......
"Uncle Jawwad Granny......"
"Shiiiii Stand clearly sae ki man magana tukun ......" ya fada yana sake mata harara ......
Dakyar ta tsayar da kafufunta sannan ta mayar da numfashi tana fadin "Granny tace ka kaini gidansu Anup......"

Harara ya sakar mata "Anup ko Jawahir?
Kamar tayi kuka tace "Jawahir Dad dinta ya saka mata ......"
"Oh......" ya fad'a yayi gaba abunshi ......
Rakashi tayi da harara sannan ta shiga part din Granny ta dauko hijab ta iskeshi a cikin mota !Bayan motar ta bude ta shiga don tasan k'a'idarshi ba'a zaman mashi a gaban mota sannan dole idan anje gurin mutane ka duk'e k'asa kada ace drivernka ne ......

Har cikin gidan ya shigar da Motarshi yayin da ya bude ya fito ya barta !Juyawar da zaiyi yaji saukar Ball a saman fuskarshi ......
Ya tsayar da Idanunshi ga Anup da ta biyo ball din da gudu ba tare da tasan ta sameshi ba......

Sae da tazo kusa dashi sannan taja ta tsaya tare da waro mashi manyan idanunta tana rawa da kafafunta ......
Tana Hango Fadila ta zagayeshi da gudu ta nufi gurin Fadilan amman ya saka hannu ya janyota ta dawo gabanshi !Dafe kirjinta tayi kafin ta duk'a da sauri k'asa tana fad'in "Good Afternoon Uncle Jawwad......"

Harara ya sakar mata tare da kallon Ball din da ta fad'a cikin flowers din dake gefe yace "Waye ya jeho wancan ball din......"

Waro Ido tayi Sae lokacin ta lura da sahun ball din dake fuskarshi !ta mike da sauri tana jujjuya kafafunta tace "Na rantse maka ba ni bace "
Kafafunta ya kalla tayi saurin matsesu guri guda kafin ta k'ara yin k'asa tace "Uncle Jawwad na yafe maka dukan da kan a School ......"

Gyad'a kai yayi yana fad'in "Oh......"
Ta Kare washe baki tace "Sannan na yafe maka seizing da ka man ......"
Tsuke baki yayi yace "Hun......"
Cigaba da daga mashi gira tayi tana rawa da kafafunta kafin ta shammace shi ta fizgi hannun Fadila ta k'wasa da gudu cikin gidan ......

Dariya yayi mai sauti tare da shafar sajenshi sannan ya bi bayansu ......Lokacin da ya shiga falon basu ciki ya tabbata da d'akinta ta shige kai tsaye ya bita dak'in ya iske sun shige cikin bargo sun lullube suna mayar da numfashi......
A Hankali ya taka har inda suke ya fizge bargon ya jefar sannan ya ware hannayenshi yana fad'in "Kowa ya yafe komae Jawahir......"

Wawan tsalle ta yi ta fad'a a jikinshi tare da sakin k'ara ta kankameshi ......
Sun dade a haka sannan ya d'ago ta yana kallon Fadila da ta duk'ufa tana gyara wayar wasan da Anup ta watso lokacin da ta rungumeshi ......
Hannu ya mika mata yana fad'in "Common......"
Kafin ta taso yaji Muryar Anup na fad'in "Jiya nace God thunder fire you Yau kuma nace God mercy Fire you Uncle Jawwad......"

"Jawahir......"ya fad'a tare da lumshe ido
Muryar Ummi yaji tana kwalawa Anup din kira ta sakeshi ta ruga da gudu tana fad'in " A minus A = Minus 2A......"

*Feedohm*💞

TAWA K'ADDARAR......Where stories live. Discover now