💧💧 *TAWA K'ADDARAR....💥*
💥
*HASKE WRITER'S ASSO💡*
(Home of expert & perfect writers)*NA FEEDOM*💞
*Wattpad:Feedohm11**Bestowed to Aunty Sis💕*
*08*"Sister Ki tattara wa'azinki idan na dawo sae ki man kinji ko……" ya fad'a hade da dafa mata tsakiyar kai……
Murmushi tayi tace "Zanje gidan Bro Abu……"
Kallonta yayi na yan minti sannan yace "Ki kula da kanki!ki saka hijab da Nikab kin ji ko……"
A Hankali ta gyad'a mashi kai ……
Motarshi ya d'auka ya nufi Princess Luxury!Tun kafin ya shiga Room din yake jiyo sautin Waka na fitowa!ya tura kofar a hankali ya rufe ya ware hannayenshi yana jefa mata wani irin kallo……
Tana zaune ta hard'e kafafuwa daga ita sae bra da pant!ta aje Cup din dake hannunta ta tako a hankali ta fad'a kirjinshi tare da lumshe ido……
A Haka har suka isa bakin bed din ya kwantar da ita sannan ya cire kayanshi ya koma daga shi sae boxer fari……
Cikin Whisper tace "Deebo dady na nasan ganin parent in ka……"
Kanne mata ido yayi tare da shafo tsakiyar bayanta yana fad'in " Dadyn mu yana UK da ya dawo zasu zo Baii……"
Lumshe ido tayi ta fara kissing wuyanshi kafin ta gangaro kan bakinshi yayi saurin kau da kai yana murmushi……K'ara k'ok'arin hada bakinsu tayi amma yayi saurin janyewa yana fad'in "Lips dina kadae ne Virgin Baiii!bana so ayi disvirgin dinshi……"
Harara ta balla mashi ya sakar mata murmushi yana kanne mata ido……
Wayarshi ta d'auki ringing ya duba yaga Aleena ke kiranshi !tab'e baki yayi ya mayar da ita silent suka cigaba da romancing juna……
Sae da suka samu gansuwa sannan ya janye jikinshi ya mike yana fad'a toilet yayi wanka ya fito!ita kam Har lokacin tana kwanshe shekeke sae jefa mashi kallo take tana had'iyar yawu……Ta gefen ido ya watsa mata kallo tare da daukar wayarshi ya kira Aleena……
"Ya jikin naki……" Ya fad'a a hankali bayan ta dauka……
Bata amsa mashi ba tace "Ance man kana Luxury kai da wace shegiya ce……?
Dariya yayi mai sauti sannan yace "Shegiya Baii ce tayi raping dina Aleena……"ya k'arashe maganar cikin rainin wayau……
Banko kofar room d'in akayi……
Su duka suka mayar da hankalinsu ga kofar !Aleena ta shigo kamar wata yar daba……sae huci take……Dage gira yayi ya mike yana k'ok'arin gyara belt dinshi ya kalli Baii ya kalli Aleena ya kwashe da dariya yana fad'in ……
"Baii !Aleena!Deebo's Folalo……"
Babu wacce ta saurareshi sae kallon juna suke ya dauki wayarshi ya matsa kusa da Aleena!ya saka hannu ya zagaye waist dinta tare da janyota jikinshi yana kissing wuyanta ……
Murya k'asa k'asa yace "Last time kin sha duka gurina Baby!Remember mahaifin Baii yaroba ne yaransu na da karfi!ki dage karki kuma cin wani dukan gurinta……"
Harara ta watsa mashi tare da tureshi da karfi ta nufi Baii da ta gama cika kamar ta fashe……
Waving yawa Baii……ya bud'e kofa ya fice ya barsu suna kallon kallo ko wace sae huci take kamar zaki ……
Kafin Baii ta sauko ta makari Aleena tana tambayarta Ubanda ya kawota nan……
Dambe suka kaure kamar wasu yan tasha……
〖〗
Kallo daya zaka mashi ka gane a baya a hayyacinshi yake ba!Wata matashiyar yarinya ce kwance a gefenshi ta lullube dukkan jikinta da bargo ko ba'a fad'a maka ba kasan ya haifeta nesa ba kusa ba……Su duka numfashi suke mayarwa a hankali ido a lumshe……
Wayarshi ya janyo ya tura dan gutun text da yaren yaruba "Ati shey gbogbo ishe na tan Sir awon omo naa wa lodoo Daniel odi aroo ola koto losi India! Alex loma lo kowan ni bhawani Singh road Jaipur Rajasthan lati ibe yen wonma gbe wan losi Rambagh Palace Jaipur... Ola ni owoo naa ma de……"( _Angam shirya komae Sir yanzu haka yaran na hannun daniel gobe da safe zasu tashi zuwa kasar india!Alex zai karbesu a Bhawani Singh Road jaipur rajastha Daga nan zaa shigar dasu Rambagh Palace jaipur……Zuwa gobe kudin zasu shigo…… _ )
Yana gama tura text din kiran 3rd Son na shigowa……Tsaki ya saki ya kai hannu ya janyo budurwar a jikinshi sannan ya dauki wayar cikin fad'a yace "Kiran me kake man dan ubanka tun d'azu Abubakar?
