[6:00PM, 2/1/2018] Feedohm💧: 💧💧 *TAWA K'ADDARAR...*💥
《K'azamar Rayuwa...》💥
® *HASKE WRITERS ASSO.*💡
_Home of expert & perfect writers_*NA FEEDOHM💞*
*Wattpad:Feedohm11**Bestowed to Aunty Sis*💕
*14**I'm Only Responsible For what I Say Not For What You Say!Before You Start Pointing Your Finger A'me Make Sure Your Hands Are Clean…🙅🏻♀*
💥
*Aunty Fateema tabbas kana rubutu ne amma baka san inda yake zuwa ba!Ni Firdaws ban tab'a yarda da hakan ba sae da na had'u dake Aunty Fateema… ban tab'a tunanin kamarki zaki iya bata lokaci ki karanta rubutana ba bare har ki tako daga inda kike ki zogurina😊 A Tunani ganinki ba mai sauki bane a gurin kamana amma sae gashi rubutu ya kawo man shi har gidanmu…Nagode sosae da Alkhairinki Allah ubangiji ya bar zumunci da kauna Allah ya k'ara girma…*
Rau rau tayi da ido sannan tace "Happiness!Kuma Su Ummi suke ceman haka!Sun rasu kuma kinga ba Happiness din kowa bace ko?na koma Sadness…"
"ANUPRIYA…" Uncle Jawwad ya fad'a a hankali tare da jan sunanSu duka suka kalleshi don bai tab'a kiranta da sunan ba!wayarshi ya d'auka ya juyo yana jefa mata wani kallon da bai san yana yi ba had'i da dage mata gira yace "Yeah Anup na mayar da sunan kin ji ko?You're My Happiness…
Maimata sunan tayi kamar yau ta fara jinshi "Anup!sannan ta rungume fadila ta saki dariya tana bubbuga kafa k'asa…
Shima murmushin yayi ya zagayesu ya fita ya shiga dakin Granny ya gayar da ita sannan ya shiga part din Alhaji ya gayar dashi!har zai fita Alhajin ya kirashi yace " Jawwad ka mayar da Jawahir school yau zaman ya isa haka kuma kaima ka koma aiki…"
"Insha Allahu" ya fad'a don shi kanshi dama yana da gurin mayar da ita saboda ta saki yanzu ……
A Dinning ya iskesu da granny tana had'a masu tea ya zauna ya janyo flask din kunun gyad'a ya tsiyaya sannan yace wa granny "Abba yace a mayar da Anup school yau"
"Anup yau kuma Jawwad a bakinka?Granny ta fad'a da mamaki don tana sane da baya iya kiranta haka asali ko son sunan bayayi
Shiru yayi yana kallon Anup da ta saki baki tana kallonshi alamun barata je ba yace " Jeki saka unifoam din Fadila kinji ko?
"Baran je ba" ta fad'a kai tsaye tana murje ido tare da sauka daga kujeran tana turo baki
A Hankali yace "Me yasa Anup……?
Idonta ya ciko da k'walla tace " Da na tafi school su Ummi suka kone bana so na tafi na barka kaima ka kone"
Takowa yayi kusa da kujeran da take tsaye ya dafa ta yace "Babu abunda zaya kuma faru kin ji ko?ki je ki saka unifoam ku fito na kaiku…"
Mak'ale kafad'a tayi tana fad'in "Baran je ba !dan Allah kayi hakuri ka barni bana son school in…"
"Shii na ji bara ki je ba shikenan ko?ya fad'a a hankali yana kallon granny da ta tsaresu ido
Sannan ta mika mata hannu a hankali tace "Zo nan Anup!
Babu musu ta matsa kusa da ita !cikin lallashi granny ta lallab'ata ta yarda fadila ta dauko mata Unifoam din ta sanya sannan suka tafi shima sae da Uncle Jawwad yasa Maigadi ya fito da gas din gidan a gabanta ta gani sannan…
YOU ARE READING
TAWA K'ADDARAR......
Любовные романыLabari ne na wata Yarinya da ta tashi cikin gata da kulawar iyayenta lokaci guda duniyar ta juya mata yayin da ta hadu Kaddara ta rasa dukkan iyayenta Sanadiyyar gobar da ta cinyesu harda karamar kanwarta !ta dimauce ta rasa duk wani tunaninta!Ta ra...