💧💧 *TAWA KADDARAR……💥*
💥
*HASKE WRITER'S ASSO💡*
(Home of expert & perfect writera)*NA FEEDOHM💞*
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
*01*
"Dad……"
Janyo hannunta yayi ya zaunar da ita saman cinyar shi yana fadin "Anup menene……?
Tabe baki nayi tare da kyafta ido daya tana fadin "Ina so nayi ta kiran sunanka kana amsawa……"Dariya ya saki irin ta manya sannan yayi powering Tv yana fadin " Anup manya!Tashi ki dauko man result dinki da aka baku d'azu……"
Waro manyan idanunta tayi tare da rufe baki tana fadin "Dad ba'a bani ba All……"
Bakinta ya buge tare da d'aura hannunshi saman lips dinshi yana kallonta ……
"Mai karya dan wuta kuma mutuwa yake da wuri Anup ……ko kina son ki mutu?Da Sauri ta girgiza mashi kai alamun a'a ta tabe baki lokaci guda idanunta suka ciko da kwallah tana fadin "Bana so na mutu Dad!Kaima bana so ka Mutu ka barni!Mah ma bana so ta mutu ka ji!Dad da Abbansu Fadila ya rasu kaga yarda Su Fadila ke kuka?……Lumshe ido tayi hawayen suka gangaro saman kumatunta ta sauke ajiyar zuciya ta mike da sauri ta nufi bedroom dinta ……
Dakin an kawatashi kamar na wata amarya komai na dakin Pink colour ne teddy ne jere saman bed din ta saka katon blanket ta rufesu ……Sanyayyan kanshin turaren maiduguri ke fitowa daga d'akin ……
Duk'awa tayi ta janye stool din dake gefen gadon sannan ta d'aga blanket da ya rufe karkashin gadon ta tura kanta ciki ……Kwanciya tayi saman tiles din tana kokarin shigar da jikinta karkashin gadon har sae da ta shige duka sannan ta fito janye da wani katon book a hannunta ……
Gyara zama tayi sossae ta janyo wani karamin towel ta goge kurar da yayi……" American international school Abuja.……" Abunda ke rubuce kenan a cover littafin ……Uban duka ta kaiwa littafin hadi da murguda baki lokaci guda tana fadin "God thunder fire you Uncle JAWAD" Sannan ta fara bud'awa a hankali tana kallo……
Result Book ne wanda kallo daya zaka mashi ka tabbatar da wahalar da yasha hannun yarinyar ……Cancel cancel ke tashi ga kowace paper ta bude yayin da inda ake rubuta aihanin Position yayi duk'u duk'u wani gurin ma ya fara yagewa saboda masifar goge goge ……
Har ta kawo karshen book din inda aka rubuta result na wannan term din sannan ta daura littafin saman cinyarta ta tsaya ta saka hannunta ta baya ta janyo school bag dinta ta na lalubar mathematical set dinta……Murmushi ta saki lokacin da ta dauko sannan ta bude ……Ido ta waro tana yarfe hannu tana fadin "Pencil!……hannunta ta saka ta tallabe kumatunta tana kyafta idanu lokaci guda ta fara harba kafunta tana ihu da karfi tana kiran "Uncle JAWAD"tare da harba kafafuwa……
Jin ihunta ya saka Dad dake falon saurin shigowa dakin yana fadin "Anup menene?
Jefa littafin tayi karkashin gado tana fadin "Uncle JAWAD ne yama seizing pencil dina jiya"Lumshe ido yayi ya karaso dakin tare da tsugunnawa ya rungumota yana fadin "Seizing pencil shi ke da wannan ihun Anup?Ina falo kin tayar man da Hankali Anup bakya so hankalina ya kwanta ko ?Bana son kukanki kin ji ko……Kuma Anup me zakiyi da pencil bayan duka jiya aka maku holiday?