Cike da girmawa Bro Abu yace "Dad Jameela ce tazo kuma tace a nan zata kwana shine na ke so naji ka amince ta kwana anan……"
Ture budurwar yayi yana fad'in "Amma Abu baka da hankali!ka aje katti a gidanka da sunan gadi shine kake maganar d'iyata ta kwana anan"
"Dad wallahi babu abunda……"
Katseshi yayi yana fad'in "Look……ta jira yanzu zanzo na dauketa anan"Katse wayar yayi ya mike yana kallon budurwar da tayi kuri tana kallonshi ya sakar mata murmushi cikin kwarewa da bariki yace "Daughtern ki ce ke son kwana gidan bro dinta……ni kuma ban yarda da sojojin dake zagaye da gidan ba!bana so wani abu ya sameta……"
Shiru tayi lokaci guda idanunta ya cika da kwallah ta mike ta sauko kafafunta daga saman gadon ta dauki kayanta ta mayar !Janyota yayi yana kissing dinta ta tureshi da karfi tana jefa mashi wata irin harara……
Kashe mata ido yayi yace " Ki jirani yanzu zan dawo kin ji ko……Jameela zan mayar gida kawae!babyna the whole day is for you ……!
Hawayen suka silalo a hankali tana kallonshi!lokaci guda tausayin kanta ya darsu a zuciyarta!Ya lalata mata rayuwa amma yana kokarin kare rayuwar d'iyarshi!Shin ita ba d'iya bace?Me yasa mutane suka cika son kansu da yawa!baka tunanin b'ata rayuwar d'iyar wani amma kana tunanin a b'ata taka……
"Menene baby?na ce fa yanzu zan dawo!ki saki ranki……" Maganarshi ta katse mata tunaninta……
A Hankali tace "Me kake tsoron ya faru da D'iyarka ne haka?
Dariya ya saki irin ta yan duniya yace "Kin gane ko baby Gidan cike yake da sojoji ina gudun wani ya kyalla ido ya ganta ya b'ata mata rayuwa a banza……"
Murmushin takaici ta saki tace "Kana gudun a b'ata rayuwar y'arka amma ka b'ata ta ya'yan wasu?
Banza ya mata ya dauki Apple watch dinshi ya saka……
"Duk iya kariyarka yarda ka b'ata ta wasu sae an b'ata taka……"Uban mari ya sakar mata a kumatunta dama da haggu kafin ya hadeta da bango yana fad'in
"Ni kike fad'awa za'a lalata man d'iya?
A Hankali ta gyada kai tana hawaye!Wani wawan marin ya sakar mata tare da fard'eta ta fad'i k'asa ……Da hannu ya nunata yana fad'in "Banyiwa d'iyar wani fyad'e ba babu shegen da ya isa yawa d'iyata!Kud'i na bayar aka zo har inda nake banyi forcing ko wace karuwa ba!Na wadata d'iyata da dukiya babu dan iskan da ya isa ya yaudera akan kud'i…Ke karamar yar iska ce ki kiyayi bakinki a kan d'iyata…"
Fashewa tayi da duka a hankali tana girgixa kai Ashe haka iyayen ke son yayansu?Lallae kam suna cutar iyayensu!Mutumin da yake lalata yaran wasu yana bakin cikin a lalata mashi ta yaranshi ina ga wanda bai b'ata yar kowa ba amma aka b'ata mashi ta yaranshi……?
【】
Rayuwa suke gwanin ban sha'awa cikin tsantsar so da k'aunar juna……Tun lil Fadila bata saba da gaganiyar Anup ba har ta saba……Ita kanta yarinyar da taga Anup zata dinga wangale baki tana harba k'afafu…Bayan an tashi daga school har sun shiga school bus da yake Uncle Jawwad bai zo ba ta fito da gudu ta matsa tana fad'awa teachers dinsu dan Allah suzo gidansu su ga Lil sis dinta wae bata lafiya……da ta ishesu da naci wasu suka ce mata zasu zo……
Cikin murna ta shiga gida ta rungume Ummi tana fad'in "Yau birin bakin gate zai zo yaga lil sis……"
"Biri?Ummi ta maimata a hankali……
YOU ARE READING
TAWA K'ADDARAR......
RomanceLabari ne na wata Yarinya da ta tashi cikin gata da kulawar iyayenta lokaci guda duniyar ta juya mata yayin da ta hadu Kaddara ta rasa dukkan iyayenta Sanadiyyar gobar da ta cinyesu harda karamar kanwarta !ta dimauce ta rasa duk wani tunaninta!Ta ra...