TAWA K'ADDARAR 9

1.3K 77 18
                                    

💧💧 *TAWA K'ADDARAR....💥*
        《K'azamar Rayuwa...》
                      💥

® *HASKE WRITER'S ASSO💡*
(Home of expert & perfect writers)

     *NA FEEDOM*💞
   *Wattpad:Feedohm11*

     *Bestowed to Aunty Sis💕*

           
                     *09*

  *I have the most awesome Fans.It's such an incredible feeling to meet people from all over the world and have them give me so much love and support!One of the things that has been really great is all of the amazing Comments!I Love it!Thank you so Munch……*❣

   Gyada k'ai tayi ta matsa kusa da Lil dake ta faman washe baki ta mata kiss a goshi tare da zazzage school bag dinta ta fiddo da sweet da biscuit d'in da ta sawo ta bude……

  "Ummi ga tsaraban Lil Sis……"

Murmushi Ummi tayi tace "To sae ki cinye mata ko ?

  Gyad'a kai tayi tana d'aga gira sannan ta kai biscuit din bakin Lil sis ta dora mata a baki ta ciro ta cinye abunta……

   A Haka ta cinye tsarabar tas wanda dama ita ke cin kayanta……

  Knocking din da suka ji ya sata mikewa da sauri ta nufi door din da gudu tana tambayar "Who is knocking?

  Daga waje aka ce "Anup……"

Waro ido tayi tana kallon Ummi "Ummi Aunty gloria……"

  Murmushi Ummi tayi tana fadin "To Bud'e masu ko?

Ta Make kafad'a tace " No sae na masu register……Yarda suke mana a school zan rama……"

  Da karfi tace "Gloria Salamu!Abbah Alhassan!Bisi Bolo……"

  Knocking Uncle Bisi ya sake yi jin tana k'wala masu kira harda sunayen ubansu……

Ummi ta mike ta nufi Kofar ta sake mata rankwashi tare da bud'e masu kofar……

Da sauri Anup ta rungume kowa banda Aunty gloria da Uncle Hasan mai masu Drawing…Cikin falon suka zauna!Cikin girmamawa Ummi ta karb'esu ta dauk'o masu drinks ta zubawa kowa a cup!Uncle Abba ya karb'i Lil Sis yana tambayar Ummi ya jikinta……

  Anup kam kusa da Uncle hassan ta matsa tace "Uncle hassan wa ya gayyatoka?

  Murmushi yayi a sanyaye yace "Jawahir kenan……"

Waro ido tayi tana fad'in "Ni Jawahir na gayyatoka gidanmu? ka fad'i gaskia ka zo shan lemu ne kai dai……!

   Ummi ta daka mata tsawa ganin abun nata na neman wuce kima……

Bata fasa tambayarsa ba "Wae kai ake cewa birin bakin gate ko?

  Kamar had'in baki duka teachers din suka dafe kai yayin da shi kuma yayi murmushin yak'e ya mike yana fad'in "Allah ya bata lafiya……"

  Jiki a sanyaye suka mike yayin da Ummi ta janyota ta tsinka mata mari Uncle Abba ya janyeta yana bawa Ummi Hakuri wae yarinta ce……

  Haka suka shiga staffbus din babu wanda yayi magana !Uncle hassan kam alwashi yaci sae ya ci uban Anup gobe a school……Da yake Uncle Hassan ake fara saukewa!yana sauka duka bus din suka kwashe da dariya suna maimaita birin bakin gate……

*Next morning……*

Bud'e hanci take tana shake warin Gas din dake fitowa daga kitchen!Sannan tayi dak'in Ummi tana k'wala mata kira……Dad ta iske yana jijiiga Lil Sis ta matsa kusa dashi tare da dafa kafadarshi tace "Dady baka jin kamshin Gas?

  Shiru yayi yana nazarin maganarta kafin ya aje Lil Sis ya fita falo ya leka kitchen!karar fitar Gas yaji !ya dawo yana tambayar Ummi ya akai gas ke fita……

  Sae da ta gama sanya earing din da take kokarin sawa sannan ta juyo tace "Bansan me yasa ba!tun jiya yake fita haka……amma anjima bala zaizo ya fita dashi a gyaro……"

  Shiru yayi sannan ya juya yace "Anup ina uniform din da kika saka yanzu?

Kusa da lil sis ta matsa ta sumbaci goshinta tana fad'in "Na fasa zuwa school din"

  Bata rufe baki ba Ummi ta janyota ta mayar mata da rigar uniform tana fad'in "Bani na sakaki rashin ji ba don haka dole ki tafi school……!

  Shiru tayi tana kallon Ummi kafin ta fizge hannunta ta fad'a jikin dad tana fadin "Dad baran je School in ba……!

  Rungumeta yayi yana fadin "Me yasa Anup?Bakya san kiyi karatu ki zama likita irin Umminki?

  A Hankali ta saki kuka tace "Ina so Dad amma yau baran je ba!Dan Allah ka cewa Ummi ta barni na zauna……"

  Dago fuskarta yayi tare da share mata hawayen yana kallonta sannan yayi kissing forehead dinta "Sorry……
   "Dear ki……"
Da sauri Ummi ta daura hannuta saman lips d'inshi tana fad'in "Karka ce ta zauna dan Allah!jiya fa daga teacher dinsu yazo nan ta kirashi birin bakin gate!shine kuma dan bata da kunya yau tace bara ta je ba!Au kenan gobe ta kuma zagin teacher dinta tunda tasan zata zauna gida……"

  Lumshe ido yayi a hankali sannan ya saukesu kan Anup data rike hannun Lil sis da nashi tana kuka a hankali……

Horn din Uncle Jawwad ya sa Ummi daukarta cak tare da tarkacenta ta fita!Kuka take da karfi tana harba kafa yayin da ta rike Kafad'ar Ummi da Hannunta biyu……

    Sae da ta bude motar Uncle Jawwad ta sakata sannan ta suka gaisa ta juya……

  Bude motar Anup tayi ta rungumeta tana kuka kamar ranta zai fita……

  "Zan b'ata maki rai wallahi Jawahir!wani ya saki rashin kunyar da zata hanaki zuwa school?Au kin san baki kyauta ba kenan……"Ummi ta fad'a tare da finciketa daga jikinta …

  Kuka take tana tirje tirje "Ummi dan Allah kiyi hakuri wallahi baran je ba……"

  "Jawwad wae baraka iya dukar man wannan yarinyar bane……"Ummi ta fad'a tana duban Jawwad…

  Hakanan yaji ta bashi tausayin !Takowa yayi a hankali ya d'agata sama ya bude motar ya shiga tare da d'aurata a jikinshi ya had'e hannayenta da take mikawa Ummi guri guda……

  A Hankali Fadila dake gefe ta saki kuka ganin Anup din nayi !Harara ya sakar mata yana fad'in "Rufe man baki……"

  Da yake tasan babu dalilin kukan ya sata kama bakinta tare da janyo hannun Anup da tunda suka fita daga gidan tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta……

  Yana gama parking cikin makarantar ya kira sunanta a hankali "JAWAHIR tashi ku tafi kin ji ko……"

TAWA K'ADDARAR......Where stories live. Discover now