💧💧 *TAWA K'ADDARAR...*💥
《K'azamar Rayuwa》💥
® *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writers_*NA FEEDOHM💞*
*Wattpad:Feedohm11**Bestowed to Aunty Sis*💕
*22*Murmushi yayi ya juya ya bar room din ya shige motarshi!direct address din da aka bashi ya bi ya isa kofar gidansu Uncle Jawwad yayi parking bakin wani icce dake nesa kadan da gidan, Iska ya furzar yana tunanin madafa shin ya jira har yarinyar ta fito ya dauketa ne koko ya shiga har cikin gidan ya daukota...Dariya ya saki shi kadae ya shafi sajenshi yace "Kamar wawaye da zan daukar masu yarinya su barni suna kallona "
Bude motar yayi ya fito ya jingina ganin an bude gate din gidan mota na shirin fitowa ya k'arasawa kusa da gate din har motar ta fita sannan ya matsa kusa da maigadin ya mika mashi hannu cikin fara'a suka gaisa sannan yace "Nan ne gidansu Jawahir ko?
Gyad'a kai yayi yace "Eh Allah ya sa lafiya"
Murmushi ya mashi yana fad'in "Lafiya lau malamin makarantarsu ne shine na biyo na dubata "
Washe baki Mai gadin jin an fad'i Jawahir don ba karamin so yake mata ba yace " Uwar dakina mai kwashe kwashe, ai kuwa kayi rashin sa'a jiya nan kakanta ya zo ya dauketa suka tafi zaria tana kuka tana ihu "
Dafe kai yayi yana hade lips dinshi yace "Yaushe zata dawo kenan?Wangale baki ya kuma yi yana kallon Jawwad da ya fito da sassarfa sannan yace "Ga mai amsa wannan tambayar can Shine Ubanta Shine Uwarta...!
Gurin da yake kallo Deebo ya kalla, ya k'urawa Jawwad ido da ke takowa cikin mazantaka da isa har ya k'araso ya mika mashi hannu yana kallonshi cike da neman karin bayani...
Kwarjini sosae Jawwad ya mashi amma da yake dan duniya ne sae ya dake ya sake kankame hannunshi yana murmushi...
Shi kam Jawwad murmushin yak'e yayi ya dubeshi sosae yace "Bismillah ka shiga ciki... "
Spreading arms yayi yace "No dama Jawahir na zo gani ko tana nan?
Kallonshi yayi na yan mintina sannan yace "Daga ina?
Kai tsaye yace "Daga School din su ""School?ya maimaita yana jinjinawa kafin yace "Ban gane ka ba...!
Murmushi yayi yace "Englishi Teacher din su ne"
"No...!ya fad'a kai tsaye
Shiru Deebo yayi kafin ya saki murmushi na yan duniya yace "Ban dad'e da fara aiki ba anan may be shi yasa baka sanni ba...Amma ita Jawahir d'in ta sanni "
Juyawa yayi ba tare da yace komae ba ya fiddo wayarshi dake ringing ya katse kiran ganin Hajiya ce sannan ya sake dialing ya juyo yace "Bata nan "a takaice
Granny ta fito a rud'e ita da Fadila tana k'wala mashi kira, su duka suka juya suna kallonta har ta k'araso gurin tana fad'in "Jawwad ka dauko mota mu tafi ..."
A rud'e yace "Ina?
Cikin rud'u tace "Yanzu hajiya ta kirani a news suka ga su Anup sunyi accident ana cigijyarsu..." Ita kanta bata san lokacin da ta fad'a ba sae da taga Jawwad zaune a k'asa sannan ta saki kuka tayi kanshi...
Kuka ya saki tare da dakatar da granny, Deebo kam ajiyar zuciya ya saki ya fita da sauri ya janyo motarshi ya zo da ita yace su Granny su shiga ya kaisu tunda Jawwad din bara ya iya driving ba, Cikin tashin hankali ta kama Jawwad ta saka a motar Deebo sannan ta shiga ita da Fadila ya ja motar a guje ya bar unguwar cikin ladabi yace "Ina zamu je hajiya?
Kallon Jawwad tayi da ya jinjina kamar mutun mutimi sannan ta share hawayen da suka zubo mata tana rike da hannun Fadila dake kuka kamar ta sik'e ta mashi kwatancen gidan hajiya...
Cikin mintina kad'an ya isa yayin da suka ga su Hajiyar sun fito da mota suna jiran zuwansu ko wane cike da tashin hankali Hannun Jawwad ta kama ya fizge da sauri tare da fiddo Atm dinshi ya mikawa Deebo murya a sarke yace "Ka dauki ko nawa kake so ka kaini gurin Jawahir dan girman Allah...!
Juyowa yayi yana kallonshi, ganin hawaye kwance a fuskarshi ya sashi guntse dariyar dake niyar sub'uce mashi "Akan mace yake kuka stupid..."ya fad'a a ranshi amma a fili cewa yayi "She's my student ba sae an biyani ba..."
Shiru ya masa yana jin lokacin da granny ta dawo tace ya fito amma ya mata banza Deebo d'inne yace mata shi zai kaisu...
