TAWA K'ADDARAR 13

1.3K 80 12
                                    

💧💧 *TAWA K'ADDARAR...*💥
           《K'azamar Rayuwa...》

                     💥

® *HASKE WRITERS ASSO.*💡
_Home of expert & perfect writers_

        *NA FEEDOHM💞*
    *Wattpad:Feedohm11*

   *Bestowed to Aunty Sis💞*


                      *13*

       Cikin tsawa yace "Shut up!Me zaka fad'a yanzu?kun hana amata abunda aka mata ne?ko sae yanzu kake da karfin guiwar hanani daukarta?

  Dr din ya shigo a rud'e yana tambayarshi ina zaya tafi da ita !amma ko kallonsu baiyi ba ya fita ya sakata mota ya bar harabar asibitin!

  Ko asibitin da Granny take bai je ba direct gidansu ya kaita yayin da ya rungumeta yana kuka kamar Karamin yaro!Sister Hafsa ya kira da yake ta kware wajen fannin mata tazo har gida tayi treating dinta……

  Sae kusan karfe 8 na dare sannan su Granny da hajiya suka dawo gidan!Baffa kam da Alhajinsu Jawwad da ya iso daga cairo gidansu Anup suka koma wurin mutanen da suka baro, sam gidan baya da maraba da kango komae ya cinye idan ka d'auke d'akin maigadi da wutar bata tab'a ba ...

   Lokacin da suka shiga d'akin da Jawwad suke ko kallonsu baiyi ba yana zaune bisa abun sallah sae Fadila dake zaune gefen gadon ta hade kai da guiwa tana kuka!Sae da yaga Hajiya ta nufi gurin Anup sannan ya mike cikin tsawa yace "Karku sake ku taba ta!

  Cak ta tsaya tana kallonshi idonta cike da hawaye yayin ta koma tayi zaman dirshan ta saki kuka...

  Itam granny kukan ta saki ta matsa kusa dashi tana fad'in " Jawwad mu kake wa tsawa akan abunda Allah ya kaddara?

  A Hankali ya juya mata baya kamar karamin yaro ya fashe da kuka yana fad'in " Me yasa kuka barta ta fita?

  Muryar Anup suka ji tana fad'in "Ummi!Ummi……
  Da sauri ya matsa kusa da ita ya rike hannunta yana girgizata ……
  A Hankali ta bude idanunta sukayi jawur ta daura a fuskarshi!wata razannar kara ta saki ta fincike hannun tana fad'in "Bana so!Ka daina da zafi!Ummi……

  "JAWAHIR !Ya kira sunan a rud'e yayin dasu hajiya suka zagayeta...

Sake bude idon tayi a karo na biyu ta k'urawa Uncle Jawwad din ido sannan ta mike da sauri ta rungumeshi tana kuka " Uncle Jawwad Ummina Dan Allah ka fad'a man ina Ummina suke?ina suke ko da gaskene sun kone?naji wani na fad'in duk sun rasu kenan baran sake ganinsu ba Uncle?me yasa ni ban rasu bane?

   Rungumeta yayi sosae yayin da shima ya saki kuka da karfi yana girgiza mata kai...Sam bai da sauran kalmar da zai hanata kuka…
Ina ma zaya iya maido da baya gaba!

*AFTER 1 MONTH*

  Dafa kanta yayi yana kallonta tayi wani fayau ta k'ara haske kamar ba ita ba yayin da lips dinta suka bushe sukayi wani haske kamar ta shafa faran k'asa a sama, Sae kumburin da cikinta yayi kamar an kifa kwarya, Cikin sanyin murya ya kira sunanta "Jawahir"

  Tar ta bude idonta tana kallonshi kafin ta mayar dasu ta lumshe hawaye su gangaro ta gefen kunnenta a hankali tace " Har yanzu ina kallonsu Uncle Jawwad kuma ina sonsu ji nake kamar idan na bude idona zan gansu...ku tayani addu'a su dawo dan Allah"

  Share mata hawayen yayi yana girgiza mata kai yace " Bazan maki karya ba Jawahir amma duk wanda ya rasu bara ya dawo ba"

  Murmushi tayi idanunta na rufe wanda ko ba'a fad'a ba kasan na bakin cikine tace "Na sani Uncle Jawwad ko lokacin da Abban fadila ya rasu Dad ya fad'a man ba'a dawowa kawae ina so nayita kiran sunansu da dawowa ina jin dad'i…"

TAWA K'ADDARAR......Where stories live. Discover now