Kara kwanciya tayi jikinshi tare da saka kafa ta sake tura result din karkashi gado sannan tace "Ai Sae da ya dakeni ma !Dukan da ya man na tuna Dad……"
Murmushi yayi yana fadin "To yi hakuri duka ba sauran shekara daya ba ki bar mashi school din baki daya?ko anan zakiyi secondary school dinki?
Waro Ido tayi tana fadin "Kace ya kasheni?
Murmushi kawae yayi ya mike ya fita har sae da ya kai kofa sannan ya juyo yana fadin "Ina Result din?ki kawo man shi yanzu muje mu dauko Umminki ko?
Dariya tayi sannan ta koma karkashin gadon ta janyo littafin ta bude tare da dangwalo miyau ta fara goge 3 din farko ta bar 2 din baya ……Sae da gurin yayi bakikkirin ya fara gogewa sannan ta rufe ta fita har da tsallenta ……Tana zuwa ta daura mashi saman cinya ta nufi fridge din dake gefe ta bude ta dauko Apple guda hudu ta dawo kusa dashi tana fadin" Gan nawa gana Dad ga na Ummie sannan gana Unborn ……"
Gani tayi yana budewa da murmushi dauke a fuskarshi ,Wani dadi ya ratsata ta balli Apple din tana fadin "Duk bak'in ciki na Uncle Jawad da bakin ciki na Aunty gloria wannan term din sae da headmistre ya bani gift……Amma kasan me nace lokacin da Aunty Bisi tace JAWAHIR ALMUSTAPHA……"Girgiza mata kai yayi a hankali yana dauke da murmushi ……
Tabe baki tayi tana yarfe hannu sannan ta mike ta rike kugu tana fadin " Ni na gaji da amsar gift a wannan school din don haka a bawa Nafisa Muktar……"Sannan ta koma ta zauna tare da kai Apple din bakinta tace "Haka nace Dad……"Dariya yayi mai sauti sannan yace "Kin kyauta Anup!Amma gaskia wannan karan baran siya maki komae ba……"
Ido ta waro tana fadin"Me yasa Dad……"
Rufe book din yayi ya mike yana fadin "Bakiyi kokari ba!"Dad Second position fa out of 33" Ta fada kamar zatayi kuka…
Keys ya dauka yana fadin "Yeah Muhibba ta gidansu JAWAD na 32 tayi sae Abbanta ya saya mata Jirgi ……"Dafe kirji tayi tare da waro ido tace "Me yasa Dad……?
Mak'e kafad'a yayi ya bude motar ya shiga ta biyoshi itama tashiga tana nacin tambayarshi dalilin da yasa Abban ya saya mata jirgi ……
Sae da Gateman ya bude masu kofa sannan ya kalleta duk ta rude ta zuba mashi ido tare da tallabe kumatunta sannan yace mata "Saboda 32 years din Abbanta ne..I Wish nima next term kiyo man na 32 kinga nima years dina kenan……"
Gyada kai tayi tana fadin "Ta cuci Abbanta wallahi"
Yar dariya ta subuce mashi yace "Kamar ya ta cuceshi Anup?Karamin tsaki ta saki tana jujjuya baki sannan tace "Karya take ni ce fa nayi na 32 a class dinmu……"
Rankwashi ya kai mata a kai yana hararanta !ta saki k'ara tare da dafe kanta tana kuwwa……
" Shut up before I chop your month Jakkan banza ……" Ya Fada ciki tsawa ……Rungumeshi tayi tana fad'in "Wallah Dad First Postion na so nayi Amma Uncle JAWAD ya man bakin ciki suka bani na 32 "
YOU ARE READING
TAWA K'ADDARAR......
RomanceLabari ne na wata Yarinya da ta tashi cikin gata da kulawar iyayenta lokaci guda duniyar ta juya mata yayin da ta hadu Kaddara ta rasa dukkan iyayenta Sanadiyyar gobar da ta cinyesu harda karamar kanwarta !ta dimauce ta rasa duk wani tunaninta!Ta ra...