"Tana kaduna fa...Jawwad ka fito dan Allah "Ta fad'a idonta cike da hawaye...
Maida idonshi yayi ya lumshe ba tare da yace mata komae ba, tana da tabbacin in zata kwana tana mashi magana bara ya kulata ba a yanayin da yake !don haka suka shiga motar Deebo su duka har da Hajiya da Abban...
Sae da ya biya gidan mai yayi full tank sannan ya dauki hanya cikin matsiyacin gudunshi kamar kullun...
Ana isha'i suka isa asibitin ko gama parking ba'ayi ba ya fito ,Asibitin ya bi da kallo tar da ita kamar rana sanadin farin kwan lantarkin dake zagaye da ita ...Inda ya hangi yan sanda ya nufa don ya tabbata anan suke yana zuwa suka gane ko waye saboda Tshirt da wandon dake jikinshi na aiki ne, a hankali yace "Suna ina?
Ko bai masu bayani ba yanayinshi zai gamsar dasu wa yake nufi,Lokacin su granny suka iso a tare aka masu jagora har zuwa inda mutanen suke, gawawwakin aka fara budewa masu ganin yarda gawawwakin suke ya k'ara ta yar masu hankali hajiya ta juya ta bar gurin tana fad'in "Shikenan Jawahir kema na rasaki..."
Har aka gama bud'e gawar babu ta Jawahir da Baffa sannan Dpo din yace "Da akwae mutun hudu da basu rasu ba suna AE na treating nasu...!
Bai ce komae ba ya juya yana duba YKS din asitin yayin da Deebo ke take mashi baya har ya isa inda aka rubuta AE sannan ya tsaya!Ta glass din ya hango Baffa dake nad'e da bandage sae Anup a kusa da gadonshi sae sauran mutanen biyu ko wane kwance ...Hawaye suka gangaro mashi a kumatunshi yayin da ya kutsa kai cikin d'akin ba tare da ya kula nurses din dake neman dakatar dashi ba...
Deebo ma binshi yayi a baya sab'anin su granny da aka dakatar, A bakin gadon ya tsaya ya k'ura mata ido yana kallonta, wani d'an sanyi sanyi ya ji ganin babu wani rauni a jikinta sae digon jini shima kad'a a hancinta! lumshe Ido yayi yana kallon hawayen dake silalowa a gefen kunnenta , Ahankali ya duka bakin gadon ya ruko hannunta dake sanye da drip ya matse a nashi tare da daura kanshi a sama...
Karo na farko a rayuwar Deebo kenan da ya fara jin tausayin wani a duniya!dafa kafad'ar Jawwad yayi yana kallonsu a sanyaye......
Shigowar Doctor ce ta sa Deebo fita daga d'akin ya koma yana hangensu ta glass kamar yarda sauran suke...
Dafashi Dr yayi ya d'ago shi yana fad'in "Please kayi hakuri ka dan jiramu a waje...!
Bai musa ba ya fita a sanyaye ya had'e kai da wall d'in yana fitar da numfashi,Abba ya matso ya dafashi kamar jira yake ya saki kuka yana fad'in "Ta ce bara taje ba Abba!Me yasa granny ta kafe sae ta je?
"Kaddara Jawwad...!Abban ya fad'a cikin sarkewar murya
Rungumeshi Abban yayi yana tapping bayanshi har Dr ya fito sannan Abban ya bi bayanshi bayan ya zaunar da Jawwad a kujerun dake corner din...
Office suka shiga Dr din ya fito da files din dake dauke da photon brain d'in Jawahir ya aje saman tebur sannan yace "Su waye patient dinku a ciki?ko ita kadae ce...?
Girgiza mashi kai yayi ya fad'a mashi sunan Baffa sannan ya fito da file din Baffan ya aje kusa da na Jawahir din!
Cikin natsuwa yace "Shi na mijin ya samu karaya uku a hannunshi na haggu da kuma biyu a kafarshi ta haggun sae tsagewar kashin cinya a kafar dama, Wannan ba matsala bace mun rigaya mun mashi duk abunda ya dace in sha Allahu zai samu sauki a hankali......!
"Ita dayar fa?Abba ya tambaya cikin k'osawa
A Hankali yace "Ita macen bata da wani rauni a jikinta sae dae external injury da ta samu a brain dinta haka ya sa mata amnesia sanadin buguwar da kanta yayi...!
"Amnesia?What's...?Abban ya fada cikin rudani...
Ajiyar zuciya ya saki sannan yace "Memory loss...!
"Right time......!Deebo ya fad'a dake jingine jikin window yana jinsu...
![](https://img.wattpad.com/cover/131794494-288-k314378.jpg)
YOU ARE READING
TAWA K'ADDARAR......
RomansaLabari ne na wata Yarinya da ta tashi cikin gata da kulawar iyayenta lokaci guda duniyar ta juya mata yayin da ta hadu Kaddara ta rasa dukkan iyayenta Sanadiyyar gobar da ta cinyesu harda karamar kanwarta !ta dimauce ta rasa duk wani tunaninta!Ta ra...