[4:20PM, 2/1/2018] Feedohm💧: 💧💧 *TAWA K'ADDARAR...*💥
《K'azamar Rayuwa》
💥
® *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writers_
_*NA*_
*_FEEDOHM💞_*
*Bestowed to Aunty Sis*💕
*20*
Ya dad'e kwance yana juyi yayin da zuciyarshi ta shiga tunani daban daban,abunda yafi tsaya mashi rai zancen yarinyar da zai dauko yau sam zuwanshi gidan Umma bai shafeshi ba saboda yasan dole yaje donshi kanshi yayi missing Umman tashi Lumshe ido yayi a hankali ya shafi gefen fuskarshi "JAWAHIR ALMUSTAPHA" ya fad'a a fili tare da ware idonshi saman picture dinta dake aje gefen bed dinshi, Dafe kanshi yayi lokaci guda tare da daukar wayarshi yayi dialing number Alhaji Sanda ringing d'aya ya dauka yana kira "What's wrong Deebo?ba dai har kaje Abujan ba?
"Manta da Abuja...Idan na dauko yarinyar me zaku yi da ita?ya fad'a kai tsaye yana lumshe idonshi
Dariya Alhaji Sandan yayi yace "Na fad'a maka Deebo ina son yarinyar ne ko!Wae meye matsalar?Idan ma naga zan iya zan Raineta har ta girma na aureta...!
Dariya ya saki k'asa k'asa sannan ya yanke wayar yana fad'in "You're Sick..."
Wanka ya shiga minti goma ya fito daure da towel ya dad'e gaban mirrow yana shafe shafe kamar mace sannan ya saka kaya kanana ya fise urare ya bud'e fridge ya dauko kwalbar wine ya koma gefen gado ya zauna ya tultula a glass cup ya kafa kai sae da yasha mai isarshi sannan ya tsallake ya fita daga dakin......
Dad ya samu part dinshi yana kwance saman carpet da karan cigarree a bakinshi kusa dashi ya zauna yace mashi "Zamu je gurin Umma yanzu"
Kai tsaye Dad yace "You're Mad Farouk...Abujan fa?Uban wa zai je maka ita ko kana nufin Ummarka ta fi aikena?
Dariya yayi mai sauti har da girgiza kai sannan yace "Ina sonka dad baka tab'a statement ba tare da ka bayar da amsarshi ba...!
Harara ya dalla mashi tare da wurgo mashi wata envelope yana fad'in "Abuja zaka Farouk!Ga kudi nan zasu isheka komae na rayuwa kafin ka dawo sannan Alhaji sanda ya tura maka 500k account dinka...!
Ya tab'e baki yace "Tun dazu dad ka bawa kanka amsa fa,taya zaka wahalar da kanka bayan kasan Umman mu ta fi aiken ku...!
Murya k'asa k'asa dad yace "Kudi Deebo...Naira nawa zamu samu akan yarinyar idan mun fitar da ita?bawae zan barwa Alhaji sanda ita ba aa nasan yarda zanyi dashi "
Lumshe ido yayi ya masa banza kafin ya mike ya jarbi Envelop din yana fad'in "Zanje gurin Umma sannan zan je Abujan Dad duk a yau hope ya maka?
Gyad'a mashi kai yayi sannan ya fita ya samu har Jameela ta shirya ta tsaya tana gayar da sabuwar Auntyn su...Gaba yayi ta bi bayanshi suka shiga mota suka dauki Hanyar gidan Umman......
Suna shiga a compund sukayi parking mijin Umman suka hanga ya fito daga Part din kishiyoyinta da yake part uku ne a ciki Jameela tayi gaggawar matsawa ta gaidashi ya amsa mata cikin sakin fuska da yake yasan ko su wanene sab'anin Deebo da ya aika mashi da kallon tsana yayi gaba abunshi...Mijin Umman ya matso tare da mikawa Farouk hannu yana fad'in "Yau a gidanmu Farouk ko dae b'atan hanya kayi?
Tabe baki yayi yace "Huh...!Sannan yayi gaba abunshi yayin da jameela ta bi bayanshi tana hararanshi k'asa k'asa cike da jin haushin d'abi'unshi a babban falo suka iske Umman tana gyaran farce ta bisu da kallon jin dadi yayin da jameela ta zube a jikinta tana dariya,Deebo kam kujera ya kama ya zauna yana girgiza kafa kafin yayi kasa da kai yace "Ummanmu ...!
YOU ARE READING
TAWA K'ADDARAR......
RomanceLabari ne na wata Yarinya da ta tashi cikin gata da kulawar iyayenta lokaci guda duniyar ta juya mata yayin da ta hadu Kaddara ta rasa dukkan iyayenta Sanadiyyar gobar da ta cinyesu harda karamar kanwarta !ta dimauce ta rasa duk wani tunaninta!Ta ra...
